uncle naseer

251 31 5
                                    

Part 47&48
💓💓❤️💋

.....rasss! Rass! Gabanta yabada sakamakon arba da fuskar mutumin da batai zatoba....

Saurin juyawa tai, sakamakon haduwa da idanunsu yay.... window n tasa hannu tajawo tarufe a hankali...kana ta nemi gefen gado ta zauna...tana me faman haki,kamar wacce tai tsere....tama rasa ta ina zata bullowa al'amarin da taji... Shekaranjiya aka kawota cikin gidan nan a matsayin matar aure ,amma daga shekaranjiya n zuwa yau taga abubuwa masu daure kai dasa mutum acikin rudani,tama rasa ta inda zata fara bullowa...daga shigiwor  ta gidan nan ko kwana 3 bata rufa ba ace tafara cin karo da irin wadannan makirce makirce...bata ankara ba se jitai hawaye sun wanke mata fuska......'ke duniya ina zaki damu ace yau wanda yafi kowa kusanci dakai in aka dauke iyayen ka,,shike son ganin bayanka *

Tafada tana me share hawayen daya kara zubo mata....

Bathroom tashiga ta wanke fuskar ta,tana fitowa ta tarar da  hajjo  zaune akan kujera . yayinda da jakadiya keta kokarin shirya kaya acikin sif dinta wanda batasan ma na mene ba...

"Zo ki zauna a kusa dani, inbaki maganin kinji indo"

Hajjo tafada tana me jawo kwaryar dake kusa da ita...

Akunyace ta karaso cikin dakin,ta nemi waje gefen kafafun hajjo ta zauna...

Murmushi hajjo tai tana me mika mata kwaryar dake hannunta tana murmushi,kanta akasa tasa hannu ta amsa....

"Ki rintse idanunki ki shanye  kinji,"

Hajjo tafada bayan ta mika mata.. kwaryar...haka mufeeda ta rintse idanuwanta ta shanye dakyar kasancewar akwai dan daci....

Haka ta mikawa hajjo kwaryar...

Zuwa wannan lokacin jakadiya ta gama zuba kayan datake zubawa acikin sif din. ..

"Toh kinga wadannan tarkacen dik naki ne,ke guda. Kaya ne daga hannun mutanen gidanan masu kirkinsu da akasin haka suka tattaro miki a matsayin tukuivi,don kin cancanci a baki,sbd ba kowace mace bace take kai budurcin ta dakin mijinta.., shiyasa aka dauki zanin da kika bata,nace aje anunawa mutanen gidanan a bisa al ada "

Hajjo takarashe fada tana me mikewa tsaye...

Kisaki jikinki dani,ki dauke ni kmar mhaifiyarki..kinji,in kinajin wani abu ki sanar dani kinji"

"Kisamu ki kwanta, saboda maganin yana dan bugar wa..."
Cewar jakadiya

Kisa

"Yaww fada mata,muna fita  kuma ki rife kofa kofa karki bude,don mijinki yana can wajen me sultan."
Hajjo tafada tana me ficewa...
Jakadiya ma ta rufa mata baya.. ..

Jin dan dim da kanta yafara yimata ne da kuma idanunta da suka fara lumshewa yasa ta mikewa ta haye gado.....nan kuma bacci ya kwasheta...

...............misalin karfe 11:am Abdul Naseer ya dawo ,sau daya yay knocking ta taso ta bude, kasancewar maganin ya dan saketa.....nan suka bude babin sabon bacci ita dashi...basune suka farka ba se 12:30  ....

Tindaga wannan lokacin yazamana Abdul Naseer ,yana manne da mufeeda rai da rai...duk sanda aka samu akasi wata rafiya ta kamasa toh mufeeda zaka sameta a Bangaren hajjo..suna ta fira yanda kasan kawaye.. kasancewar hajjo macece me barkwanci yasa har suna tasawa mufeeda yar bafullatana....

Abangaren Abdul Naseer kuwa lokaci zuwa lokaci in asirin da akai mai ya motsa... Haka zeta bubbuga kansa da gini yanaji kmr ze fado kasa don Zaba,haka mufeeda zatai ta kallonsa tana hawayen tausayinsa ..... kokuma yay ta daukar kayan sa yana yayygawa. .harse mufi da taje takira hajjo ...

Awannan dan takinne ciki ya bayyana ajikin mufeeda kuma,murna wajen Abdul Naseer,kuwa ba a magana don har kukan murna seda yay, harda sawa yaronsuna..... hajjo da sultan kuwa suma tasu murnar bata boyuwa...

Abangaren mufeeda kuwa,itadai gatanan gatanan ne,don duk lokacin da ta tina cewar tana da ciki ta kuma tina cewar cikin wannan rikitatten gidan ze fado seta fashe da kuka....

Wani lokacin  kuma zaka sami mufeeda  tana karatun littafan hausa ko na turanc a bangarenta kasancewar ta ma a bociyar son karance karance....

Yau dinma kamar kullum mufeeda ,ce zaune akan daya daga cikin kujerun bedroom dinta ,hannunta rike da wani littai mesuna So Aljannar Duniya! Na Hafsat abdulwaheeb...

Tayi nisa acikin karatun nata...
ne taji kamar giftawar mutum ta labulen da ke.bayanta....juyawa tai azabure...don ganin mene ya gifta...don awannan lokacin Abdul Naseer baya nan,amma dai beyi nisa ba... kasancewar yagaya mata ba lokacin ze dawo ba ,kuma ya gayata lokacin da ze dawo....din..

Wayam bata ga komai ba,hakan yasa,ta maida hankalin ta ga abun da takeyi....

Jinwani sabon motsin,hadi da gurnani dake kusanto ta yasa ta saurin sakin littafin dake hannunta...batare datai aune ba seji tai an shak.....✍️

1,1,2023💓

Rip 2022❤️
I welcomed you through the door of 2023❤️
Dan girman Allah kuyi votting

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now