LABARINSU 13

117 5 5
                                    

*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*13*
~~~
*Some people are your happy pill, no matter how sad you are...*
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
*Brickhall school, Kaura District, Abuja.*
RABI'A POV.
Za ta iya!, tabbas za ta iya. Wannan shi ne abun da take faɗawa kanta, a dai-dai lokacin da take tsaye a filin ball ɗin makarantar, sanye take cikin kayan ball ɗin da Mishal ta ba ta jiya, a cikin filin kuma akwai wasu 'yan mata guda biyar, waɗanda su ma ke sanye cikin kalar nasu kayan wasan ball ɗin.
Daga can wajen ragar filin kuma, Mishal ce tsaye, ta yi ƙuri da idonta a kansu, yayin da take jiran ganin salon wasan Adawiyyan.
Rabi ta lumshe idonta na wasu 'yan sakkani, kafin ta buɗesu ta ɗora a kan ball ɗin dake tsakiyarsu, daɗewar da ta yi ba ta buga ball ba ba ya nufin cewa ta manta yanda ake buga ball ɗin, ko wani salo da ko wani taku na yin ball babu wanda ta mance, a da tasha dakun rana makamanciyar wannan, yau sai ga shi Allah ya cika mata fatanta, don haka za ta gwada, za ta gwada duk wata iyawa tata a kan wannan wasan.
Cike da ƙwarewa suka fara wasan, a tashin farko sai da suka ci Rabi sau biyu, duk da Mishal ta yaba da iya wasan nata sai da ta sare, amma kuma bayan tasu nasarar sai Rabin ta shiga yankasu, ba ta sarara ba sai da ta ci su uku.
Wani irin ihun murna da Mishal ta saki ne ya sa hankalin kowa ya dawo kanta, don zuwa lokacin hatta da ɗaliban dake kaikawo a wurin sai da suka tsaya kallon wasan, don wasan nasu akwai ban sha'awa.
Da gudu Mishal ta shiga cikin ragar ta rungume Rabi suna dariya, ba tare da sun ankara ba suka hautsina suka faɗi ƙasa, Mishal ta sauƙa daga kan Rabi ta kwanta a ƙasa suna dariya, ba ƙaramin burge Mishal Rabi ta yi ba. Ita kuma Rabi tana farin ciki ne don samun damar buga ƙwallo bayan tsawon lokaci, ita kanta ba ta zaci cewa za ta iya buga wasan da kyau irin haka ba, bayan shuɗewar wani dogon lokaci, yau ita ce take dariya sosai, wadda take fitowa tun daga ƙasan ruhinta, har ta manta rabonta da ta yi irin wannan dariyar.
RAJA POV.
Tafe suke shi da Rabi a kan titin Joy Emodi CI, layin ya yi shiru, kasancewar babu kai kawon mutane, tun bayan da ya ganta yau, ya lura da wani irin farin ciki kwance a fuskarta.
“Akwai wani abu na mussaman ne?”
Ya yi tambayar da ba tare da ya kalli fuskarta ba, ita ma kuma ba tare da ta kalle shi ba, ta sunkuyar da kanta tana murmushi.
“Bayan shuɗewar tsawon lokaci, yau na buga ball, shi yasa nake cikin farin ciki...”
Ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, ya juyo ya kalleta, Kyakkyawan murmushinta shi ne yake ƙara bayyana masa kammaninta da Mommansa, zuwa yanzu yasan da cewa akwai sabo tsakaninsa da ita, kuma a yanzun ne ya kamata a ce ya tambayeta wani abu game da kanta.
“Ammata a gidan ku da wa kike kama?”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta yi murmushi.
“Kana san sanin dangantakar ka da ni?”
Cak, Raja ya tsaya, hakan ya sa ita ma Rabin tsayawa tana kallonsa.
“Na san kana tunanin na haɗa alaƙa da kai. Ban sani ba ko kai ɗin jinina ne, amma dai a cikin familynmu babu wanda ya ɓata, da ace akwai wani wanda na san ya taɓa ɓata, ko ya bar gida, da sai na ce wata ƙila kai ne, ko kuma ka fito daga wajensa ne!”
Ta zaɓi da ya ɓoye masa ne don har zuwa yanzu ba ta gama sanin waye shi ba, ta na buƙatar fara sanin waye shi, kafin ta bayyana masa cewar ta san shi da ɗan uwansa 'ya'yan abokiyar tagwaitakar Ummanta ne!.
“Da Ummana nake kama, dan haka ko da zan yi zaton cewa kai ɗan uwanmu ne. Zan ce ka fito daga tsatson Umma ne!”
Da ƙyar Raja ya haɗiye yawu, jin cewa Rabi'a ba 'yar uwarsa ba ce kamar yanda ta faɗa, sai dai kuma shi ya jita ne kawai, amma ya riga da yasan cewa ita 'yar uwarsa ce, alaƙar tsakaninsu ce bai sani ba, amma tabbas ita 'yar uwarsa ce!.
KULIYA POV.
A hankali ya turo ƙofar ɗakinta, a lokacin kusan ƙarfe goma na dare, wai a hakan ma ya dawo da wuri, don ya na so ya sameta ido biyu, amma cikin rashin sa'a sai ya tarar ta yi bacci kamar kullum, a jiya ya nema mata drivern da zai riƙa kaita makaranta yana dawo da ita, kuma kamar yanda ta buƙata ya sai mata kayan abinci da kuma kayan girki, don ita kaɗai za ta girka kayanta, shi ba zai iya cin jagwalgalen da za ta girka ba, yanzu haka shigowa ya yi don ya sanar mata da an kawo kayan girkin.
Sai ya samu kansa da ƙare mata kallo daga nan inda yake, yanayin kwanciyarta kaɗai zai sa ka gane cewa mummunar kwanciya gareta, kanta a wani gefe da ban, haka ƙafafunta ma sun yi wata duniyar, blanket ɗin da ta rufe jikinta da shi ya yaye daga jikinta, ya yi wani wurin.
A zuciyarsa ya yi murmushi ya na shigowa cikin ɗakin, tsayawa ya yi a jikin gadon yana kallonta, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, kafin ya kai hannunsa ya na gyara mata kwanciyar, har ya ɗora kanta a kan pillow ba ta farka ba, ya gyara mata ƙafafuwan na ta duk shiru kake ji, kamar wata gawa, ya janyo blanket ɗin ya rufa mata, sannan ya mata addu'ar da yake da tabbacin ba yinta take ba, ya miƙe ya na kashe wutar ɗakin, sannan ya fita.
Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka, ya sauya kayansa, a sanda ya fito daga closet ɗinsa ya iske Ayra zaune a kan gadonsa, ya kamota ya ajete a inda ya saba kwantar da ita, shi kuma ya shiga ƙarasa aikin da bai samu ya ƙarasa a office ba. Allah ya sani a kwanakin nan ayyuka sun sha masa kai, ko lokacin kansa ba ya iya samu, don a yanzu haka ma ko abincin dare be samu ya ci ba, amma babu yanda zai yi, yana bawa aikinsa muhimmanci fiye da komai.
RABI'A POV.
Yini ta yi tana bawa Anti Saratu da Zara labarin ball ɗin da ta buga, haka ta kwana da wannan farin cikin fal ranta, da ga ta yi juyi za ta tuna da yanda ta buga wasa me kyau, sai wani kalar farin ciki wanda ba ta san daga inda yake ba ya lilliɓeta har ka.
Washe gari weekend, don haka gidan kawai ta gyara, sannan ta shiga kiciniyar haɗa kayan suyar funkaso, kuma har washe garin wannan farin cikin bai bar ranta ba.
RAJA POV.
“Su kenan?”
Ya tambaya a dake, yayinda yake kallon mutumin da ya kawo musu makaman da suka yi oder, mutumin ya zuƙi karan sigarin dake hannunsa sannan ya furzar yana gyaɗa kansa.
“Su kenan”
Sai shi ma Rajan ya gyaɗa kansa, ya na ɗaga kafaɗarsa.
“Na fahimta”
sannan ya waiga yana bawa su Zuzu umarni da su kwashi makaman su zuba a booth ɗin motarsu, har ya juya zai koma cikin motarsu mutumin ya katse shi ta hanyar faɗin.
“Ɗan uwa wannan cikar fa?, Idan ba damuwa ina buƙata!...”
Mutmin ya ƙarashe yana wa Rhoda wani irin shegen kallo, babu shiri Raja ya juyo ya na watsa masa wani masiffafen kallo, idanuwansa da suke a lumshe da sune ya buɗesu tar a kan mutumin, kuma ba jimawa da buɗesun, farin cikinsu ya rikiɗa zuwa ja, jijuyoyin kansa suka fito raɗa-raɗa, yau shi akewa magana kan ya bada ƙanwarsa a matsayin karuwa?, me wannan mutumin ya ɗauki kansa ne.
A fusace ya yi kan mutumin, shi kuma ya riga da ya tsorata har ya shiga ƙoƙarin guduwa, Raja ya ci kwalar rigarsa da hannunsa na dama, sannan ya shiga naushin fuskarsa da hannunsa na hagu. Cikin su Zuzu da Jagwado da Rhoda babu wanda ya yi yunƙurin dakatar da shi, dukansa yake yana ƙarawa, kunnuwansa sun toshe, babu abun da yake ji sai maganar mutumin da ya yi a ɗazu, sai da ya farfasa masa fuska tukkuna Alandi ya ga kamar kashe mutumin Raja ke ƙoƙarin yi, don haka ya ƙarasa kusa da shi ya riƙe shi, amma bisa ga mamakin Alandin sai Raja ya ha kaɗashi shi baya.
Hakan ya ankarar da Rhoda cewar Rajan ba a hayyacinsa yake ba, saboda haka ita ta ƙarasa kusa da shi ta dafa kafaɗarsa ta dama.
“Zaid is okay!”
Cak, hannun da Raja ya ɗaga don dukan mutumin ya tsaya a iska, ban da hucin ɓacin rai babu abun da yake, har wani datse haƙwara yake, gaba ɗaya ilahirin jikinsa sai rawa yake.
Yakan shekara ransa bai ɓaci ba, amma idan ransa ya ɓaci abubuwa da dama za su ɓaci, sakin kwalar mutumin ya yi, hakan yasa ya zube a ƙasa ragwajab!, hannunsa na hagun da ya ɗaga ya daki iska da shi.
Har lokacin idanuwansa a buɗe suke gaba ɗaya, sai huci yake, kamar wani wanda ya yi wasan tsere, juyawa Rhoda baya ya yi yana rufe fuskarsa, duk da iskar dake kai kawo a wurin shi gumi yake, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana ɗaga kansa sama.
Kamar wanda aka tsikara kuma sai ya zabura ya faɗa cikin mota yana kwantar da kansa a kan dash-bot. Sai sauƙe ajiyar zuciya yake, a hankali kuma girman idanuwansa suka shiga raguwa.
*No.181, Guzape, Abuja...*
*80:40 AM*
MISHAL POV.
Tsaye take a kitchen tana girka jallof ɗin couscous, fuskarta kawai idan ka kalla za ka gano tsantsar farin cikin da take ciki, don yau da safe da ta tashi ta shiga kitchen ɗin ta tarar da tarin kayan abinci da kayan girki. Allah ya sani, ita ba san wannan abincin restaurant ɗin take ba, shi yasa ba ta ci sosai, don har wata 'yar rama ta yi a kwanakin.
Daga ƙasan marbles ɗin kitchen ɗin kuma Ayra ce ke cin kifin da Mishal ɗin ta saka mata.
Mishal ta kwashe jallof ɗin tare da zubata a kan wani plate me kyau da ya fi burgeta cikin kayan kitchen ɗin, dai-dai da lokacin da aka turo ƙofar kitchen ɗin.
Kallon ƙofar ta yi, duk da ta san cewa shi ne, kamar kullum sanye cikin baƙar suit, yana kallonta a sanyaye, wani abu sabo game da shi.
“Ina kwana Abu Aswad!”
Ta faɗi a sanda yake shigowa cikin kitchen ɗin, cak Kuliya ya dakata da tafiyar da yake, sannan dubansa ya zarce zuwa kan fuskarta, yayin da take zama a kan kujerar island.
Abu Aswad?, shi ɗin ne Abu Aswad?, don kawai ya na saka baƙaƙen kaya, sai ua zama Abu Aswad? Sai ya ƙi tanka mata, saboda wani daddaɗan ƙamshi da ya ziyarci hancinsa, kuma ƙamshin ba na turera ba ne, na girki ne, hakan yasa ya kalli plate ɗin dake gabanta.
Sai da ya baɗiyi wani kakkauran yawu a sanda kalolin jallof ɗin gaban nata suka shiga idonsa, kayan lambun da ta ƙawata girkin da shi yasa girkin ɗaukar ido, ga kuma kamshin da girkin ke yi, kenan dai ta iya girkin kamar yadda ta faɗa?, kai ina!, ta ya za ayi ace wannan ta iya girki?, ai sai dai jagwalgwalo, don wata ƙila kyan da ƙamshin ne kawai, a baki ba llale abincin ya yi ɗanɗano me daɗi ba, saboda haka ba zai yi kasadar cin abun da zai zo ya ɓata masa baki ba, ko ma ya ɓata masa ciki, shi da ko abincin daren jiya bai ci ba.
Sai ya ƙi amsata ya juya zuwa wajen da ya saba a je kayan haɗa coffeensa, sannan ya haɗa shi a coffee maker, kafin coffeen ya haɗu, ya zaro wayarsa yana daddanawa.
“Abu Aswad! Na ga kayan girki, kuma nagode”
Sunan ɗazu ta kuma faɗa, hakan ya sa ya ɗago da kansa daga barin kallon wayar ya kalleta, a wannan karon ita ma shi take kallo, me makon ya bata amsa da baki sai ya gyaɗa mata kai. Yana ɗaga kafaɗa.
“Ga abinci nan na rage maka. Za ka ci?!”
Yawu ya haɗiya a fakaice, ya ɗan saci kallon abincin nata, a kan me zai ci wannan abinci? Zai fiye masa sauƙi ya sha coffeen sa, duk da ransa ya biya abincin, ga ƙamshinsa da ya cika masa hanci. Sai ya daure ya girgiza mata kai alamun a'a.
Juyawa ya yi ya kashe coffee maker ɗin, sannan ya fara firfita shi.
Mishal ta taɓe baki cikin faɗin.
“Ba dole ma mutum ya gamu da ulcer ba, ba tare da ka ci abicin ba  ka tashi ka ɗirkawa cikinka baƙin shayi da sassafe, kuma fa ita ciyawar shafin nan, amfanita a jikin mutu shi ne saka digestive system aiki cikin gaggawa... To ka tashi ka sha baƙin shayi ba tare da ka ci abinci ba, me zai faru kenan?!”
Kuliya ya aje mug ɗin hannunsa ya na kallonta, wai da shi take?, to ai shi ba ma baƙin shayi yake sha ba, coffee ne. Sai ya ƙi ya kulata, ya shiga shan coffeensa a nutse, har ta gama surutanta ta cinye abincinta ta wanke kwanukan ta ɗauki Ayra ta bar kitchen ɗin shi bai gama shan coffeen ba.
Ko da ya fito daga kitchen ɗin a falo ya sameta, zaune kan kujera tana kallo tv.
“Sai na dawo”
Ya faɗi murya ƙasa-ƙasa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama. Mishal ta miƙe tsaye, hannunta na hagu riƙe da Ayra.
“Na raka ka ne?”
Ya ɗan ja da baya ya na kallon kayan jikinta, har yanzu pyjamas ne, da alama ko wanka ma ba ta yi ba.
“Na gode. Ki kula da kanki”
Ya na ƙarashewa ya kama hanyar fita, bakinta ta taɓe tana zama, ai shi ya jiyo.
Yinin ranar haka ta ƙarashe shi cikin farin ciki, da rana sakwara da miya ta girka, kuma har me gadin gidan ta zubawa, da daddare kuma ta girka tuwon shimkafa, bayan ta ci, sai ta ɗan yaɓa aikin makaranta, kafin ta kwanta, ita zama cikin kaɗaicin ma sam be dameta ba, don ta saba zama ita kaɗai, bare kuma akwai girki, ga kallo ga kuma Ayra.
Mamakinta ɗaya, ta na som sanin dalilin da ya sa ya fita yau, bayan yau ana cikin weekend, kuma har ta kwanta bai dawo ba.
*Hotoro, Ring Road, Kano...*
“Sai na dawo Mesoma”
Cewar Uchechi tana rungume da yayarta, sakin juna suka yi Mesoman na mata murmushi, a satin da ya wuce Uchechi ta riga ta yankewa kanta shawarar tafiya Abuja, kuma ta yarda da za ta yi abun da Mesoman ta ce mata, don ta samu ta cimma burinta a kan Raja.
Wato bugar da shi ta hanyar saka masa maganin bacci a cikin abun sha, ta riga ta yankewa kanta hukuncin za ta iya, kuma ba ta jin akwai abun da zai dakatar da ita daga yin hakan. A da ta na tunanin ta ya za ta aikata masa hakan saboda su Rhoda dake tare da shi a koda yaushe, sai kuma ta samo mafitar ɗaukarsa ta bar gidan da shi. Za ta cemasa ya ɗauketa su fita yawo, kuma a wannan yawon da zai kaita za ta samu damar da za ta cimma manufarta a kansa.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja...*
“Nemo min lambar Nimra”
Cewar Jadda wadda ke danƙawa Hajjara wayarta, Hajjara ta karɓa tana yatsina fuska, don Allah ya san,i ita Wallahi ta gaji da zama da wannan masiffafiyar tsohuwar, duk ta bi ta isheta, Allah-Allah take ta koma Maiduguri.
Zaune suke a falo, daga can gefe kuma Mama Ladi ce ke bawa Daala abinci.
“Ga shi. Ta shiga”
Ta ƙarashe tana miƙawa Jadda wayar, Jadda ta karɓa tana tsara kalar masifar da zatawa Nimran.
“Falmata! Tun muna sheda juna da ke ki saka wanan ɗan yankan kan da ya aurar min jiki ya saketa, Wallahi idan ba haka ba zan ɗau mummunan mataki a kanku daga ke har shi!”
Kalamanta na farko kenan, bayan da Nimra ta ɗaga wayar, daga cikin wayar Nimra dake zaune a office ɗinta ta yi murmushi.
“Da ma na san mijin Mishal ɗin ne?”
“Ko kin san shi ko ba ki sanshi ba wannan be shafe ni ba, abun da na sani kawai shi ne ke ce kika danƙa masa jikata ya tafi da ita, don haka tun muna sheda juna ki nemo mun gidan da ya kaita, in ba haka ba!...”
Daga haka ta kashe wayar tana kumfar baki, A fakaice Hajjara ta saci idon Jadda tana watsa mata harara. Jadda ta miƙe tare da nufar hanyar ɗakinta rai a ɓace.
“Mtswww!, aikin banza, wai ita a nan me san jikoki, ƙaaaa!”
Ta ƙarashe da ƙwafa.
*
Jadda na sauƙe wayarta, Nimra ta lalubo lambar wani masanin kan na'ura me ƙwaƙwalwa dan ya binciko mata lambar Kuliya. Jim kaɗan sai ga saƙo ya shigo wayarta, kuma ba jira ta aika masa kira.
Daga can DSS Headquarter, Kuliya dake tsaye a ɗakin horo ya na hora wani me laifi ya ji kamar wayarsa na vibrating, hakan ya sa ya saki wayoyin lantarki dake hannunsa ya juya ya fice daga ɗakin, don ya samu ya amsa wayar, abakin ƙofar ɗakin ya iske Sharon, don haka ya yi mata alama da ita ta shiga ta ci gaba.
Ganin baƙuwar lamba ya sa shi ɗan jinkirtawa kafin ya ɗaga, kuma kamar ma ba zai ɗaga ɗin ba, sai da kiran ya shigo a karo na uku sannan ya ɗaga. Tun daga jin muryarta ya ganeta, hakan yasa suka gaisa a mutunce, kafin dalilin kiran ya taso.
“Magana ce a kan Mishal, ɗazu kakarta Jadda ta kirani. Wai ta na so ta san inda aka kai mata jikarta. Na san ko ni ban faɗa mata ba, za ta iya nemo address ɗin gidanka, Jadda bata san zaman lafiya, don haka ko da wasa kada ka bari ta ɗauki Mishal daga cikin gidanka. Saboda ko a sanda tana ƙarama Abubakar be bata renonta ba, bare yanzu da ta girma, zamanta a wurin Jadda ba ƙaramar matsala ba ce!”
Kuliya ya ɗan yi jimm, to a kan me ma zai bari wata Jadda ta ɗauketa?, ai a yanzu ba ya jin ko ita kanta Nimran za ta iya raba shi da Mishal, Mishal amanarsa ce, babu yanda za ayi ya bar wani abun cutarwa ya sameta, zai yi duk iya iyawarsa don ganin be bari an cutar da ita ba. Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya amsa mata da.
“Insha-Allah”
Daga haka ya mata godiya ya sauƙe wayar.
*Joy Emodi CI St.*
RABI'A POV.
Tafe suke ita da Raja a kan titin, hira yake mata jifa-jifa, sama-sama take ba shi amsa, don yau gaba ɗaya tunaninta ba ya jikinta, tunaninta ya lula kan maganarsu da Yaya ta jiya.
_“Rabi'a da ace kina sona, da za ki bi abun da na faɗa. Saboda Allah ya za'ayi ki riƙa kula wani da sunan me kamarki, kika sani ma ko ɗan satar mutane ne, ni dai gaskiya ki dena kula shi. Dan har ga Allah ba na so!...”_
Kalamansa gareta kenan a jiya da daddare da ya zo fira, ita ba ta ɓoye masa komai game da Raja, duk ranar da suka haɗu da shi sai ta faɗa masa sun haɗu da wannan me kamarta tata, abun da ko Anti Saratu ba ta faɗawa ba, shi ne; Raja na kama da ita, kawai ta faɗa mata cewar suna mutunci da shi.
“Ammata?”
Ya kira sunanta a lokacin da suka fita kan babban titi, juyowa ta yi ta kalleshi, a zahirin gaskiya ba za ta iya dena kula Raja ba, don tana da tabbacin shi ɗan uwanta ne, alaƙar jinin da suka haɗa ce ta sa ba za ta iya haƙura da shi ba, don a yanda take ji za ta iya rabuwa da Yaya a kan Raja, kuma akwai wani abu a kan Rajan dake motsi a ƙasan zuciyarta, duk da ta na amfani da duka ƙarfinta wurin danne shi, don bisa ga dukkan alamu hakan ba me iyuwa ba ne.
Ko kafin Raja ya kuma faɗin wani abu, wata motar taxi da ta tsaya a bakin titin ta ɗau hankalinsa, hakan ya sa ya ci gaba da kallon motar har zuwa lokacin da aka buɗe gidan baya na motar, Uchechi ta fito, fuskarta ɗauke da wani abu me kama da fushi da kuma ɓacin rai.
Hakan yasa fuskar Raja rikeɗewa zuwa mamaki, yaushe ta zo?, wa ya bata address ɗin inda yake?. Ganin yanda Raja yake kallon bayanta ya sa Rabi'a juyawa, kuma tana juyawar idonta ya sauƙa a kan wata budurwa dake tsaye kisabda wata motar taxi. Kallo ɗaya za ka mata kattabatar da cewa ita Cristian ce, saboda yanayin shigarta. Amma kuma ita Raja yake kallo ?, ko me?. To mi ye haɗinsa da ita?. Kuma ga shi ma ta ahiga tunkarosu.
Ba ta ankara ba ta ji hannun Raja cikin nata, sanna a hankali ya ja ta ya mayar da ita zuwa bayansa, dai-dai da isowar Uchechi gabansa, kuma tana zuwa ta ɗaga hannunta sama ta shararawa Raja mari.
Har saida ya karkatar da fuskarsa, Rabi ta tsorata sosai, ido waje take kallon gefen fuskar tasa. Zuwa lokacin har Uchechi ta fara hawaye, ta nuna Raja da ɗan yatsa ta na faɗin.
“Macuci. Ma ci yi amana, da ma ashe yaudarata kake?. Saboda wannan 'yar talakawan kake yaudarata?”
A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya juyo ya zuba lumsassun idanuwansa a kan Uchechi. Kafin ya furta abun da ya wargazo da duniyar Rabi da kuma Uchechin zuwa ƙasa.
“Uchechi! She is my wife to be. So show some respect!”
Bakin Rabi ya faɗo a har ƙasa, kallon bayan Raja kawai take tana ƙarawa, ai ba ta ganin fuskarsa, wata ƙila ma daga wani wurin maganar ta fito, ba daga bakinsa ba, inaa, wai Raja?, kai! Wallahi da sake, ba shi ya faɗi wannan zancen ba.
Uchechi ta fashe da matsanincin kuka tana cin kwalar Raja, dai-dai da isowar su Rhoda da suke binsu a baya ita da Alandi, dom cewa suka yi bari su je gulma, sai kuma Allah ya sa suka ci karo da wannan faɗan.
“Ke sakar shi!...”
Rhoda ta faɗi tana yin kan Uchechi, Raja ya ɗaga mata hannu alamun ta dakata.
“Ni za ka ci amana Raja?, Ni?, Ni Raja?, Idan ka isa Yesu ya kwashe min albarka!, A kan wannan ƙazamar za ka gujeni?...”
Tass!, ka ke ji, Raja ya wanke fuskar Uchechi da mari, hakan yasa ba shiri ta sake shi tana dafe fuskarta setin inda ya mara, hawaye wani na bin wani a kan fuskarta, ta ɗago da idanuwanta ta kalleshi.
Ba ƙaramin tsorata ta yi ba, ganin idanuwan Raja buɗe a kanta, wani abu da za ta iya cewa tsawon zamanta da shi ba ta taɓa gani ba, a ko da yaushe idanuwansa kusan a lumshe suke, amma yau ga su buɗe a kanta, sun yi jajawur, jikinsa har karkarwa yake dan ɓacin rai, mutanen dake wucewa har sun ɗan fara tsayawa tagumi, duk da layin babu mutane sosai.
”Don't you hare what i just said?, I said that she is my wife to be!, You better respect her before i injured you!”
Kuka sosai Uchechi ke yi, haka ta juya da gudu ta shige motar da ta fito daga ciki, ba ɓata lokaci motar ta bar wurin, ba ta taɓa tabbatar da cewa Raja ba ya santa ba sai yau, ta gaji da abun da ya ke mata, don haka za ta sakar masa mara ya yi fitsari, babu ita babu shi, za ta jurewa komai da zai mata amma banda cin zarafi. Ta haƙura da shi har duniya ta naɗe.
Da sauri Raja yake sauƙe nufashi, ya ɗaga hannunsa ya dafe goshinsa, zuciyarsa na bugawa da sauri, be so ya bayyanawa Rabi ta ji wannan sirrin zuciyar tasa a yau ba, ba yau ya kamata ta sani ba, ba a irin wannan lokacin ya kamata ta sani ba, ko wani kallo za ta masa bayan wannan abun da ya faru?, Oho.
Rhoda dake cikin farin ciki da ɓacin rai a lokaci guda ta dafa kafaɗarsa. Ta na cikin farin ciki jin yau Raja ya rabu da Uchechi, ya kuma bayyana sirrin zuciyarsa kan abun da yake ji game da Rabi'a, ranta kuma ya ɓaci ne saboda nasa ran ya ɓaci.
A hankali ya sauƙe hannunsa daga kan fuskarsa, sannan ya juya bayansa da sauri, ya kalli Rabi dake a sanƙare a wurin, kamar wata mutum-mutumi, kamar wadda aka manne mata ƙafafunta da glue me ƙarfi, kuma kamar wadda ta cillar da hankalinta a hanya, haka take jin kanta, duniyar ta mata shiru, babu abun da take ji sai muryar Raja cikin faɗin “She is my wife to be!”, anya kuwa tana cikin hayyacinta?, kamar fa ta haukace ma, yau in ba wadda ta yi hauka ba, waye yake jin abunbda babu shi a zahiri, ko kuma dai iskokai ne suka shiga jikin Rajan?, Oho, a'a abun zai fi kyau ace jikinta suka shiga ba nasa ba. Kanta ta ɗaga ta kalli fuskarsa, jin yana kiran sunanta.
Kallonta kawai yake, ya kasa cewa komai, don ya ma rasa abun da zai faɗa mata, sai kawai ya juya ya tsayar mata da mota, sannan ya kamo hannunta ya sakata a cikin motar, don ya ga kamar bata cikin hayyacinta.
A kan idonsa motar da ya sakata ta bar wurin, sannan ya dafe kansa cikin neman sauƙi, a bisa tsautsayi idonsa ya sauƙa kan wata rumfar me ƙosai, wutar da ya yi arba da ita tana ci a cikin murhunta ta tuno masa ƙiyayyarsa da wuta.
*2008.*
*Gidan Maman Rhoda, Kano...*
*08:30 PM.*
“Zaid miƙo min kwanon can!”
Cewar Maman Rhoda tana nunawa Zaid kwanon dake ɗauke da farfesun kifi, Zaid ya ɗauki kwanon sannan ya miƙa mata, zaune suke a kan carpet ɗin dake falo, Rhoda na daga gefen Zaid, yayin da Maman Rhodan ke facing ɗinsu, girkin ranar da suka yi ne zube a gabansu, yayin da suna shirin cin abincin dare.
“Mom ni kifin nake so kawai”
Cewar Rhoda tana shagwaɓe fuska, Maman Rhoda ta wurga mata harara.
“An ƙi a baki kifin, da ci kike ?, Kifi na Zaid ne kawai”
Zaid ya kunshe dauriyarsa ya na shafa kanta, kasancewar ta jingina da shi, Maman Rhoda ta zubewa Zaid gaba ɗaya kifin, sannan ta bawa Rhoda tata shinkafar babu kifi sai miyar kawai. Rhoda ta turo baki tana ture abincin, sannan ta miƙe ta bar falon da hawaye.
Nan da nan Zaid ya shiga damuwa, don Allah ya sani ba ya son ɓacin ran 'yar ƙanwar tasa, don haka ya miƙe, hannunsa riƙe da kwanon abincin nasa.
“Zaid ina za ka?”
Ba tare da ya juyo ba ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan yace.
“Abincin zan je mu ci”
“Da ka rabu da ita kawai”
“Ba zan iya cin abincin ba tare da ita ba!”
Ya amsa mata a lokacin da ya ke ƙarsa fita daga cikin falon, Maman Rhoda ta girgiza kanta tana murmushi, soyyayar Zaid da Rhoda sai kallo, ko ka shiga tsakaninsu kai ne za ka ji kunya.
“I'm sorry Cuzie”
Zaid ya faɗi a karo na biyu ya na kallon Rhoda, wadda ta cunkune tana wani kawar da kai, wai ita a dole an ɓata mata rai, tana zaune a bakin gadonta, yayin da Zaid ɗin ke zaune kusa da ita.
Ya na murmushi ya aje kwanon abincin a kan cinyarsa yana buɗe kifin, ya guntsuro tsoka ya haɗa da lomar shinkafar, sannan ya kai mata saitin bakinta, kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta buɗe bakin ya saka mata.
“Story time!...”
Sai ta juyo tana kallonsa da kyau, ta harɗe ƙafafunta a kan gadon, tana buɗe duka kunnuwanta dan ta ji labarin da zai bata. Ta san labaran Zaid, babu na yarwa.
“Wani Gayene ya zo Wajen Budurwarsa. Saiya Kira Yaro Yace mai; Kai je Gidannan Kace Sani Striker Na Kiran Hassana. Yaro Ya Antaya,yace wai Ana kiran Hassana. Babanta Yace waye Ke Kiranta? Yaro Yace Sani Striker. Sai Babanta Yace; Je Kace Isah Defender Yace Bata Zuwa” (Labaran musha dariya).
Yana ba ta labarin yana kai mata lomar abincin haɗi da kifin, yana kaiwa ƙarshen labarin Rhoda ta tintsire da dariya. Abincin ya ci gaba da bata ya na bata wasu labaran, sai da ta ga ta kusa cinyewa, sannan ta karbi kwanon, ita ma ta shiga ba shi a baki.
Kamar daga sama suka ji an banko ƙofar falonsu, hakan yasa ba shiri suka miƙe suka bazama zuwa cikin falon. Abun da suka gani ya bala'in gigita duniyar ko wannensu.
Maman Rhoda ce yashe a ƙasa, Bala ya danne mata kai, ga sauran yaransa su Garuje tsaye a bayansa.
Bala wani me kuɗi ne a unguwar kusa da ta su Maman Rhoda, ya na bawa mutane bashin kuɗi, musamman ma mata, sannan ya kan ƙawarawa mutane da kuɗin ruwa me yawa, idan kika ka sa biyan bashin kuma sai ya nemi ya fanshe a kanki, ga shi da tara yara 'yan daba, kasancewarsa ɗan uwan sanata ya sa ake ɗaga masa ƙafa ya na cin karansa babu babbaka.
Lokacin da Maman Rhoda za ta biyawa Zaid kuɗin makaranta gaba ɗaya har zuwa lokacin da zai gama, kuɗaɗen hannunta ba su da yawa, hakan ya sa ta karɓi bashi a hannun Bala, suka yi da shi kan za ta riƙa biyansa da kaɗan-kaɗan.
Kwana nan kuma sai ya bijiro mata da maganar ta ba shi kanta kawai, ita kuma sai ta nuna ƙin amincewarta, harda marinsa a yammacin jiya.
Shi ne kuma yau ya iyo musu dirar mikiya a wannan daren. A cikin wannan daren Bala ya yiwa Maman Rhoda fyaɗe a kan idon Zaid da Rhoda, waɗanda ke riƙe a hannun yaransa su Garuje, sai da Zaid ɗin ma ya yi ƙoƙarin kaiwa Balan farmaki amma Garuje ya riƙe shi tare da buga kansa a jikin bango, hakan ya haddasa masa jiri da fashewar goshi.
*
Sosai Maman Rhoda take kuka, Zaid da Rhoda rungume a jikinta, yayin da suke tsaye a harabar police station, bayan da ta kawo ƙara kan zalincin da aka mata, faɗar sunan wanda take ƙara ya sa 'yan sandan korarta har da haɗa mata da duka.
Babban tashin ha kalinta shi ne yanda Rhoda da Zaid ke cikin damuwa, ba za ta iya ɗaukan baƙin ciki irin wannan ba, hakan yasa ta fita wajen police station ɗin, ta siyo fetir da ashana, ta ture Zaid da Rhoda gefe, sannan a kan idon Zaid da Rhoda da kuma sauran jama'ar station ɗin.
Maman Rhoda ta ɗaga jarkar fetir ɗin nan ta tittila a jikinta, sannan ta kunnawa kanta wuta, Rhoda na kuka tana fisge hannunta daga ruƙon da Zaid ya mata, yayin da wannan wutar ke ci a kan idon Zaid, komai na cikin kansa ya taɓu, tsoron wuta ya kama shi, ya zamana ba shi da wata abokiyar gaba kamar wuta.
Don a lokacin suma ya yi, 'yan san dake da imani a wurin ne suka temaka musu, ita kam Maman Rhoda babu abun da ya yi saura a gawarta, ta ƙone ƙurmus, Zaid kuma ya suma, Rhoda kuma sai kuka take, ta rasa inda za ta sa ranta, ita a tunaninta shi mq Zaid ɗin mutuwa ya yi.
Kwanan Zaid ɗaya a aibiti kafin ya farfaɗo, kuma yabna farfaɗowar babu wanda ya samu kusa da shi sai Rhoda, haka ya ƙanƙameta suka rera kuka me isarsu, kafin ya ɗauketa suka dawo gidansu.
Haka suka ci gaba da rayuwa, sai dai ba kamar yanda suka saba a da ba, kamar yanda Maman Rhoda ta bar musu kuɗinta da kayan ƙosai da kokonta, haka suka ci gaba da yin sana'ar, kuma a ɓangare guda suna zuwa makaranta,  Zaid ne ya ci gaba da riƙe su har zuwa lokacin da shi ya kammala makaranta. Duk da Rhoda ce ke soya ƙosan, dan shi ya koma maƙiyin ganin wuta. Amma kuma ba ya bafinta ita kaɗai, duk inda za ka ganta to shi ma za ka ganshi.
Haka ya yi join wata University a nan cikin garin kano, don ba zai iya yin nisa da Rhoda ba. Da haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu, yau da daɗi gobe babu.
A lokacin da Zaid ya kammala karatunsa, sai ya shiga neman aikin DSS, aikin da ya sha burin yi tsawon rayuwarsa, aikin da yake kwana yake tashi da shi a zuciyarsa, aikin da suke da burin yinsa tun suna yara shi da ɗan uwansa.
Cikin ikon Allah ya samu, hakan tasa ya ɗauki Rhoda suka koma Abuja, kuma ita ma bayan ta gama makaranta sai ta ce tana san ta shiga aikin DSS ɗin, Zaid be hanata ba, sai ma shige mata gaba da ya yi har ta samu.
Shekerar Rhoda biyu da fara aiki, aka basu wani assignment me haɗari, wani assignment me ɗauke da sumatsi, wani assignment wanda ya shafi rayuwar ko wannensu, wani assignment wanda ya taho da guguwar ƙaddararsu, wani assignment wanda zai zama sanadiyyar faruwar wata ƙaddara, wadda za ta iya tarwatsa komai, sannan ta shirya wasu lamuran.
Assignment ne a kan wani me kuɗi wanda ake zarginsa da yin safarar makamai da kuma miyagun ƙwayoyi, Alhj Bala, wanda a lokacin yake zaune a garin Abuja. Daga Zaid har Rhoda babu wanda ya yi musu wurin karɓar aikin, don za su jefi tsuntsaye biyu ne da dutsi ɗaya.
Dole ta sa suka dawo garin Kano, don suna buƙatar bi ta hannun Garuje, babban yaron Alhj Balan, ƙarfi da ya ji suka koma 'yan daba, shi Zaid har da sauya suna zuwa RAJA. Sannan sun yi yarjejeniya da Rhoda kan idan sun kawo ƙarahen aikin za ta musulunta, babu yanda be yi da ita ba kan ta musulunta tun tana ƙarama, amma taƙi, sai yanzu ta yarda da hakan, shi ya sa Zaid ya zage damtse, don ya samu ya kawo karshen aikin ta ko wani hali, saboda ya na so ƙanwarsa ta samu rabauta, tun da Allah be sa Maman Rhoda ta samu rabon ba.
Kuma sun nemo wasu 'yan dabar kan titi guda uku, dan aikin nasu ya tafi dai-dai, Alandi, Zuzu da Jagwado, Zaid ya temaki rayuwarsu sosai, kafin ya ɗauke su aiki. Kuma a lokacin ne suka haɗu da Uchechi.
____________________
_Salmanians!... Ku ce kallon kitse mukewa rogo, ashe Raja ba ɗan ba ba ne, kai amma wanga bawan Allah an yi ɗan reni_
_Kada fa ku manta da sirrin zuciyar Zaid da ya bayyana ya fito fili, shin kuna ga Rabi za ta amince da shi?_
_Ku dai ku ci gaba da bi na  sannu a hankali, dan ganin wata waina za mu toya a feji na gaba_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 15 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LABARINSUWhere stories live. Discover now