LABARINSU 6

28 0 0
                                    
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*06*
~~~
*The wrong one will find you in peace and leave you in pieces. The right one will find you in pieces and lead you to peace.*
***
*Shekara ta 2000*
*Kano.....*
A hankali Zaid ya juya ya kalli ƙaninsa Aliyu, wanda har zuwa lokacin yake ta risgar kuka. awa biyar kenan da aka kashe wutar da ta kama a gidansu. Wutar da ba ta bar musu komai ba, ciki kuwa harda mahaifiyarsu. Kuma har zuwa lokacin, suna sanye da wannan uniform ɗin islamiyyar, yayin da ƙonnaniyar gawarbmahaifiyarsu ke rufe a gabansu.
Zaune suke a ɗakin da aka ajeta bayan da aka samu aka kawota asibiti, kuma tun kafin su kawo asibitin jama'ar da suka ɗaukota ke faɗin ai ta cika.
Shi ma kansa Zaid ɗin so yake ya yi kukan, amma ya kasa. Bai san ina za su je ba, bai san ina za su koma ba, bai san kowa nasu ba, kuma Momman nasu ko ƙawa ba ta da ita, bare su ce za su je wurinta.
Hatta da asalinsu basu sani ba, bayan ce musu da ta yi ita 'yar haɗejia ce, ba ta ƙara ce musu komai a kan asalinsu ba.
"Aliyu...."
A hankali nitsataiyar muryarsa me cike da kamewa ta kira sunan, yayin da lumaassun idanuwasa masu ɗauke da gray ƙwaya suke kallon Aliyu.
Aliyun ya juyo ya kalli yayansa. Kuma har a lokacin kuka yake. Lokacin ƙarfe takwais na dare da ɗorariya, jama'ar da suka kawo su asibitin ma tafiyarsu suka yi bayan an tabbatar musu da rasuwarta.
"Ba mu yi sallar magrib ba... Ga isha ta kawo kai"
Da ƙyar sautin muryar tasa ke fita, don mai sauraro ma zai iya tsintar ɗacin da muryar tasa ke ɗauke da shi, ba zai ce ya gama mallakar hankalinsa ba, amma ya san cewa duk wanda ya mutu ba ya dawowa.
Ya san cewa yanzu su da ganin Mommansu wata ƙila sai a lahira, sun zama marayu, yanzu su marayu ne waɗanda basu da kowa sai junansu. Babu wanda zai taya su kukan rashin da suka yi.
Ba tare da Aliyun yace komai ba ya miƙe tsaye, shi ma Zaid ɗin miƙewar ya yi, ya dafa kafaɗarsa suka fara tafiya zuwa waje.
Kuma har lokacin Aliyun na kuka, shi kuma Zaid ɗin sai rarrashinsa yake. A masallacin asibitin suka yi sallah. Sannan suka fita wajen asibitin.
Dan Zaid ɗin ya tuna da ɗari biyun da Momman ta basu a yammacin ranar, tace da su; su siyi wani abun idan sun je islamiyya.
Awara ya sai musu da ita, sannan suka dawo cikin ɗakin da aka kwantar da ita. Suna kallon gawar suna cin awarar. Kuma bayan sun gama suka ci gaba da zama a ɗakin, har zuwa lokacin da dare ya tsala. Aliyu ne ya samu ya yi bacci, shi kuwa Zaid kwana ya yi yana gadin su su duka biyun.
Washe gari Zaid ɗin ne da kansa ya bazama cikin asibitin, kafin ya nemo inda mahaifiyarsu ta yi aiki a da. Ya faɗawa abokan aikin nata rasuwarta.
Kuma su ne suka zo suka yi Duk wani abu na sutura. Har aka mata sallah, kafin aka binneta a maƙabartar asibitin.
Har kowa ya watse da ga maƙabarar, Zaid da Aliyu na tsugunne a kan kabarin. A wannan karon shi ma Zaid ɗin sai da ya yi kuka. Kukan rashin sanin madafar da za su dafa a yanzu, mutuwa irin wadda mahaifiyarsu ta yi akwai raɗaɗi.
"Yanzu a nan zamu kwana?"
Aliyu ya tambayi Zaid ɗin, a sanda suka dawo gidansu. Wanda wuta ta gama ƙonawa, ko ina ya yi baƙi, babu abinda ya rage sai rufin gidan.
"Bamu da inda ya wuce nan... Aliyu"
Zaid ɗin ya faɗi yana ƙoƙarin sama musu inda za su zauna. Har ya gama kwashe kayan da wuta ta bari Aliyun na binsa da kallo.
Zaid ɗin da kansa ya share ko ina, ya fitar da tokar abinda ya rage, sannan da ƙyar a cikin kayan ya samu wani bargo wanda bai ƙone ba. Asalin bargon a kan gadon Mommansu take shimfiɗawa. Sai guntuwar katifar Zaid ɗin da ita ma kaɗan ne ta ƙone. Sai wasu kwanuka irin na silver wanda suka yi baƙi. Kuma a cikin tarkacen kayan, Zaid ya samo wani hotonsu guda ɗaya da rage.
Zaid ya fita can banɗakin gidan na waje, ya duba randar cikinsa ya ga akwai ruwa, ya zuba a cikin bokitin da ya samu a banɗakin, sannan ya koma ya kira Aliyu kan ya zo ya yi wanka.
"Zaid wani kaya za mu sa?"
Aliyun ya tambaya a sanda ya fito daga banɗakin, bayan ya yi wanka.
"Babu Aliyu, ba mu da wasu sauran kaya, komai kana ganin yanda ya ƙone, wutar nan bata bar mana komai ba sai ran mu"
"To ni yunwa nake ji!"
Aliyu ya faɗa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. Zaid ya yi shiru yana tunanin ta inda zai samawa ƙaninsa abinci, bai san ta ina zai fara ba, ba shi ma da wata dabarar sanin inda zai samu ko da kuɗin sai masa abincin ne. Shi ba ya ta kansa, ta ƙaninsa da ƙaddara ta bar masa yake.
"Ka zauna, bari na je gidansu Naufal na roƙar mana Mamansu, ƙila ta bamu ko da sauran ne"
ya ƙarshe yana ɗaga kafaɗaraa ta dama. Aliyunya gyaɗa kansa a hankali, a yayin da yake zama a bakin baƙar katifarsu. Zaid ya fita daga gidan ya shiga gidan dake maƙotansu.
Matar gidan ya fara gaisarwa, ta amsa shi da 'yar fara'ar da yake da tabbacin ba ta kai zuci ba.
"Ashe kuma mamarku ta rasu?"
Maman Naufal ɗin ta tambaya a sigar gulma, kan Zaid a ƙasa ya gyaɗa mata, don da ma shi yaro ne mai ladabi, ba kamar Aliyun ba.
"To Allah ji ƙanta!"
"Amin... Da ma Aliyu ne yake jin yunwa, kuma wutar ba ta bar mana komai ba, shi ne na ce ko za mu samu wani abun, da zan bashi ya ci..."
Ya ƙarashe maganar, zuciyarsa na masa tuƙuƙi, wai yau su ne suke roƙon abinci, su ɗin da abinci sai dai su yi sadakarsa, wai aka ce rayuwa juyi-juyi.
"Eh, akwai wani guntu, amma iyaka na cin mutum ɗaya ne"
Kitchen ta shiga, sannan ta fito hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano, ta miƙa masa ya sa hannu ya karɓa yana miƙewa tsaye.
"Na ce kuma wai ku baku da wasu 'yan uwa ?"
Tun ba yau ba da ma yasan halin matar, kuma halinta na san jin ƙwaƙwaf yasa Mommansu ba ta shiri da ita. Sai kawai ya girgiza mata kai, yana ɗaga kafaɗarasa ta dama.
"Bamu da kowa"
Sai ta jinjina kai tana gaskata abun da mutane kan faɗa a kan Rabi'ar, na cewa wataƙila cikin shege ta je ta yi a garinsu, shi ne ta gudo nan ta zo ta kafa sabuwar rayuwa.
(Kai jama'a, duniya ina za ki da mu?!, Baiwar Allah ta rasu, maimakon ai mata addu'a, sai dai a ci gaba da cin namanta. Wanda kuma hakan sam ba dai-dai ba ne).
"Ga wata jallof ɗin taliya, ka ta shi ka ci"
Zaid ya faɗi a sanda ya dawo gidan, Aliyu da ke kwance a kan katifar ya miƙe zaune, sannan ya kai hannu ya karɓi 'yar robar. Kafaɗarsa ya ɗaga yana kallon taliyar.
Abincin duka bai fi loma biyar ba, kuma ko shi Aliyun kaɗai ba ya jin abincin zai isheshi, bare ace shi ma ya zauna ya ci.
"Kai ba za ka ci ba?"
"Ba na jin yunwa"
A sanda ya kai ƙarshen maganar cikinsa, a lokacin ya wani irin ƙulle, saboda yunwar. Amma sai ya dake ya ɗaga kafaɗarsa, sannan ya ce.
"Bari na je na watsa ruwa"
Kuma daga haka ya fice daga ɗakin. Wankan ya je ya yi, ya dawo ya tarar da Aliyu ya raba taliyar biyu, ya ci rabi sannan ya bar masa rabi.
"Me yasa ba ka cin ye ba?,ko ba daɗi ?"
Ya jero masa tambayoyin yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, tare da juya rigar uniform ɗin islamiyyarsa dai-dai.
"A'a, akwai daɗi mana, na ga kai ma ba ka ci ba, ka daure ka ci wannan ɗin"
Wata ƙwalla ta taru a idon Zaid. A hankali ya zauna kusa da ɗan uwan nasa yana kallonsa. Wannan karon kusan a tare suka ɗaga kafaɗunsu na dama.
"Aliyu... Yanzu babu Momma, da ga ni sai kai... Babu wani mai temakon mu sai Allah... Yanzu rayuwa za ta mana wahala, ban san ya za mu ci gaba da rayuwa ba, Aliyu ban san ma mecece rayuwar ba, kawai dai nasan akwai ƙalubale, kuma shi ne abinda za mu tunkara a yanzu!..."
Shi kansa ba ya ce waɗanan kalama nasa ba ne, bai san da ga ina suke zuwa ba, jin su kawai yake suna fita daga bakinsa. Bai taɓa sanin ya iya su ba ma.
Haka kawai ya ji wani nauyin kula da ƙaninsa ya hau kansa, ya na jin zai iya komai dan ganin ya sa ƙaninsa farin ciki, yana jin zai iya sadaukar da komai don ɗaukar nauyin ƙanin nasa...
*Present day......*
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
RAJA POV.
A hankali ya zauna a bakin gadon ɗakin da yake a matsayin nasa. Yanzun nan suka gama zaga gidan, dan ganin abinda za su buƙata. Har yanzu abinda ya faru ɗazu ya ƙi sakin ransa, gani yake kamar mafarki yake, abun akwai ɗaure kai.
"Raja me ke faru wai ?"
Muryar Rhoda ta katse musu kallon-kallon da suke a ɗazun. Kuma maganar tata ce ta sa ya kalli hannun yarinyar dake zubar jini.
Ba tare da ya amsawa Rhodan da ta tsaya tana kallon ikon Allah ba, ya sa hannusa a aljihunsa ya zaro handkerchief, sannan ya ɗaure hannun yarinyar.
Ya lura da ita ma tun ɗazun kallonsa take, sannan irin mamakin da ke kan fuskarsa shi ne sak a kan tata fuskar.
"Babu inda kika ji ciwo?"
Wannan salihar muryar tasa ta tambaya, yayin da take kallonta da gray drunken eyes ɗinsa.
Ya lura da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta gyaɗa masa kai. Shi ma sai ya gyaɗa mata nasa kan, sannan ya miƙe a hankali, idonsa a kanta, yayin da ita take zaune a dandariyar ƙasa.
Juyawa ya yi a hankali sannan ya nufi motarsu da ke tsallake, Rhoda da Zuzu da su ma suke kallon abun mamaki suka bi bayansa, kuma da haka suka iso gidan.
Waɗanan lumsassun idanuwan nasa ya ƙara lumshewa, fuskarta na dawowa a idonsa. Sai kawai ya shafi sumar kansa dake cikin askin high fade. Sannan ya ɗaga kafaɗarsa.
Shi ya kasa ganewa, me yasa hakan ke faruwa da shi ?, wacece wannan yarinyar ?, menene LABARINTA ?, me yasa take kama da shi, Momma da Aliyunsa?.
A hankali ya buɗe rabin idon nasa kamar kullum, ya kamata a ce ya kawar da wannan tunanin, don ba abun da ya kawo shi Abuja ba kenan, ya zo ne domin cimma wani ƙudirinsa, ya zo ne domin ya kawo ƙarshen wani abu.
Dan haka dole ya jingine komai, ya fuskanci abun da ke tunkararsa, Allah ya ƙaddara haɗuwar wannan yarinyar da shi ne dan kawai tasa ya tuna rayuwarsa ta baya, kuma ya tuna ɗin, dan haka komai ya ƙare, ya ƙare daga nan.
Abun da bai sani ba shine; yanzu komai zai soma, yanzu ƙaddarar ta soma, ba ayi komai ba ma. Ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta nan da 'yan wasu kwanaki na dab!, da faruwa, wata ƙaddara da za ta tarwartsa komai, sannan ta saita wasu lamura.
*Unguwar Madallah, Suleja , Niger State*
*08:30pm*
RABI'A POV.
Zaune take a ɗakinsu, yayin da take jera kayanta a cikin ghana most go ɗinta. Gani ta yi kayan nata sun jima ba tare da ta duba su ba, shi yasa yau ɗin ta fitar da su, dan ta sauya musu ma'aji.
Hannunta na dama ta kalla, wanda ke ɗaure sa handkerchief ɗin da wannan mutumin na ɗazu ya ɗaura mata. Wannan mutumin?!, Wannan mutumin da ta ji macen da suke tare, me kaya irin nasa ta kira shi da RAJA!. Wannan mutumin mai kama da Ummanta.
Tunaninsa ya tuna mata da wallet ɗinsa da ta tsinta a ɗazun. Don bayan ya miƙe ya shige motarsa sun bar wurin, ta shiga yunƙurin miƙewe, kuma miƙewar da za ta yi idonta ya kai kan wallet ɗin da take da tabbacin tasa ce. Hakan yasa ta tsugunna ta sa hannu ta ɗauka, kuma ba ta buɗe a lokacin ba, sai kawai ta juya ta ci gaba da tafiyar ta.
Waige-waige ta shiga yi a kan katifar Saratu, dan tana zaune ne a bakin katifar, ƙasan hijabin da ta fita da shi yau ta samo wallet ɗin.
A hankali ta ɗauketa, sannan ta jujjuyata, kafin ta saka hannu ta buɗeta, a dai-dai inda ake saka hoto, ta ga hoton mutum biyu masu kama ɗaya, kuma hatta da kayan jikinsu iri ɗaya ne.
Ba dan dariyar da ɗaya ya yi ba, da babu abun da zai hana tace duka mutum ɗaya ne, zaune suke a ƙasa, daya ya dafa ɗaya. Yau ta fara ganinsa, amma duk da haka sai da ta gano shi a cikin su biyun, saboda rabin idanuwasa da suke a lumshe, sannan akwai tsotsiyar karen da ta ga a ƙasan haƙorinsa.
Iko sai Allah, kenan ba ma shi kaɗai ba ne, to amma umma ta faɗa mata cewar abokiyar tagwaitakar ta wato mai sunanta Rabi'a ta rasu, kuma ta rasu, bayan rasuwarta ma aka ce su ma yaran da ta haifa sun rasu.
To su waye waɗanan ?, me yasa suke kama da Ummanta da kuma ita, dan ganin ɗaya ɗan uwan nasa yasa ta ƙara ganin kamarta a cikin fuskokinsu, duk da a lokacin yarinta aka musu hoton.
A hankali hannunta ya ci gaba da buɗa wallet ɗin, akwai kuɗaɗe a ciki, sai atm cards. Bakinta ta taɓe, sannan ta rufe wallet ɗin, wata ƙila Allah zai sa su ƙara haɗuwa, sai ta samu damar ba shi kayansa.
Aje wallet ɗin ta yi a gefe, sannan ta ci gaba da shirya kayan nata. Kuma a cikin kayan ne, hannuta ya ɗauko wata jersey, jerseyn ta Bacerlona ce. Kuma tata ce. Nan take idanuwanta suka hango mata lokacin da aka samu rigar.
_"Yaya Baby, Umma ta dawo"_
_Muryarta ta faɗi, a sanda take kallon Umman tasu da ta dawo daga asibiti, sannan a lokaci guda ta faɗa jikin mamar tata ta rungumeta._
_"Umma sannu da dawowa"_
_Baby ta faɗi a sanda ta leƙo daga ɗakinta. Umman tasu ta kalleta tana amsawa._
_"Yayar mamarta kin san me Umma ta kawo miki ?"_
_Umman ta faɗi a sanda take zama a kan sofa, cike da ɗauki Adawiyya ta girgiza mata kai alamun a'a._
_"Jersayn Becelona!..."_
_Umman ya faɗa tana fiddo da jersyn daga jakarta da ta saba fita da ita. Adawiyya ta daka tsalle ta rungume Umman tana murmushi._
_"Thanks Umma"_
Jin wata ƙwalla na shirin taruwa mata a ido yasa ta yi saurin cilla rigar cikin kayanta, a mafiya yawan lokuta rayuwarta ta baya ba ta faɗo mata sai a sanda ta ga wasu kayanta na da.
A da ba ta da jerseyn sakawa da ta wuce wannan, dan Barcelona shi ne favourite team ɗinta. Ba ta da burin da ya wuce idan ta girma ta fara biluga ball, har ta kai ga wata rana Barcelona su ce za su siyeta, ta tafi can ta je tana buga musu ball.
Jama'a da dama sun sha mata kallon banza a kan ball ɗin da take da burin yi, kuma ba kowa ba ne illa al'umarta, hausawa 'yan arewa, kamar dai sauran mata, ita ma haka ake fatan ta darƙushe baiwarta ta ja bakinta ta yi shiru.
Saboda ana ganin ba za ta iya ba, a matsayinta na mace, mutane na ganin zaman gida ne ya dace da ita, ita kanta ta san da hakan, amma kuma aure ba shi zai hanata cimma burinta ba, tana san ta zama wata aba a fannin buga ball.
Wata rana ita ma a saka sunanta a jerin ƙwararru, kuma duk wanda zai kira sunan nata dole sai ya kira arewa, domin nanne tushenta, nan ne asalinta.
An sha cewa ba ta da hankali, dan kawai tana san zama 'yar ball, a ganin mutanen arewa ball wasan maza ne, mace ba za ta iya ba.
A da Ummanta ta saka mata a ranta cewa za ta iya, ta ba ta duk wani goyon baya kan ta yi, amma kuma yanzu komai ya tsaya, komai ya wargaje tare da rasuwar Umman.
*DSS (Department of State Service) Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
Cikin takunsa mai ƙarfi yake tafiya, kansa a sama, babu ruwansa da kallon kowa, ciki kuwa harda waɗanda ke gaida shi, kuma suma da alama basu damu ba, don idan da sabo sun saba. Shi kullum haka yake rayuwarsa, babu ruwansa da kowa a wurin, idan har kai ba a tawagarsa kake ba, to fa shi babu ruwansa da kai. Elevator ya shiga, wadda ta kai shi zuwa floor ɗin office ɗinsa.
Ya fita daga ciki, kafin ya shiga office ɗinsa, kujerarsa ya ja ya zauna, sannan ya kunna desktop, ya shiga danne-danne.
Kafin bayan shuɗewar wasu lokuta, ya ɗauki wayar land line ɗin dake kan table ɗinsa ya aika kira, kuma kalamai biyu kawai ya faɗi sannan ya katse kiran.
Bayan ɗan wani lokaci, aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin, gyaran murya ya musu kamar kullum, kafin ƙofar ta buɗe.
Sharon, Abubakar da Symon suka shigo, nuni ya musu da kan set ɗin wasu sofa da ke tsakiyar office ɗin, alamin su zauna a can. Zama suka yi, a sanda shi ma ya taso daga kan tasa kujerar, hannunsa riƙe da wasu takardu ya zauna a kusa da su. ya shi ga musu bayani akan abun da ya sa ya kirasu.
"Kamar yanda muka riga muka fara wannan binciken, tun farko na sanar muku da rukuni garesu... Sunan ogansu Tomes, yana da yara shida, sannan akwai mace ɗaya a cikinsu... Kuma ana zarginsu da fasaƙwaurin miyagun ƙwayoyi, kisa..."
Sai kuma ya yi shiru, yana tauna maganar da zai faɗa ta gaba, dan har wa yau kalmar na masa nauyi a bakinsa, musamman ma idan ya tuna cewa wannan hanyar ita ce silar samuwarsa, ita ce silar zuwansa duniya, ita ce silar raba mahaifiyarsu da farin cikinta.
Wannan hanyar ita ce ta sa bayan rasuwar mahaifiyarsu aka rasa wanda zai bawa rayuwarsu agaji, har ta kai ga ya rasa yayansa, ɗan uwansa, mafi soyuwa a ransa. Kafaɗarsa ya ɗaga yana ci gaba.
"...Fyaɗe, sai kuma saye da siyarwar miyagun ƙwayoyin... A halin yanzu na yi magana da Ram, ya na tricking location ɗinsu, kuma daga zarar ya gano inda suke, kai tsaye farmaki za mu kai... Ko a mutu ko a yi rai!"
Abun da bai sani ba shi ne,wasu lokutan abubuwan da mukan furta su ne ke faruwa, wasu ƙaddarorin kan faru kamar yanda muka ayyana a zukatanmu. Wannan kalaman nasa na da alaƙa da wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwar ta 'yan lukuta ƙalilan da za su zo. Wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura.
A yammacin wannan ranar, bayan lokacin tashinsa a aiki ya yi, yana tuƙi cikin baƙar motarsa ƙirar honda elevate. Hannunsa na dama kan sitiyari, yayin da ɗayan kuma yake kan bakinsa.
A hankali ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, yana tsuga gudu a motar tasa, dan dama can shi haka tuƙinsa yake, ba ya tafiya a hankali, kuma hakan ne ke sawa suke raba gari idan za su yi tafiya shi da Anna, don haka take cewa; ita tabna san rayuwarta, ba ta shirya mutuwa ba.
Tunanin hakan yasa shi yin murmushi a cikin ransa, a fili kuwa babu komai a kan fuskar tasa, ba fushi yake ba, ba fara'a yake ba, haka kuma ba ƙunci yake ba.
Duk ƙwaƙwaffin mutum ba zai iya tsintar abun da ke kwance a kan fuskar tasa ba. Kamar daga sama wata motar ɗiban yashi, ta daki motar tasa daga gefe. Motar tasa ta yi ta dungurawa tana sakewa a kan titin, hakan ya sa ta yi kwatsa-kwatsa tun kafin ta tsaya da dunguwarawar da take.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja*
MISHAL POV.
Tsaye take a cikin kitchen, sanye cikin uniform, a hankali hannayenta ke jera kayan abincin da ta gama girkawa a cikin lunch box ɗinta.
Ƙofar kitchen ɗin ta buɗe, Hajjara ta shigo tana mata murmushi kamar wancan karon, kuma a yanzun ma sai da ta tsorata, dan ba ta san da me ta zo ba wannan karon. Ƙarasowa ta yi gabanta ta tsaya tana mata wani irin kallo.
"Ya akabyi Tsaka?!"
Mishal ɗin ta tambaya, tana maida dubanta kan kayan da take jerawar. Sunan ya daki gangar zuciyar Hajjara, amma da ta tuna abin da ya kawota sai kawai ta basar.
"Tsaka ba?, za kuwa ki ga ma'anar tsaka"
"Ai babu kalar tsakar da ban ga ba... Me haɗa mutum da mutum ai tsaka ne Hajjara!... ko babu wanda ya taɓa baki labari cewar kaf tarihi babu wanda ya kai tsaka iya munafirci?"
Ta kira sunanta kai tsaye, kuma tana kallon cikin idonta. Dan ba ta shakkarta ko tsoronta, tsoron sharrinta kawai take.
"Yaro man kaza... Ke a tunanin ki za ki iya raba ni da mijina kuma na zauna ina kallonki ?"
Mishal ta ɗan yi murmushi tana harɗe hannayenta a ƙirji.
"Hajjara... Ke ce kika ɗauke ni a matsayin kishiya, ko da wasa ba na kishi da ke, saboda ban ga dalilin yin hakan ba, na ga kamar jahilcinki na san taɓa miki ƙwaƙwalwa, babu aure tsakanina da mijinki... Kuma kafin ya fara saninki ni ya fara sani... Amma ba zan yi mamaki ba dan kina kishi da ni, tun da 'yar da kika haifa ma kin ƙita saboda tana da nakasa... Me zai sa na ji haushi dan ni kin ƙini?"
A wasu lokutan duk da ƙarancin shekarun Mishal da kuma yarintarta tana da hankali, dan wani zubin takan yi magana ta hankali.
"Wata ƙila daga yau ba za ki ƙara ɗaga yatsarki a fuskata ba..."
Hajjara ta faɗa tana kallonta. Mishal ba ta fahimci abin da take nufi ba, sai da ta ga ta shiga waige-waige a cikin kitchen ɗin, sannan ta gane me take nufi. Kuma ba ta ƙara tabbatar da abin da kanta ke gaya mata ba, sai da ta ga Hajjaran ta rarumo wuƙa.
Abubakar na zaune a falo yanawa Daala wasa, sai ji ya yi an ƙwalla wata razannaniyar ƙara, wadda yake jin tana fitowa daga kitchen. Tsabar tsoratar da ya yi, ya kasa gane ƙarar waye.
Ba shiri ya miƙe, ya nufi kitchen ɗin gadan-gadan. Ba ƙaramin tashi hankalinsa ya yi ba, a sanda ya yi arba da abinda ke aukuwa a kitchen ɗin.
Mishal ce zaune a kan marbles, hannaunta na dama riƙe da na hagu. Yayin da tsintsiyar hannunta na hagun ke zubar da jini, sai kuka take tana hawaye. Dubansa ya kai kan Hajjara dake tsaye a kanta, hannunta riƙe da wuƙa.
A tsorace Hajjara ta kalli Mishal sannan ta kalleshi, sai kuma ta cillar da wuƙar, idanta ya cika da ƙwalla, ta ci gaba da kallon Abubakar tana girgiza masa kai, alamun a'a.
"Innallilahi wa inna ilaihi raji'un, Hajjara, kashemin ƙanwa kike san yi?"
Abubakar ya tambaya a kiɗime, yayin da ya ƙarasa gaban Mishal yana duba hannun nata. Hajjara ta shiga girgiza masa kai, tana san ganar da shi gaskiyar abin da ya faru. Ita fa ba ta yi komai ba, ba ta san ya aka yi komai ya auku ba. Cikin muryar kuka ta shiga faɗin.
"Abubakar Wallahi... Walahi ban mata kom..."
"Ki min shiru!, Kada ki sake min magana. Na ɗauka tsanarta kawai kika yi, ahse har kasheta ma za ki iya yi!"
Abubakar ya katseta a zafafe, bayan da ya ɗago daga duba Mushal ɗin da yake. Ya ƙara tsugannawa kan Mushal da ke ta kuka kamar zata fasa gidan.
Yasan ƙanwarsa da dauriya, ba komai takewa kuka ba tun tana ƙarama, tana iya jure komai duk zafinsa, dan haka tun da take kuka, dole ciwon nata ba ƙarami ba ne.
Kamata ya yi, sannan ya miƙar da ita yana shirin fita da ita daga kitchen ɗin. Sai da suka zo wucewa ta kusa da Hajjara, Mishal ta kalleta, kamar ba ita ceke yin gunjin kuka yanzu ba. Sai da ta faki idon Abubakar, sannan ta ƙiftawa Hajjara ido ɗaya, tana murmushin da ke nuna ita ta yi winning gasar.
"You lose!"
Ta furta hakan a iyaka kan leɓenta kawai, wanda Hajjaran dake ganinta ce kaɗai za ta iya gane me ta faɗa. A sanda Hajjara ta zube a ƙasa tana runzar kuka.
A lokacin Mishal ta dawo da nata sabon kukan, tana riƙe hannunta. Hakan yasa Abubakar ƙara ruɗewa, don bai ko Hajjara bai waiwaya ba.
*Nizamiye Hospital, Sector S. Cadestral zone, Life Camp, Abuja*
"Kamar yanda na faɗa maka ne, yanka ba wani sosai ya shigeta ba, dan haka ba wata damuwa, za ku iya tafiya..."
Likitan da ya duba Mishal ne ke korowa Abubakar bayani, wanda gaba ɗaya hankalinsa ya gama ta shi.
Daga can wata kujera dake gefe a office ɗin kuma, Mishal ce zaune, daga ita sai long sleeve Oxford shirt ɗin uniform ɗinta, suit ɗina na aje a gefen kujerar da take kai. Kanta a ƙasa tana tuna abun da ya faru ɗazu.
A ɗazun bayan da Hajjara ta rarumo wuƙa, sai ta ɗorata a tsintiyar hannunta sannan tace.
"Zan yanka kaina, dan na rabaki da Abubakar, zan zubar da jini na fansa, dan na shiga tsakaninku, zan yanka kai na yanzu, sannan na kira shi na ce kece kika yanka ni..."
Kuma tun kafin ta gama faɗin abun da za ta faɗa, Mishal tai wuf ta ƙwace wuƙar daga hannunta, sannan ta ɗora a nata hannun ta yanka kanta. Ta kuma yi sauri ta danƙawa Hajjaran wuƙar, kafin ta faɗi ƙasa, shi ne ta kurma wannan ihun tare da saka kuka.
Sai kawai ta yi murmushi a fili, yanzu da ace ba ta yi hakan ba, da yanzu ita ce a ciki, ta rasa me ta tsarewa Hajjara da ta tsaneta haka, ba ta san me ta yi mata ba.
Hannunta na hagu ta ɗago, ta kalli plastern da aka saka mata yanzu, sannan ta ɗaga kai ta kalli Abubakar da ya zo ya tsaya a kanta yana kallonta cike da tausayawa.
"Sannu Hafsat, tashi mu je"
Sai ta miƙe tsaye, tare da kai hannunta na dama ta ɗauki suit ɗin.
Wayar Abubakar ta yi ƙara a sanda suka fito daga office ɗin, hannunsa ya sa a aljihu ya ɗauko sannan ya amsa.
"Hello Sharon, howdey?!"
Daga cikin wayar Sharon tace.
"Fine sir... Kuliya ne ya yi hatsari jiya, sannan an kwantar da shi a asibiti..."
"What?!, hatsari?!, a ina?, wani asibiti yake?"
Ya katseta tare da jero mata tambayoyin. A lokaci guda kuma ya dakata da tafiyar da yake, hakan yasa Mishal ma dakatawa tana kallonsa.
"Nizamiye hospital"
Sai ya yi shiru.
"Yanzu haka ina cikin Nizamiye hospital ɗin, wani ɗaki yake ?"
"Room No.18"
"Nagode Sharon"
Kuma daga haka ya sauƙe wayar.
"Ukti abokina ba shi da lafiya, muje mu duba shi"
Mishal ba ta damu da san sanin waye abokin nasa ba, dan haka kawai ta bi bayansa.
*Room No.18, Nizamaye hospital*
KULIYA POV.
"Yanzu miye amfanin irin wanna?!, Ka daba abun da ya sameka ka gani da idonka, kullum ina cikin maka nasiha a kan yawan gudun da kake da mota, amma sam baka kulawa, yanzu ga irinta nan!..."
Anna ce ke ta balbale shi da faɗa, yayin da take tsaye a kansa, kusa da gadon marasa lafiyar da yake zaune a kai. Ya jingina bayansa da gadon, gefen fuskartsa na manne da plaster, hannunsa da kuma wuyansa gaba ɗaya rauni ne.
Allah ne ma ya kawo masa abun da sauƙi, dan a sanda wannan babbar motar ta daki tasa sai Allah yasa ya fita ta wundo, sanda motar ta tashi sama.
Bayan ya faɗo sai ya gangara bakin titi, hakan ne ma yasa ya ji raunikan jikinsa. Kuma a sanda jama'a suka kawo masa ɗauki ya suma, don haka bai farka ba sai cikin daren, shi ne ya tsinci kansa a asibiti.
"Yanzu idan ka ga motar taka ba za'a ce ɗan adam ya fita daga cikinta ba, saboda yanda ta kwankwatse!..."
Anna ta ci gaba da faɗi cikin faɗan da take, a hankali ya ɗaga kansa ya kalleta, sannan ya ce.
"Ki yi haƙuri Anna, amma ni ban san daga inda motar take ba, kawai da..."
"Ina za ka sani?, ai ba za ka sani ba!"
Kuma tana kaiwa nan ta figi jakarta ta fita, dan ba za ta iya jurewa ba, Aliyu kaɗai ya rage mata a duniya, duk da ba ita ta haife shi ba, amma ta na sansa, tana masa so irin na ɗa da uwa. Gawara ta nuna masa fushinta a kan abinda ya yi, wata ƙila ya fahimci kuskurensa ya gyara.
A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya shafa kansa. Duk yan da aka yi wannan haɗarin shiryyaye ne, dole ne ma wani ne ya shirya shi. Kuma ko kokonto ba ya yi, imma dai waɗan da ya taɓa sakawa ciki matsala ne, ko kuma waɗanda yake tunkara a yanzu.
Kan nasa ya sauƙe shafawa, sannan ya kalli side drawer, inda wayarsa da sauran kayan da ke jikinsa a jiyan suke aje. Hannu ya kai ya ɗauki wayarsa da ya buɗeta tun jiya ya ga yanda ta farfashe.
Bai damu da fashewarta ba, ya shiga daddanawa, duk da bata dannuwa da daɗin rai. Lambar Ram ya nemo, wani ma'aikacinsu wanda ya san kan computer, kuma ɗan baiwa wanda yake aikin ɓadda kama.
"Easy..."
Ya amsa gaisuwar da Ram ɗin ke masa bayan ya ɗaga kiran. Ya ɗaga kafaɗarasa a hankali,sannan yace.
"Me ka gano ?"
"Sir na samo location ɗin, sun sauƙa ne a wani gida dake Abacha road"
Muryar Ram ɗin ta faɗa daga cikin wayar. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa, sannan ya kashe wayar ba tare da yace komai ba. Ya kai hannu ya aje wayar tasa, kuma a dai-dai lokacin ne, ƙofar ɗakin ta buɗe.
Abubakar ya fara shigowa, biye da shi wata yarinya ce, mai kama da Abubakar ɗin, sai dai kuma ita yafinyar ta fi Abubakar ɗin hasken fata da kuma kyau. Zuciyarsa ta faɗa masa cewar yarinyar na da kyau, wani irin sihirtaccen kyau, wanda a kallo ɗaya za ka tabbatar da cewa ƙwarai, tana da kyau.
Amma kuma shi ba ya san raini, shi yasa bai ciki shiga sabgar mata ba, musamman wannan da ya gane cewa ita ce ƙanwar Abubakar ɗin da yake yawan masa zancenta. Kansa ya kawar yayin da Abubakar ɗin ya miƙo masa hannu alamun su gaisa. Gaisawar suka yi yana wani basarwa.
Kallo ɗaya Mishal ta masa ta sheƙar, dan ta ga alamun wannan mutumin ɗan raini ne, amma duk da haka sai wani ɓari na cikin zuciyarta wanda yake me hankali ya ce mata; ko ba komai ai abokin Akinta ne, kuma da gani ya girme mata, dan haka ya kamata ta gaida shi. Ciki-ciki kamar me ciwon baki tace.
"Ina kwana..."
Wani abu me kama da igiya ya ɗaure zuciyar Kuliya a ma'ajinta, ya ji kamar zuciyarsa ta gaza, ya ji yana san ya sake kallonta, amma dan kada ta raina shi, sai kai wai ya ƙi ya kalleta ma bare ya amsa gaisuwar.
Abun ya bawa Mishal haushi, duk da ba da ƙarfi ta yi maganar ba ai yaci a ce ya ji gaisuwar, bata iya ɓoye-ɓoye ko riƙe fushi ba, don haka ta kalle shi tace.
"Ba ka ji ina gaida ka ba ne ?!..."
Sai a lokacin ta kalli abinda ba ta lura da shi ba a kallo na farko da ta masa, kammanin fuskarsa, kammace sak irinta Antinta ADAWIYYA!, kenan yayanta ne?, ko ɗan uwanta ne ?.... Haka tunanin ya ci gaba da yawo a cikin kanta.
Ba Kuliya kawai ba, hatta da Abubakar kallonta ya yi, abun ya bashi mamaki, a cikin shekarunsa za'a iya kwasar nata, kuma a bar sauran da zai isa a bawa wani mai hankalin. Amma ko tsoro babu a idonta ta kalleshi take masa magana a tsaye. Idonta da ya kalla ne yasa gabannsa wani irin bugu, wanda sai da ya ji ƙaran bugun zuciyarsa a kunnuwansa. Ƙwayar idonta na da kyau kamar fuskarta, wasu irin olive green colour eyes gareta...
#Labarinsu
#SaiKaska
#TaurariWriter's*LABARINSU*

#TaurariWriter's

LABARINSUWhere stories live. Discover now