uncle naseer

188 28 2
                                    

Part 39&40
💓❤️❤️💋

..... ahankali ya saka hannunsa na dama yafara ,yaye rawanin dake kanshi........lallausan gashin kansa baki kirin me kyalli ne yafara sakkowa zuwa kan kafadarsa....

Ahankali ya cigaba da warware daurin ,yanayi kamar bayaso...
Way! ahy!".. shine abun da matasan yan matan dake cikin filin suka rinka,fada sakamakon yin arba da fuskar yarima Abdul Naseer....duk da kasancewar ba yau suka fara ganinsa ba,amma a kulllin idan zasu ganshi ganinsa suke kamar wani sabon wata....kwantaccen sajensa da yaywa fuskarsa kawanya ,ma kadai ya isa zautar da ma abocin kallonsa,kwayar idanunsa sunkasance kalar golden amaimakon baki na sauran mutane......

Yarima Abdul Naseer  yakasance da na 2 awajen mahaifinsa sarki Muhammad sultan......acikin yayan sultan guda 6 da Allah yabasa, yakasance shidin na dabanne,don tindaga  tashinsa da kuma abubuwan al ajabin da suka rinka shigowa rayuwarsa,da kuma  su suka taru suka haddasa mai kiyayya acikin yan uwansa,... kiyayyar da yan uwansa suke mai ba irin kiyayya bace dazaka gane farat daya,kiyayyace irin wadda ake kira da Saran boye!...don a yanayin da suke gudanar da rayuwarsu afili cike da tsantasar soyayya da ...da kulawa.. ya isa yasa ka yi musu kallon tsintsiya madaurin ki daya,sedai kash abun ba haka yake ba don wannan tsintsiyar afili take a dunkule amma daga ciki wani,kamar tsintsiyar kwakwace ,ce ahannun ka kake shara da ita yau da gobe batare dakasan tsakiyar ta manyan kwari  sunyi mata rami ba,sedai kawai rana guda kaga ta fara zagwanyewa, yayinda zakaga kowane sashi najikin tsintsiyar ainahin suffarsa ta fito,zakaga wani yafara karewa yazama guntu,wani wani kuma  be kare ba amma kana tabashi ze karye...toh kamar haka hassada da kiyayyar wadannan yan uwan take... Allah ya kyauta....

Tindaga sanda kiyayyar , wadannan yan uwa akanshi takaru shine, watarana sarki sultan ya ziyarci dakin da duk wani sarki a a wannan masarautar yazame masa kamar dole ya ziyarta aduk sanda wani abu ya shige masa duhu. Sarki sultan mutunne wanda a wannan lokacin yay imani da abun da  tsubbu ,wanda hakan yasamo asaline  tin daga kan kakkanninsa......ba komai ne acikin dakin ba face wani aljani kwaya daya dan mitsisi kamar ka kifeshi da kwarya.. tsoho tukuf ne aljani n don har gemunsa na taba kasa... ...bayan ziyarar da sultan ya kaiwa....wannan aljani akan ya bincika mai ko Abdul Naseer ne wanda ze gajeshi,don shi yafison ya Abdul Naseer ya gajeshi. Don tindaga lokacin da wannan aljani ya sanar dashi  shirye shiryen da yan uwan Abdul Naseer din suke yi akanshi ganin sun kawar dashi...tindaga wannan lokacin yaji yamafi son ya gajeshi ...duba da irin kyakykyawar zuciyar da yaga yanada da ita na rashin son cutar da yan uwansa.....koda sultan ya sami tabbaci daga gun wannan aljani wannan aljani....memakon yabar abun a ransa kawai seya kira amintaccen wazeerina da kuma baffansa galadima ya gayamu su...hadi da rokonsu karsu fadawa kowa,,ba a dade ba sega magana ta fasu  ,harta dawo kunnen sultan din,batare da bata lokaci ba sultan yay kiransu yay  ya nuna musu fushinsa sosai akan abun da daya daga cikin su ya aikata na fitar mai da sirrinsa....nan dukkansu suka rantse akan basu suga gaya ba.....haka dai sultan ya sallame su ,zuciyarsa fal da tinanin ta inda zance ya fita,hartakai ga yakoma kunnen yayansa...saboda shi tsoron da yake kar suyi wani yunkuri..na cutar da shi Abdul Naseer din.....

Ta sanadiyar hakan yasa sultan ya dauke Abdul Naseer ya maidashi birtaniya da zama..inda ya cigaba da karatunsa acan.....

.........

Bayan kowa ya nutsu ne , aka gabatarwa da sultan ,yayansa maza uku da sukayi gasar inda Abdul Naseer ya kasance a gaba , kasancewar shi yaci gasar atake alqalin gasa ya kama hannun Abdul Naseer din ya kai shi gaban me martaba sultan..don kai gaisuwa,inda shikuma Abdul Naseer ya gabatarwa da sultan dankwakwalin mufeeda.....daya zamemai shaidar shi ya cinye wannan gasa.......anan sultan yadafa kansa yasa mai albarka hadi da sunbatar tsakiyar kansa...

Bayan Abdul Naseer ,ya mike,suma su muhsin da umar suka je suka kwashi gaisuwa awajen mahaifinsu sultan,yayinda suma yadafa kawunansu hadi da samusu albarka,amma batare da yasunbaci tsakiyar kawunansu ba......

Gabaki daya kuma Abdul Naseer da yan uwansa biyun se suka rungume junansu ... Bayan sun saki junansu ne umar ya kalli Abdul Naseer yana murmushu yace...
"Yakai dan uwana,inason kasani bayan mahaifinmu babu wanda yakaini farin ciki da annashuwar cinyewar ka wanna gasa, don haka inason in rokeka wata alfarma idan bazaka damu ba?"

Yafada kwalla na cikowa a idanunsa...

Saurin kamo hannunsa Abdul Naseer yay yana mecewa.....

"Yakai rabin raina inason kasani nima bayan mahaifinmu babu da mahafiyarmu babu,wanda yakaini sanku a wannan duniyar, inkana kiran zaka rokeni,kanasawa inaji kamar baka  dauke ni a yanda na daukeka ba,don haka kafadi bukatar  ko mecece zan biyama da yardar Allah"..

Murmushi umar yay sannan yace....

"Inason aduk sanda matarka ta haihu ,bayan ta yaye yaron ko yarinyar inason kabar minshi yadawo wajena......"

Murmushi Abdul Naseer yay sannan yace..
"Dama akan haka, kake cewa zaka rokeni toh inhar wannan ne na yarda 100% bisa 100%"

Muhsin ne yay saurin cewa kai  hamma umar daga jin zan roka shine kaima ka roka"

Yafada yana me turo baki ,asfa yay fishi...dariya dukkansu suka kwashe da ita sannan Umar yace.

"Toh ai tare zamu,raineshi ,kafinnan ma muma munyi aure,kajikoh"

Yafada yana me talle me keya...
Dariya suka kara fashewa da ita akaro na biyu...suna masu rungume junansu....

Kowa dake cikin rumfar nan abun nasu saida ya birgesa,,aka rinka samusu albarka da fatan dorewa a haka....shidai sultan yana daga zaune yana dan murmusawa.....

Anan take alqalin gasa ya mike ya gabatarwa da jama'ar zazzau Abdul Naseer a matsayin wanda ya cinye wannan gasa....atake anan wajen kuma aka daura aurensa da mufeed...wadda ta kasance ya ga daya daga cikin aminan sultan.......

Ana gama daura auren ..Abdul Naseer dake tsaye,ya yanke jiki ya fadi..... aguje muhsin da umar sukai kansa ,ihun da umar yasa ne, ya janyo hankalin su sultan da galadima wajen.....✍️

Nagode da addu'o inku Allah yay albarka ameen thumma ameen ❤️
Please adaure arinka voting

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now