uncle naseer

244 27 6
                                    

Part 45&46
💓💓💓❤️

.... Daddagewa yay ya kwarara mahaukacin ihu, yana me gwara kansa da bishiya..... cigaba yay da gwara kansa ajikin bishiyar yanayi yana sambatu,yana ihu hadi da buga kafarsa a kasa ,....

Daka mai tsawar da Wannan
tsohon arnen kule kulen yay ne ,yasa sa dakatawa ,batare da ya juyo ba Amma....

Cikin tiririn baki, arnen kule kulen yafara magana bakinsa na fitar da wata kalar kumfa mara kyan gani.....yace

"Inaso kasani,babu  wata data isa ta haifi wani dan kutumar uban da ,zai dakatar dani daga aikin dana fara ba,babu kuma baza ai ba"....

Yakarashe fada yana me komawa,ciki bukkar  duk da wutar dake ci aciki....bayan kamar mintuna uku yafito ...

Kallonsa yay sannan yace mai,zanyi ma wani  shu,umin aiki, aikine daba kowa nakewa ba,kai ma din zanyima ne domin innunawa makiyanka  cewar basu isa su lalata min aikina ba,amma fa inaso kasani inhar nayima wannan aikin toh nai ma narantsuwa,se yanda kaso komai ya gudana acikin zazzau,sedai kuma akwai jinkiri"

Cikin zakuwa yace mai....

"Menene jinkirin,?" ...

"Bakomai ne jinkirin ba,face zaka jira harzuwa sanda matar Abdul Naseer zata haihu,dole ne kasan yanda kayi ka samo jinin haihuwar ta,adai dai wannan lokacin,bayan ka yi nasarar samun jinin haihuwar tata ne, zaka kawo minshi nan wajena,tin afarko dama na umarce ka daka kawo maniyin matar Abdul Naseer din,sedai kash Abdul Naseer ya shammace ka,inda ya tara da matarsa adai dai sanda baka gari,toh yanxu a madadin wannan ,zakai jira na tsawon shekara 35 harzuwa lokacin da dan  da Abdul Naseer ya haifa, sannan ka samo. Maniyin matar dan Abdul Naseer din...."

A matukar zabure ya dubi wannan arnen kule kulen, sakamakon jin abunda ya fada,yace...

"Injira kamarya injira harna tsawon shekara 35, kana nufin kenan harna tsawon shekara talatin da biyar din ni inah zaune batare da cikar burina ba,ayanzu nakeso inga na haye wannan karagar,ni a lissafina nanda shekara 35 aina zama shugaban kasa kuma,donni wannan karagar inason hawanta ne don cikar burina...da son ganin na wulakanta rayuwar Abdul Naseer"

Yakarashe fada yana me goge gumin da ya tsatstsafo mai...

Dariya wannan arnen kule kulen yasa,yarinka kyalyatawa harna tsawon wasu mintuna sannan ya dakata yana me kallon shi yace...

"Kaji dan durun uwa,waya gaya maka tsawon shekara 35 din Abdul Naseer din ne ze cigaba da mulki,toh bari kaji ingaya maka harna tsawon shekara 35 din nan mahaifinku shine ze cigaba da mulki, ta dalilin bacewar da Abdul Naseer zeyi...."

Cikin kullewar kai ya dubeshi yace....

"Bacewa kuma kamarya bacewa,mezai batar dashi?..

"Wannan ne kuma bansaniba,kawai dai inason kasani bayan kai akwai wani kamar ka yanda kaganka din nan a bakar zuciya da komai kamarku daya,don shi yama fika hatsabibanci ....shi kungiya guda ce dasu shida abokan huddarsa...

"Wai waye wannan ,kuma daga ina zezo??"

Ya jero mai tambayoyin yana me zabga tagumi...

"Ba kowa bane face dan uwanka ,kuma ba daga ko ina zezo ba,yana cikin gidanku tare dakai",

"Nifa?"

"Eh kai, sannan kuma inason kasani in ta tabbata shekara 35 din nan tazo..baka samu nasarar samo maniyin matar dan abdallah ba toh wlh wlh wlh!  Sekayi mutuwar karen farauta,domin a bola zaka mutu,don koh alfarmar binnewa bazaka samu ba,nafada maka,gwara ma tintini inkasan bazaka iya ba kadakata na gaya maka...."

Yafada yana me yafito sa da hannu alamar ya biyosa......

.............................................................

Acan cikin gidan sarauta kuwa...

Abdul Naseer be saurarawa mufeeda ,harse wajejen kiraye kirayen assalatu ,don seda yay sau uku......komawa gefe yay yana me maida numfashi ,kana kuma yajuya ya kura wa kyakykyawar fuskar mufeeda idanu ,tayi jajir saboda tsabar kuka abunka da farin mutum...jawota jikinsa yay ya rungume itadai bata da katamus don ko motsi bata iyayiba....

Tashi yay,ya shige bandakin dakin,yay wanka...yana fitowa ya shimfida dadduma ya tada sallah.....

Seda ya shigaa kitchen ya dora ruwan zafi... sannan ya dawo ya kwanta a gefenta yana ta famanyin nishi....bayan kamar mintuna 6 ya mike ya koma kitchen din ,ganin yay ne yasashi dakko bucket din da hajjo ta sa jakadiya ta ajjiye a cikin dakin..ya juye ruwan yay bandaki ...

Cancarakat ya dauketa yay ciikin bandakin da ita....

Badadewa ba Abdul Naseer,ya kammala gyarata kana kuma ya ya mike ,yaje ya bude kofa saboda knocking da yaji anyi....

Jakadiya ce tsaye , yana ganin itace yay saurin matsa mata tashige yana me gaida ta sannan yay zamansa a falon....

Kaitsaye jakadiya ta dau haske,dakin da mufeeda ke kwance ta nufa.....

Ganinta da tayi a zaune Akan kujeran dake dakin yasata,gaida ta dauke murmushi,cikin jin kunya mufeeda ta amsa mata tana me kauda idonta gefe don bataso su hada ido da jakadiya....

Kaitsaye gadon jakadiya ta nufa,ta yaye kyallen da Abdul Naseer ya shimfida tafita.....

After like 10 minutes da fitar jakadiya Abdul Naseer ya shigo ,sanye yake da jalllabiya maroon...inda take ya nufa yasa hannu ya dago kanta,suna hada ido tai saurin sunkuyar da kanta. ..agefen kujeran da take ya zauna yana me jawota jikinsa...hadi cusa to hannunsa acikin breziyarta...yaywa nonanta guda damkar dambu

"Bana da lfy" mufeeda tafada cikin muryar maasa lfy...

Cikin tashin hankalin ya sakko kasa,ya durkusa a gabanta hadi da cewa....

"Aish!,meye yake damunki,nine koh ?"

Hannuta tasa ta dauke kwallar da ta zubo mai akan kumatunsa...kana tace...

"A,a, zaxzabi ne kawai nakeji.."

Zagayo ta gefenta yay  yay mata side hug kana yace mata...

"Jirani inje Bangaren ummi indawo kinji koh"...

Kai ta gyada mai kana ya fice daga cikin dakin,

Ganin ta ita kadai acikin dakin ne,yasa ta mike ta nufi window dakin don tashaki iskar dake fitowo  ta cikin lambun sultan , kasancewar ta ma,abociyar son ganin son shuke.....

Cikin kwanciyar hankali take shakar iskar ,abunta tanayi tana lumshe ido..motsin da taji ne hadi da magana kasa kasae,yasata saurin bude idanunta. Dukkuwa da kasancewar da dan taku daga inda ake maganar zuwa inda take, sakamakon kasancewar ta mace me saurin ji da kuma karfin gani yasata juyowa...kasa kunnenta tayi...cikin tsananin tashin hankali tasa hannu tafara goge gumin da yafara tsatstsafo mata.....jin kafafunta bazasu iya daukanta bane yasata juya da zummar barin wajen window din,harta juya sekuma wata zuciyar ta bata umarnin ta kara lekawa taga fuskar mutumin......✍️

Merry Christmas 💓

Masuyin votting ina gani,kuma inatai muka adduar gamawa da duniya lfy,domin kuna matukar bani farinciki in kukai votting din nan...💓💓❤️

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now