LABARINSU 8

33 0 0
                                    
*LABARINSU*
*© SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*08*
~~~
*You deserve a love that goes to war alongside you, not against you* 
-Heart spekeaks-
***
KULIYA POV.
_🎶What should i do?_
_What should I do when we come face to face?_
_Should I cut my fingers while admiringly glancing at your beauty,_
_Like Qibdiyyat when the greatly admired Joseph?_
_Or Should I abnegate your humanhood by saying that you're a noble angel and exalt your creator?_
_How should I be in that day?......🎶_
A hankali waƙar what sould i do? ke tashi daga mpn motar Sharon, wadda Nura Ismail Abou Othaymeen ya rera.
Tayoyin matar na garawa a kan titi, yayin da Sharon ke zaune a mazaunin driver, shi kuma Kuliyan na zaune a gefenta yana kallon hanya.
“Ina muka yi sir?”
Ya juyo ya kalleta, sannan a hankali ya ɗaga kafaɗarasa ta dama. Yana mayar da dubansa gefen hanya.
“Gidan Anna”
Ya amsa mata a taƙaice, kuma daga hakan bai sake cewa komai ba, har suka iso gidan.
Ita ta zaune a mota shi kuma ya fita ya shiga cikin gidan. Babu kowa a falo, dan haka kansa tsaye ya nufi ɗakinta.
Tsaye take a jikin loka, ba zai iya cewa ga abinda take ba, amma ya ga sanda wani abu mai kama da farin ciki ya wulƙa ta cikin idonta, a sanda ta yi arba da shi. Kansa ya sunkuyar ƙasa, kafin ya ci gaba da takawa zuwa gabanta. Yana ƙarasawa ya rungumeta.
Anna ta rintse idonta, tana jin ƙwalla na shirin zubo mata, ba ƙaramar azabtuwa ta yi ba da hana kanta zuwa duba shi, sai dai ta yi hakan ne kawai don ta ganar da shi kuskurensa. Ba wai dan ba ta san ganinsa ba. Dan Allah ya ɗora mata san Kuliya tun ranar da ta fara ɗora idonta a kansa.
Ranar ita ce ke da dutyn yamma. Ta na shara a gidan marayun da ta samu aiki, wanda ke garin kano, a lokacin tana cikin matsananciyar buƙatar kuɗi. Hakan yasa a sanda aka mata tayin aikin ta karɓa ba tare da wani tunani ba.
A garden ta ga wani yaro zaune kan duwatsu, ya ba ta baya, hakan yasa ba ta kalli fuskarsa ba. Kuma ganinsa a wurin ya ba ta mamaki, don a lokaci irin wannan yaran gidan ba sa zama a ko ina da ya wuce islamiyya, don lokacin ɗaukar darasi ne. Kuma tasan da cewa sauran yaran yanzu haka suna can, amma to wannan me yake a nan.
“Kai yaro!, me kake a nan ?”
Ta tambayi abun da ke yawo a cikin kanta, a sanda ta ƙarasa kusa da shi, ɗagowa ya yi da kansa ya kalleta. A kallo ɗaya da ya yiwa matar ya ji cewar zai iya yarda da ita.
Saboda tun bayan zuwansa gidan marayun bai ƙara yarda da kowa ba, ba ya shiga cikin sauran yaran gidan, ba ya cin abinci tare da su, ba ya walwala, ba ya komai, sai tunanin ɗan uwansa da ya cika zuciyarsa.
“Ka na jin yunwa ne ?”
Annan ta kuma tambaya a wancan lokacin, sai ya girgiza mata kai.
Ita kuma sai ta gyaɗa kanta, don ta fahimce shi, da alama sabon zuwa ne, kasancewar ba ta taɓa ganinsa a gidan ba, kuma rashin sakewa na faruwa da sabbin zuwa gidan.
Hakan yasa ta zauna kusa da shi, ta na jingine tsintiyar hannunta a jiki wata bishi.
“Kana ji ko!, ban san me yasa ka zo nan gidan ba, amma ina fatan ka ɗau haƙuri, ka dangana da rashin da ka yi, dan nasan duk wanda ya zo nan to ya yi wani rashin ne... Idan ka kwantar da hankalinka, ka saba da kowa a nan ka ji?”
Maganarta da shi ke nan a wancan lokacin. A yanzu kuma sai ta ɗago shi daga jikinta tana kallon fuskarsa.
“Anna i am so sorry, ba zan sake ba...”
Ya zaɓi ya bata haƙuri, dan yasan fushi take da shi, Annan ta kai hannu ta riƙe fuskarsa.
“Ka kiyaye Aliyu, kasan da cewa ba mu da kowa sai junanmu...”
Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya gyaɗa mata kai.
Daga bakin ƙofar ɗakin, Siyama ta saki murmushi, haɗi da ajiyar zuciya, jin cewar masoyinta na cikin ƙoshin lafiya, a cikin kwana huɗun duk sanda za ta tambayi Anna game da shi ba ta bata amsa, sai dai ta yi banza da ita.
Ita kanta ta san cewar ta na cikin tashin hankali, dan har watq ƙwarya-ƙwaryar rama ta yi, ramar rashin sanin halin da abun santa ke ciki. Ta kuma yin wani murmushin, ta na karanta wasiƙar jaki, kanta take hangowa a tsakiyar hannayen Kuliya, wani mafarki da ta saba yinsa a farke.
Hannunta na dama ta kai  ta ɗan daki goshinta, sannan ta bar ƙofar ɗakin, ranta wasai.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja*
MISHAL POV.
Zaune take a falon gisansu, ta na rubuta assignment ɗin da aka basu yau, yayin da Daala ke zaune a gefenta, ta na yi ta na ɗan yiwa Daalan hira.
Takun da ta ji daga kan stairs yasa ta kalli wurin, ganin Hajjara ce yasa ta sakar mata murmushin mugunta, irin wanda take mata a duk sanda za su haɗa ido a kwanakin nan.
Sannan ta ci gaba da rubutunta. Wani malolon baƙin ciki ya tokare maƙoshin Hajjara, tun bayan ranar da suka dawo daga asibitin nan Abubakar ya hau fushi da ita. Sai da ta haɗa shi da kawunsu sannan ya saurareta, ba su shirya ba sai da ya bar mata kakkauran warning a kan Mishal.
A ranta ta yi ƙwafa, ta ma wurga mata harara, tare da kama hanyar kitchen.
“Haka fa... Ai tsakanina da ke sai hange daga nesa... Babu yanda za ki iya da ni Hajjara... Na zame miki ciwon ido, kuma ƙadangaren bakin tulu!”
Muryar Mishal ta dakatar da ita, juyowa ta yi ta kalli Mishal ɗin ba ita take kallo ba. Rubutunta ta ci gaba da yi, wata ƙwafar ta kuma yi sannan ta kaɗa kanta ta shiga kitchen ɗin.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
RAJA POV.
Zaune suke shi da Zuzu a falo, suna tsara yanda za su karɓo wasu kaya da Alhaji Bala ya saka su su karɓo masa, a kai  akai yake duba time. Dan ba ya san har lokacin ta shi ya yi ba tare da ya ganta ba.
A kwana biyun nan kullum sai ya fita ƙofar estate ɗinsu dan ya ganta, ko ba ta yi masa magana ba, shi yana ɗaga mata hannu, kuma ganinta na masa daɗi, don ya na ganin Momma in her. Kuma shi ne dalilin da yasa ya ke san ganin nata.
“...Ni zan fara zuwa, zan yi magana da su, idan ba su yi taurin kai ba... Shikenan, idan kuma sun yi taurin kai... Sai kawai kai ka fahimtar da su...”
Raja ya gyaɗa kansa cike da gamsuwa. Sannan ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Na fahimta”
Idonsa ya ƙara sauƙa a kan agogo, ganin lokacin ya cika yasa shi miƙewa.
“Ina zuwa Zuzu...”
Daga haka ya yi hanyar fita.
Zuzu ya yi murmushi, dan ya harbo jirginsa, ko su kansu za su so ya samu wannan yarinyar me kama da shi, tun da duk lalacewarta ita musulma ce, ba kamar Uchechi ba. Duk da suma ba hankali suka cika ba, amma sun san abinda ya dace.
RABI'A POV.
“Sorry Anti Adawiyya...Wallahi na je class ɗin kung fu ne, shi yasa na makara”
Cewar Mishal a sanda ta matso kusa da Rabi'a dake jiranta a compound ɗin makarantar. Rabi'a ta yi murmushi.
“Karki damu ƙanwata”
Mishal ta miƙa mata ƙatuwar ledar dake hannunta, sannan tace.
“Ga shi Anti...”
Rabi ta sa hannu ta karɓa,bkafin ta buɗe ledar tana duba abin da ke ciki, atamfofi da lesuka ta gani a ciki, kuma da alama kayan a ɗinke suke.
Mishal ta ci gaba da kallonta cike da tausayawa, don tun bayan da ta bata labarinta tausayinta ya ƙara kamata. Kuma a jiya bayan ta koma gida, ta ɗebo gaba ɗaya kayan sallarta da tai alƙawarin kai mata, ta haɗo da duk wani kayan atamfa da ta san ba sawa take ba, ta haɗa ta aje da zummar za ta kawo mata.
“Sis...”
“Pls don't... Tun da har kun zama 'yan, to babu godiya a tsakaninmu”
Ƙwalla ta taru a idon Rabi, amma sai ta gyaɗawa Mishal kai.
“Zan wuce... Baba Ali ya zo tun ɗazu, Sai gobe”
Ta ƙarashe ta na barin wuri, Rabi ta rakata da murmushi.
Mishal na isa wurin da motar Baba Ali take ta faɗa ciki.
“Hafsatu ya aka yi kika makara yau ?”
Muryar Baba Alin ta tambaya, yayin da yakewa motar key.
“Malamin kungi fu ɗinmu ne ya makarar da mu”
Bai sake ce mata komai ba, ya juya kayan motar suka fita daga makarantar. A tsallaken makaranatar idanuwanta suka hango mata shi, wannan fuskar irin ta Adawiyya. A lokacin da ta ganshi, ta ɗauka cewa ɗan uwanta ne, amma sai ba ta cewa Adawiyyan komai ba. Ta jira har zuwa lokacin da Adawiyyan ta bata labarin rayuwarta. Ta yi zaton zata ce mata tana da wa na miji, amma ba ta ji hakan ba.
Kuma rashin jin hakan ne yasa ta ɗora ayar tambaya kan lamarin, duk yanda aka yi Adawiyya ta haɗa jini da abokin yayanta. Dan kamar ta wuce kama haka kawai.
Sai mamakin son sanin abin da ya kawo shi wurin ya kamata, me yake a nan ɗin?, sannan me yasa yanayinsa ya sauya ?, duk da a sanda ta ganshi yana cikin halin jinya, hakan bai hanata ganin buɗar idonsa ba. Sai dai yau kuma idon nasa kusan a lumshe suka. Ko dai ba dhi da lafiya ?. Da saƙe-saƙen nan a ranta har suka bar layin suka hau kan titi.
Rabi na fita daga gate ɗin makarantar idanuwanta suka hango mata shi tsaye daga can tsalleka, ya jingina da jikin bango, sanye yake cikin wata orange T-shirt, da farin chinos trouser. Hannaynesa duka biyu sanye cikin aljihun wandonsa. Waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallonta ƙasa-ƙasa.
Kusan kullum a kwanakin nan sai ta ganshi tsaye a wurin, ba ta san me yake ba, amma kamar jikinta na bata cewar bibiyarta yake, ko kuma yana tsayawa ne a wurin kawai dan ta fito ya ganta.
Kanta ta ɗauke, tare da gyarawa ledar hannunta riƙo. Ba tare da ta sake kallonsa ba, ta kama hanyar da ta saba bi.
Sai da Raja ya gama ƙare mata kallo, zuciyarsa na faɗa masa abubuwa da dama a kanta, kafin ya ga ta kama hanya tana tafiya. Wani abu daga can ƙasan zuciyarsa yace masa kawai ya bita.
Bai yi wata-wata ba wurin bin umarnin, ƙafafuwansa suka soma takawa cike da nutsuwa. Har ya kai kusa da ita, a yayin da suka ci gaba da tafiya tare.
Rabi ta yi saurin juyowa ta kalle shi, jin an tsaya kusa da ita, wannan fuskarce dai, mamallakin fuskar ne ke biye da ita. Sai dai ba ita yake kallo ba, hanya yake kalla, kuma har zuwa lokacin hannayensa cikin aljihu.
“Sannu Ammata!”
Wannan salihar muryar tasa ta furta ya na ci gaba da kallon hanya, sai da gaban Rabi ya faɗi, saboda yanda amon muryar tasa ya kunna wata jiniya a cikin kanta. Ta haɗiye wani abu sannan tace.
“Sunana Rabi'a...”
“Na sani ai, Ammata!”
Ya yi hanzarin katseta. Rabi ta ɗauke kai tana kallon hanyar ita ma.
“Daga ina kike zuwa nan ?”
Ya tambaya yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, tare da zaro hannunsa na dama daga cikin aljihu, ya kaishi bayan wuyansa, saitin inda tatto ɗin kan zaki yake, yana sosawa.
Rabi ta ɗan kalleshi kaɗan, sannan ta amsa da.
“Unguwar Madallah, Suleja!”
Ta lura da yanda ya ɗan tsaya da tafiyar da yake, kafin kuma ya ci gaba, sai a yanzu ya kalleta tun bayan da ya tsaya kusa da ita.
“Kusan tafiyar muntuna arba'in fa kenan ?”
“Umhum”
Ta amsa da ɗan sakewa, ba kamar yanda suka fara hirar ba.
“Amma me yasa kike zuwa nan ?”
Rabi'a ta ɗan sunkuyar da kanta ta kalli yatsun ƙafarta, sannan tace.
“Aikin shara da goge-goge nake”
“Ba kya zuwa makaranta ?”
Ya kuma tambaya. Sai ta gyaɗa kanta.
“Eh, ba na zuwa..”
Ta ba shi ahi amsa a dai-dai lokacin da suka iso bakin titi, sai ya dakata, hakan yasa Rabin ma dakatawa.
Shiru ya ratsa tsakaninsu na 'yan wa6sy muntuna... Kafin Raja ya ɗaga hannunsa ya tsayar wani mai mota, sannan ya buɗe mata gidan baya.
“Zo ki shiga 'yan mata!”
Rabi ta kalleshi,sannan ta kalli motar.
“Akwai bus...”
“Ammata ba'a mun musu, just enter, kin fahimta ?!”
Rabi'a ta haɗiye wani abu, dan ya yi maganara ne yana kallonta da ƙwayar idonsa da take gray color.
Ta tara yaɗonta gu ɗaya, sannanta shiga bayan motar, ciniki suka yi da mai motar, ya zaro kuɗin ya biya, har da haɗa shi da gargaɗin kada ya ɗauki wani bayan ita, sannan kada ya yi gudu da ita.
“Sai gobe 'Yan mata”
Ya faɗi sunan in full, saɓanin da da yake faɗarsa a wata sigar. Rabi'a ba ta iya ce masa komai ba, sai hannun da ta ɗaga masa. Motar ta fara tafiya, zuciyarta na ƙara cika damamaki da tunanika iri-iri.
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
Tsaye suke a ɗakin tattaunawa na headquartern, yayin da ya buɗe musu map ɗin wurin da za su wa dirar mikiya a yau ɗin nan, don a yau aka basu damar kamo 'yan ta'addan da suke bincike a kansu.
Sharon, Kamis, Sani, Mubarak, Symon da kuma shi kansa, su ne tsaye, kana kewaye da teburin da taswirar ke kai.
“Wannan ita ce hanyar shiga gudan... Ta nan za mu shiga, akwai ƙofa ta baya, dan haka za su iya guduwa idan suka gane cewa muna cikin gidan... Dan haka Ab...”
Bai ko ƙarasa furta sunan Abubakar ɗin ba, Abubakar ya turo ƙofar ya shigo, a tare suka ɗaga kai suka kalleshi. A gurguje ya ƙaraso ya tsaya a jikin teburin shi ma.
“I'm so sorry guys, cinkoson ababen abun hawa ne ya makarar da ni”
Kuliya ya haɗiye wani abu, a sanda ya ɗora idonsa a kansa, kammaninta suka faɗo masa a rai. Yarinyar nan ta rakurawa tunaninsa, ya gaji!, me yasa wai take damunsa ne ?. Sai ya ɗaga kafaɗarsa, sannan ya juya ya ci gaba da kallon taswirar.
“Abubakar kai da Symon za ku tsaya ta nan, ni da Sharon, Kamis da Sani, za mu shiga...”
Bai ƙarasa ba Abubakar ya dakatar da shi, ta hanyar furta abun da zai zama sanadiyyar faruwar ƙaddarar da Allah ya hukunta a wannan ranar.
“Me zai hana ni da kai, Sharon, Kamis da Sani, mu shiga cikin gidan, Symon da Mubarak sai su tsaya a ƙofar baya!...”
Cike da gamsuwa Kuliya ya gyaɗa kansa.
“Well, hakan ma ya yi, Good to go guys!”
“Yes Sir!”
Suka amsa kusan a tare, sannan suka yi azamar fitar.
*Abacha Road, Abuja...*
Motoci ne guda biyu suka yi parking a ƙofar wani madai-daicin gida, cikin gaggawa ƙofofin motocin biyu suka buɗe a tare.
Kuliya, Mubarak, Sharon, Kamis, Symon, Sani da Abubakar  suka fito, kowannensu sanye da baƙaƙen kaya irin na aikinsu, jikin bullet proof jacket ɗin kowanne daga cikinsu an rubuta 'DSS' da farin rubutu.
Kowanne a cikinsu hannunsa riƙe da bindiga, Kuliya ne ya yi wa Symon da Mubarak alama da su zaga ya ta bayan gidan, cikin sassarfa suka bi umarninsa. Shi da sauran kuma suka nufi cikin gidan. Shi ne kan gaba, su kuma biye da shi.
Daga cikin gidan kuma, mutum biyar ne zaune kan kujeru, baje a gabansu kayan maye ne kala-kala, mace ɗaya ce a cikinsu, yayin da sauran suka kasance maza.
“Chizoba, wai ka biya me tifar nan da ya kaɗe Kuliya ?”
Ogansu dake zaune kan kujera ya tamabaya cikin harshen igbo. Chizoba ya amsa masa da:
“Eh mana, dubu talatin na bashi”
Ogan ya yi dariya, yana hango nasarasu a cikin idanuwansa, a sanda suka sauƙa a garin sai da aka sanar musu da cewar wani wai shi Kuliya zai kawo musu cikas.
Kuma da suka bincika sai suka samu cewa ma a kansu yake bincike, hakan yasa suka saka wani me tifa ya daki motarsa, a sanda ya tashi daga wurin aiki.
Yanda suka ga motarsa ta yi raga-raga ne yasa suka ɗauka cewar ya mutu. Babu wani mai basu matsala kan aikin da ya kawo su garin Abuja.  A tunaninsu kenan, sai dai cikin abin da bai fi muntuna uku ba, komai ya sauya.
Gidan ya karaɗe da ƙarar harbe-harbe. Daga waje babu abin da ke tashi sai ƙarar musayar wutar da ake tsakaninsu da su Kuliya.
Kuma a cikin musayar wutar ne, ɗaya daga cikin 'yan ta'addan ya aikowa da Kuliya harbi, kasancewar shi bai lura ba, yansa harbin bai same shi ba, Abubakar da ya ankara ne ya hankaɗashi gefe. Shi kuma harbin ya same shi a ciki!.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*
RABI'A POV.
_🎶Bari ki ji, ki zauna_
_Batun so na zana_
_in zanyi batun ƙauna, za ki shigo labarina_
_Na zaga duniya_
_Ko wacce nahiya, na zamma jan wuya, amma kin saita ni da ƙauna🎶..._
Waƙar Idan babu ke, wadda Umar Mb ya rera ce ke tashi ta cikin wayar Anti Saratu, wadda ke kwance ta na sauraren waƙar, yayin da take daddana wayarta.
Daga can gefe kuma Rabi ce ke gogewa kayanta, Fatima kuma na daga ɗayan ɓarin tana tsifar kai, daga cikin ɗakin Habiba kuma, Mahmud ne kwance yana bacci, yayin da ita kuma Habiban ke bakin ƙofar ɗakin, ta na kaɗa wani abu a cikin kofi.
Ɗaya daga cikin magungunan da Malamin yayarta ya bata ne, kuma yace a haɗa da madara, ta sa an siyo mata madarar, shi ne yanzu take haɗawa, zuciyarta cike da fatan kasancewar abin da take fata.
“Anti Saratu Yaya yace min jiya an yi wasa” Cewar Rabi, tana motsa iron a kan kayanta.
Daga kan katifa, Anti Saratu ta ɗan kallota sannan tace.
“Ko na baki ki je ki turo ?”
Da sauri ta gyaɗa mata kai. Anti Saratu na murmushi ta miƙe zaune, sannan ta kashe waƙar ta miƙa mata wayar.
“Dan Allah ki ce masa nima ya saka min sabbabin fina-finan indian hausa guda uku... Nawa zan bada ?”
Rabi'a na saka hijabi ta yi dariya. Kullum idan za ta je turi shagon Yaya Sai Anti Saratu tace za ta biya kuɗi, shi kuma baya fasa cewa ba zai karɓa ba. Ta karɓi wayar tana faɗin.
“Ni na gaji da garan bawul ɗin da kuke da ni, nasan cewa zai yi an yafe miki, dan haka ki bar kayanki”
Anti Saratu ta yi murmushi tana kwanciya.
“An ji asara dai, daga bin maza sai kallon wasan maza, mtswww!”
Cewar Fatima tana makowa Rabi harara, Rabi'a ta juyo ta kalleta, du-du-du a shekaru Fatiman ba za ta wuce 14 ba, amma yanda take mata rashin kunya kai kace sa'arta ce.
“Fatima! Ba na hanaki yin wannan rashin kunyar ba? Ko Rabi'a sa'arki ce?...”
Rabi'a ba ta tsaya ta gama jin faɗan da Antu Saratu ta fara ba ta kaɗa kanta ta fita. Tana saka takalmi suka haɗa ido da Habiba. Ba tare da sanin daliliba ta ji gabanta ya faɗi.
Saurin dafe ƙirjinta ta yi tana karanto duk addu'ar da ta zo giftawa ta tunaninta. Ta ƙarasa saka takalmin, sannan ta kama hanyar fita.
“Ke Rabi! Zo nan!”
Kamar daga sama muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta tsaya da tafiyar, gabanta ya ci gaba da bugu. Tsoro ya mamaye mata ruhi. Da ƙyar ta iya juyowa ta kalleta. Suka haɗa ido, ba shiri gabanta ya ƙara tsnanta bugu.
Haka kawai ta ji ba ta yarda da wannan kiran da ta mata ba, ta haɗiye wani kakkauran miyau, sannan ta soma takowa zuwa gareta. Kusa da ƙofar ɗakin ta tsugunna.
“Ungo shanye!”
Habiba ta faɗa tana miƙo mata wani abu a kofi, kallon abun dake cikin kofin kaɗai ya haddasawa Rabi faɗuwar gaba fiye da ta da. Ta juya kallonta kan Habiban, ta ga yanda ta tsareta da ido.
Hannunta na rawa ta kai ta karɓi kofin, sai da ta raintse idonta, ta yi bismillah, sannan ta kafa kai ta shanye abun cikin kofin. Taste ɗin bakinta ya mata wani iri, dan abun sam ta kasa gane na miye, sai dai tana da tabbacin koma miye sharri ne. Kofin ta aje mata a gabanta, ta miƙe, ta kama hanyar fita.
Habiba ta bi bayanta da kallo tana murmushi, tasan kamar yanda yayarta ta faɗa mata ne, komai ya zo karshe tun da ta sha wannan abun, saura kuma jiran ganin sakamako.
“Honeynah, Ya kika yi shiru?”
Muryar Yaya ta faɗa, yayin da yake kallon Rabi'a, wadda ke zaune a kan wani benci dake bakin shagon, shi kuma yana daga cikin shagonsa, wayar Anti Saratu riƙe a hannunsa, yana tura mata abubuwan da Rabi'an ta lissafa masa.
Rabi'a ta sunkuyar da kanta ta na murmushi.
“Ni kam ina san wannan kunyar taki, tarbiyyarki da kyawunki su ne ke ƙara min shauƙin ƙaunarki Rabi'ata...”
Rabi ta ƙara sinne kai tana wani murmushi me kama da dariya.
Shi ma Yayan murmushin ya mata, yana juyar da kansa ga turin da yake mata. Kafin daga bisani ya shiga ba ta labarin yanda wasan jiya ya kasance, dan yasan yanda take matuƙar san ball, kuma shi ma yana tayata.
Sai da suka ɗan taɓa hira, sannan ta masa godiya ta fito daga shagon. Wata mota ta ga ta yi parking a bakin titi, kasancewar shagon Yayan a bakin titi yake. Fuskar Mama ta gani a gaban motar zaune a gefen drivern.
Kanta ta girgiza kawai ta yi gaba, ta zo wucewa ta kusa da wasu matasa dake kan benci suna hira, hirar ta su ta ɗauki hankalinta.
“Wannan 'yar gidan tsohon najaduncan ce ko?”
Na kusa da shi yace.
“Ko ba Mama ba ?, Ita ce, kai kuwa barewa ba ta yi gudu ɗanta ya  yi rarrafe ?... Ai kamar Kumbo kamar kayanta ?”
“Allah ya kyauta mana kawai...”
Sauri ta ƙara, gudun kada ta ji abun da zai sa ta fashe da kuka nan take.
Daga can cikin motar Mama ta shagwaɓe fuska tana kallon sabon Alhajin da ta yi.
“Gaskiya Baby ni sati zamu yi”
Alhajin ya yi dariya irin tasu ta goggagun 'yan bariki.
“Baby Mamancy! Ai sai yanda ki ka ce, idan kin ce mu yi wata ma babu wata matsala”
Daɗi har ran Mama, ta je ta yi wata a England ita da wannan Alhajin?, ai har ta hango irin kuɗin da za ta yi.
“Shikenan, zuwa yaushe za mu tafi?”
Alhajin ya shafo ƙaton tumbinsa, sannan yace.
“Nan da next week, kawai dai ki zama cikin shiri, sannan ki aikomin da hotonki na passport”
“To sai na jika”
Ta faɗi tana masa wani farrr da ido, sannan ta kama ƙofar motar ta buɗe.
Idan ka hangeta daga nesa, cewa za ka yi sam ba ta haɗa jini da hausawa ba. Wata matsataiyar duguwar riga ce a jikinta, sai wani ɗan fingil-gilin mayafi da ta riƙoshi a hannunta.
Small knotless barid ɗin dake kanta, wadda aka kitsa mata ita da wani golden attachment ta sauƙo tana lilo a gadon bayanta. Fatar jikinta har wani pink-pink take, don tsabar man bleaching ɗin da take shafawa. Ga wani nose ring da ta saƙala a gefen hancinta. Duk wanda zai mata kallo ɗaya, a tashin farko zai kirata da karuwa!.
Ko sallama babu, haka ta sa kai a cikin gidansu. Habiba da har lokacin na zaune a ƙofar ɗaki ta miƙe tsaye tana washe baki. Ganin Maman ma na fara'a.
“Umma, mu shiga daga ciki”
“To...To!”
Habiba ta faɗi cike da zumuɗi, ɗakin nata suka shiga, ta tsaya tana kallon Mama, tana jiran abun da za ta faɗa.
“Wannan sabon Ahajin da na yi ne, tafiya ta kama shi zuwa ingila, kuma yace da ni zai tafi”
“Ayyirri!...Yirriri!”
Habiba ta rangaɗa guɗa tana kama danannen hancinta hancinta.
“Ni na san ban yi haihuwar banza ba, ni da kaina na san cewa na yi farar haihuwa... Ingila fa Mama?, Ƙasar turawa ?”
“Nan fa”
Mama ta tabbatar mata murmushi kwance kan fuskarta data sha mai.
Saratu da Rabi dake ɗaki suna iya jiyowa komai, zuwa lokacin Fatima ba ta ɗakin, dan Anti Saratu gama mata faɗan ta tashi ta fice ta bar gidan gaba ɗaya. Anti Saratu ta girgiza kai cike da takaicin mahaifiyarta da ƙanwarta.
Rabi da ta fara kallon wasan a waya ta kalleta.
“Ba ƙunci ya kamata ki yi ba... Ki musu addu'a kawai”
Anti Saratu ta yi murmushi.
“A kullum ina yi Rabi, amma gani nake kamar abun nasu ba na ƙare ba ne”
“Kada ki ce haka Anti Saratu, Allah ma jiroƙon bayinsa ne, ki dage da addu'a, Allah zai amsa miki ”
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters*LABARINSU*

#TaurariWriters

LABARINSUWhere stories live. Discover now