LAIFINA NE 42

77 11 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

   '''This page goes to *UMMIEY XEEY* Ina matukar Sonku kuma comment dinku nasani nishadi....Thanks 4 ur luv and support❤️💙'''

*PAGE 4️⃣2️⃣*

Ummiey da gudu taje ta rungume Fauxeey, Dr Muhd da lukman Da Muhseen suka koma yan kallo a zuciyar Dr Muhd yace dama sunsan junane dan shidai yasan fauxeeya patient din Muhseen ne shi ya kawota asibitin

Kallon juna suka sakeyi suka kara rungume juna, Mamansu itama ta karaso fauxeey  ta rungumeta tana kuka me taba zuciya tana Mama I missed you

Sudai Su Dr Muhd suna tsaye suna kallon Ikon Allah,

Fauxeey ce tace Meya kawoku nan? Ko kunji labarin ina nanne?

Mama ma abun mamaki ya bata kamar a mafarki, kallon Dr muhd tayi tace Nagode Maka Sosai matuka, ka cika Alkawari

   "Dr Muhd yace Mama Ni banma santa ba Ga wanda ya kawota nan Ya nuna Muhseen, ya kara da cewa kodai itace Fauxeeyan ki?

Mama Tace itace Fauxeeya na yau kwana 3 ban gantaba, Daga Zuwa aiki, Tace aiki sun mata yawa a offfice karshe dai tace mana anyi kidnapping dinta

Muhseen Yace ikon Allah, ni kuma ba haka tacemun ba dan ko inda Na Ceto ranta ba Aikin Office bane gaskiya a wani gida ne
   
Gaban Fauxeeya ne yai mugun fadi tace yau na shiga Uku, Asirina zai tonu, ya Muhseen zai kalleni sannan Na boyewa mahaifiyata 

Mamanta maido da hankalinta kan Muhseen tai tace" a ina ka Ceto ranta?

Yace Maganane me tsaho gaskiya, Ya kamata mu sama waje mu zauna,

Dr Kallon agogo yai yaga lokacin tashin shi ya kusa, ya kallesu yace ina fatan duk kunsama lafiya ko? Sukace Eh, Yace to Alhamdulillah shiga pharmacy yayi yadan harhada musu maganguna ya kawo masu Sannan dukansu suka Dugunzuma Suka wuce Gidan Su Hajiya mama,

   Fauxeey kuwa gabanta se fadi yake mata gashi yaune ranar farin cikinta amma Kuma da alamu zai koma ranar bakin cikinta.....

Sauka sukai Dukansu Gidansu Hajiya mama, nan suka shiga falonsu dan madaidaici gaba dayansu suka zauna

  Nan Maman Su fauxeey ta umurce Da Muhseen ya fada Komai kar yai mata karya gaskiya kawai takeso, Nan ya fara bata labari tundaga ran daya fara ganinta lokacin suna Lukman, Har izuwa gidan da take aiki, be boye mata komai ba hatta number ta wani gidan akaje aka bashi, shi harga Allah yanasonta amma yanda ta nuna bata sonshi ya kyaleta amma Still yana binta dan shi yaji a jikinshi mutumiyar kirki ce

Yace da har nai fushi ban sake dubata ba se jiyan nan na bude waya saboda ita naga texts dinta shine nai azama naje na ceto ta

Tunda Muhseen ya fara maganar Gaba daya fauxeey taji kunya,

Yana gama maganar Maman Fauxeey ta wanketa da mari guda Biyu zafafa, Tace Kinbani kunya, Wato duk Abunda nake fada maki bakiji ba kenan ko? Me kikaje yi gidan mutane me kika nema kika rasa a fadin duniyar nan, Ubanku ya barmuki arzikin da har jikokinku bazasui talauci ba amma wani irin taurin kaine gareki?

"Ni mun dauka ma Wallahi sune Suke farautar rayuwarmu har yanxu ashe Ke kika Kai kanki, Haba Fauxeeya

Sharr sharr hawaye ya fara zubo mata tace Mama Dan Allah kiyi hakuri ki yafemun

Muhseen da Dr Muhd yace Suwa suke farautar rayuwarku dan Allah munason Muji ko kadan ne?

Mama tace dole in sanar daku yanda kuka temakemu

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now