uncle naseer

199 32 3
                                    

Part 51&52
💓💓💓💋

.... misalin karfe 2 na dare mufeeda ta fara nakuda,nishi kawai take ta faman yi..hadi da ambaton sunan Allah,yayinda hannunta yake sarkafe da na Abdul Naseer..sannu kawai yake ta faman jera mata...yanason yafita yaje yakira jakadiya koh hajjo amma yana tsoron barin ta ita kadai..
Mufeeda kuwa tana nakudar amma Allah besa ta fice daga cikin hayyacinta ba ,hakanne yabata damar ganin wanda yake kawo mata hari kullum,tsaye yake kyam manne da bango se dariya yake ta faman kyalkyalawa...dahannun ta ke nunawa Abdul Naseer shi amma ina shibaya ganinsa....
Abdul Naseer rike da hannun mufeeda..yaji tsakiyar kansa ya sara mai, ahankali yafara jin ,gurnani  na tinkaro sa...yayinda idanunsa yafara juyawa ,kalar dakin ta fara canzamai dagaduhu zuwa haske..duk da haka be saki hannun mufeeda ba sema kara rike ta da yakeyi gam..ana cikin wannan halin ne mufeeda kankame da Abdul Naseer..na gudar tagasken ta taso mata gadi da wani masifaffen karfi da taji yazo mata....jinta tarinkayi kamar in aka bata dutse zata iya gatsawa... cikin tafara kai wa hari tana dannawa da hannunta biyu, lokaci guda idanunta suka sauya daga nata zuwa na wata jalar halitta.. Inda kaitsaye kuma halittar ta bayyana kanta akan fuskar mufeeda,kiri kiri kiri Abdul Naseer yaga muskar wanda be taba tinaniba..akan fuskar mufeeda yana me kyalkyala mai dariya.mugunta..
Hannunsa guda yasa yana me nuna shi amma ina yakasa dagawa...sema kansa da yaji yana juya mai din da karfi.....

Zumbur hajjo dake gefen sultan tana bacci ,ta mike kamar wanda aka tsikarawa allura shima sultan ya mike..duk wadannan abubuwan dake faruwa abangaren Abdul Naseer da mufeeda sultan seda yagansu a cikin mafarkinsa.
. hajjo kwa ajikinta taji babu lfy..babu abunda jikinta keyi se karkarwa..yayinda shima sultan se maida numfashi yake akai akai..zumbur hajjo ta mike ta dira daga kan gadon sultan ne yay saurin dakatar da ita ta hanyar cewa..."Ina zaki?"

Shuru tayi batare da tacemai komai ba ,ita bata juyo takalleshi ba ita kuma bata cigaba da ta fiya ba....kidawo kinemi waje ki zauna mubarwa gobe mugani"

Sultan yafada yana me tasowa ya nufo inda hajjo take..juyo da ita yay suna me fuskantar juna.....cikin..daddatsewar magana tafara yimai mgn araunane..."ranka yadade..nayi mummunan mafarki ne,gameda da Abdul Naseer da mufeeda...,gabaki daya halin dana gansu aciki yayi muni,ina me rokonka daka bani dama naje koh muje dakai...."

Dukdakasancewar sultan mutum ne me dakewar zuciya amma seda..yaji gabansa ya fadi..saboda shima kwatankwacin mfrkin da yayi kenan.. domin ya kwantar mata da hankali kar ta kuma rudewa se yace yana meyin murmushi"inbanda abinki fulani dama akan mafarki ne kika tada hankalinki haka...da ilimin ki kibari mafarki yana rudaki,bayan kinsan shedanin yana da tasari sosai acikin mafarkanmu yanzu..?"

Shiru tai batare da tace komai ba.. yayinda yacigaba da cewa"inhar hkn toh ki kwantar da hankalinki babu wani abu da zai faru da Abdul Naseer da mufeeda seda amincewa da kuma yardar allah walau sharri koh alkhairi...mugun mafarki kuma ba komai bane face aikin shedan...".
Yakarashe fada yana me jan hannunta suka koma kan gado yayinda itadai hankalin ta be kwanta ba.....

Ana cikin wannan halin ne,maryam matar Umar (daddy) ta wannnan lokacin nakuda itama ta taso mata gadan gadan... lokacin daddy bayanan yayi tafiya kmr yadda yashaida mata tun adaren jiya,daga ita se hadimarta atare da ita saboda da dama ta yini tana yin ciwon atatstsaye......

Bayan bakar wahala datasha.ta haifo danta namiji...nan da nan hadimarta ta taimaka mata ta gyara jikinta tagyara dan tai mai,duk abun da ake bukata ayiwa jinjiri sabon wanka.. sannan ta fita....

Bayan fitar hadimar maryam ne kuma, maryam ta mike da nufi tazaka bandaki...yayinda ta bar jinjirinta akan gadon yana cilla kukansu na jarirai..

Nandai hadimarta ta temaka marta ta gyra
Abangaren Abdul Naseer kuwa...shida mufeeda yanaji yana ganin halin da take ciki amma babu halin ya temaka mata,ahaka cikin ikon Allah mufeeda ta haifo Yayanta guda biyu duk maza twins..cikin karfin hali tasa hannu ta dauke su tashafa kansu ,duk subiyun..hawaye na zubo mata..ta ajjiyesu tana me jero kalmar" lah ilah ha illallahu muhammadan rasulullahu,sallallahu alaihi wasssalama!...."
Tana gama fada tai saurin tura dayan jinjirin cikin karkashin gado..

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now