LAIFINA NE 27

85 12 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

PAGE 2️⃣7️⃣

Bangaren Muhseen
    Daren jiya sam beyi bacci ba saboda text din da Fauxeey ta turamai, da dama ya dena bata lokacinshi dan akwai wanda zata aura, Abun tsayamai a rai yayi dan haka yau da sassafe ya yashi tsab yai wanka ya shirya yazo yabiyo hanya inda yake tinanin zaiga Fauxeey samun waje yayi yai parking, ya fito ya zauna samar booth din motar, kallo daya zakaimai kasan kudi sun zauna mai a jikinshi dan kosasshe ne ga kyau masha Allah

Fauxeey kuwa fitowa tai da zumbulelen hijab dinta tana tafe tana waige waige kamar mara gaskiya, tundaga Nesa Muhseen ya hangota ya fara murmushi yaji sanyi a ranshi
   Tana tafe abunta Bata sama bike ba (Mashin), tazo daidai inda Muhseen yake, Sallama yai mata ga mamakinshi sai ta tsaya

Bayan sun gaisa yace baki ganeni ba? Kanta na kasa sai a lokacin ta dago kanta sosai ta kalleshi, Tabbas bazata manta da fuskar nan ba tace kamar kune wanda suka tsayar dani rannan ko?
   Abun yabashi mamaki yace eh Mune, Tace Ayyah so ya kake ina dan uwanka? Yace lafiya lau

Yace Wallahi tun ranar dana ganki nakejin shaawar kasancewa dake, Har wani gida naje akaban numberki, Yana magana ta gane gidan su baba mairo yaje,

Yace ina miki text ina kiranki bakya mun reply, karshemai kikace Kinada wanda zaki aura

Kunya ya kamata tace dan Allah afuwa, yace bakomai yanzu ina zaki haka? Tace wani gidane chan yace ok Shiga motar inkaiki mana

    Aranta tace tab yaushe zan bari kasan gidan kawai ka batamun Plan dina, Murmushi tamai tace aa kaga Ba nisa yanzu zan karasa

"Yace to bakoma zai dinga kiranki muna gaisawa tunda kince akwai wanda zaki aura
   Uhm kawai tace aranta tace bakasan Chakwakiyan dake kaina bane

Sallama sukai tai Tafiyarta ta barshi a wajen, Da yake yadan taba karatun psychology kadan yagane Akwai damuwa a tattare da ita, kuma meye take boyemai da bataso a san inda zataje,

shuru yai yana nazarin sanda yaje gidan su baba mairo inda aka bashi lambarta, suma sunce Basusan daga inda takeba, basusan gidansuba Wai aiki tazo yi
     Kai bazan barta ba yace, akwai abunda take boyewa,

Wani me mashin ne yazo wucewa ya tsayar dashi, Ya bashi kudi yace yabimai yarinyar chan duk inda taje har yaga gidan da zata shiga, Sannan ya dawo ya fadamai yana wajen zai karamai kudi, Yace amma kai ahankali karta gane kana binta

"Mai mashin yaji kudi yace Ok Angama, nan take ya bashi 2000 yace ya dawo ya amsa 3000
Me mashin bin Fauxeey yai ahankali har seda yaga fauxeey ta shiga gidan su Bobo, Kowa yasan bobo a garin bayaji, Kuwa yasanshi da halin rape, rike baki yai yace to fa

    Reverse yai da mashin dinshi yace Gaskiya yallabai Gidan da naga yarinyar ta shiga yaban mamaki Gidan su Wannan yaron nanne da kowa ke kuka dashi a ung

Muhseen yace wane kenan? Me mashin yace gidan Su Bobo,
Shuru Muhseen yayi yana nazarin maganar,

Kallon mai mashin din yayi yace da gaske kke? Me mashin yace kasan bazan maka karya ba idan ma baka yarda ba kazo muje ka tambaya me gadin gidan kasan kuwa ba yanda za'ai me gadi yai karya dan Duk wanda zai shiga se an budemai kofa

Muhseen shuru yayi yace Ok to bakomai nagode, ciro 3000 yayi ya bashi kamar yanda yai mai alkawari,

Me mashin yace nagode,  amma ina mai baka shawara ko auranta zakai ka tabbata ka nema gaskiya, Dan Duk wanda ake ganinshi a gidan kallon uku saura kwata akemai, Ya buga mashin dinshi yabar wajen

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now