uncle naseer

449 57 3
                                    

Part 13&14

08109939902 WhatsApp only....

..kyam takame awajen ko motsi kasayi tai..."muje koh maman baby" taji anfada daga bayanta.. murmushin dole ta kakalo ,kana tacewa abdulmaleek "au I'm sorry"... Tafada tana mai nufar cikin gidan zuciyarta fal da tinanin uncle naseer.... tai Nisa atinani batare datasan  sun karasa kofar part din gidan ba...sai dataji muryar haleema wato matar abdulmaleek tana cewa.."au sister kece agidannamu,ina yallaban,yake,koh yana sauri yajuya ne?" Kasa cemata komai tai sai murmushin dabaika zuciba datai mata...kama hannunta da akaine yasa ta saurin dawowa hayyacinta ... Murmushi tai mata batare data ce komaiba,don ita yanzu babu abun da yake mata yawo azuciya kamar tasan inda mijinta yanufa...har dakin da aka tanada dan baki halima ta kaita,itadai sai binta da ido take ,duk kuwa takalar ta da magana datakeyi... ganin kamar akwai abun da yake damunta ne yasa halima kyaleta tare dayimata saida safe......hartakai bakin kofa kuma saita juyo tace"idan kina bukatar wani abu feel free to call me,ga wayacan a kan mudubi,zan aiko maid dinmu takawo miki dinner,kidaure kici kinsan ba ason mai ciki tana zama da yunwa, saida safe" tafada tana murmushi sannan taja mata kofa tafita....

Neman waje najma tai a edge din gadon tazauna,tana mai rafka tagumi..."oh Allah,kakare min mijina aduk inda yake,don tsarkin zuciyar annabi Muhammad s.a.w ,innalillahi wa inna ilaihirrajiun..ni najma naga takaina wannan wane la'annen ne wanda yakeson bata da daddiyar shukar dabinon data ginu da gaskiya da amana,akaimata ban ruwa da tsarkakken ruwan alkawari,wayyo Allah, who's after me!?" Tafada wasu zafafen hawaye na zuba bisa kumatunta...

Jin ana knocking din kofar dakin ne yasa ta saurin sa gefen hijabinta ta goge hawayen da suka zubo mata.. sannan tabada damar shigowa.....wata yar matashiyar macece wadda bazata wuce 37to38 ba  tashigo hannunta dauke da plate arufe da jug ... durkusawa tai daidai saitin da najma take ta ajjiye sannan tai mata sallama tafita..

Badon tanasoba,ko tana tinanin zataji dadin abunciba ne yasata ci ,saidon kawai babyn dake jikinta wanda tasan inbataci ba ta cutar da shi..duk kuwa da kasancewar taci jollop ,amma ai wannan guje gujen da wannan mara tausayin yasata yi ma,ya isa yasa abincin yayi kasa......
Dan dole tarinka turawa ,kamar zatayi amai tanaci tanajin wasu zafafen hawaye na zubo mata....batafi 10mnts dafara cin abincin ba ,ta ajjiye,ta zuba tea din tasha ta dauke ta dora kan dan karamin table din dake dakin,....wajen da mirror din dakin yake ta nufa tanazuwa ta dauki wayar da haleema tafada mata tana wajen...domin ta manta tata agida.. dialing din number uncle naseer tafara ti ,tanaji tanata ringing amma ba a daga ba wajen sau uku  dole ta ajjiye wayar takoma kan bed din ta zauna ....batafi minti biyu dazama ba text ya shigo wayar ..dauka tai taduba ...'please ki kwantar da hankalinki kinji,ki daure kici abincin da aka kawomiki, please not for my sake,for the sake of our unborn child'...murmushi ne ya subuce mata..tai mai reply da ...'kaima ka kwantar da hankalinka kaji hubby,whom am i,dazanki cin abinci bayan nasan hakan zaiyi affecting din mijina da dansa,ka kula da kanka too'........

Tana gama turawa ta haye gado ..ta haye gado ta kwanta. zuciyarta fal da tinanin uncle naseer,,ahaka bacci ya kwasheta fuskarta dauke da murmushi.....✍️

Asubah ta gari najman bobo uncle naseer ......

Gaskiya zandaina tafin, Saboda rashin voting,dan Allah kunayimin voting shine zaike bani kwarin guiwar yin updating da wuri....🍭🍭🍭

Uncle naseer
By
Naseer Bn Umar

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now