4

5.4K 371 4
                                    

CIKI DA GASKIYA.......!!
        {🔪wuk'a bata hudashi🗡}

         Bilyn Abdul ce🤙🏻

0⃣4⃣

     Kamar yanda Bishirah tafad'a kuwa hakance ta kasance, k'arfe 4am iya tazo ta tada bishirah, amma banda Aysha daketa barcinta.
       Aysha bata farkaba saida wasu masallatan suka fara kabbara sallahma, ahanzarce ta tashi tana ambatar addu'ar tashi daga barci, kallonta takai gefenta inda bishirah take kwance, amma saitaga wayam, tunowa da firarsu ta daren jiya tayi, tagirgiza kai cikin takaicin rashin 'yanci da talaka ke fuskanta ak'asarnan, barcinma bazakayi isashsheba, saida tsayayyen lokacin tashi domin hidimtawa wasu, ganin tunani zaisata makara sallah yasata mik'ewa, bata 6ata lokaciba tafad'a toilet d'in dake d'akin ta d'auro alwala.
    Bayan tagabar da sallarta tayi azkar a gaggauce tatashi.
      6angaren tsit yake, alamun duk suntafi bautar data zaunar dasu agidan, ran Aysha babu dad'i tafice itama, cikeda fargaba tanufi 6angaren mutanen gidan, k'ofar arufe take, kuma bazata iya bud'ewaba, harta juya zata koma inda tafito saiga matasan gidan suduka, sunsako k'yak'yk'yawan dattijo a tsakkiya, kafin tabar gurin harsun k'araso gareta, dole tazube guywoyinta ak'asa tana kwasar gaisuwa, duk suka amsa mata, dattijo Alhaji Abdallah yakafama Aysha ido, haka kawai yaji gabansa yafad'i, girarsa ta dama ta harba, (in bilynku nace komiyasa?) yad'an lumshe idanunsa tareda maidasu kan yaransa yana tambayarsu da ido wacece?.
        Mujaheed yace Baffah d'iyar Maman yarace.
      d'an murmushinsu Na manya yayi batareda yace komaiba yacigaba da tafiya, matasan yaransa suka take masa baya.
    Muslim ne yadawo baya yacema Aysha mikike nemane?.
    Har yanzu tana a durk'ushe kanta ak'asa tace zanje wajensu Gwaggona natayasu aiki, shiru yayi yana nazarin waye gwaggonta?, saican yace, "kina nufin Maman yara?.
    Kanta tagyad'a masa batareda tayi maganaba, yace, " OK tashi Na nunu miki.
     K'ofar baya ta kichin Muslim ya nunama Aysha yace kishiga suna aciki. Baijira cewartaba yajuya abinsa.
   Bayansa tabi dakallo harya 6ace mata sannan tashiga Inda ya nuna mata.
    Aikam duk suna ciki, Rabi ce kawai babu, tanacan tana gyaran babban falon gidan, Aysha tagaida kowa, sai sannan talura da hajiyar jiya dasuka tadda akichind'in lokacin dasukazo, matsawa tayi tadurk'usa har k'asa ta gaisheta.
   Yanzuma cikeda fara'a hajiya ta amsa mata, tad'ora dafad'in Aysha nazata kinacan kina barcin gajiya?.
    d'an murmushi Aysha tayi tace, "a'a mama natashi nayi sallah. OK tojeki kwanta abinki kinji.
   A'a mama banajin barci, zan tayaku aikin.
   Kai Aysha bazaki iya da wannan aikinba yamiki girma.
   Lah mama inayi aii, kullum mune mukeyi agidanmu nidasu yaya fadeelah, kubani komiye zan iya insha ALLAH.
      Aysha tayi matuk'ar birge hajiya bilkeesu, harcikin ranta taji k'aunar yarinyar...

___________________________
        Gaba d'aya yaran gidan sun hallara ak'aton dinning table d'in suna breakfast, wasu sanye da Uniform, wasukuma sunsha kwalliyarsu ta mayan guys, bakajin komai sai k'arar filets da cokula, sai surutun wasunsu k'asa-k'asa, Aysha da Bishirah suna daga kichin suna wanke-waken kwanikan da'aka 6ata.
     Kwas-kwas Hameedah tafito daga 6angarensu, ko Inda sauran 'yan uwanta suke bata kallaba, haka suma babu Wanda yadamu da'ita, Dan kowa yasan k'arancin tarbiyyar 'ya'yan hajiya babba agidan.
    Mintina4 tsakani dafitarta saigata tadawo tana k'unk'uni, dinning table d'in tanufa, babuko tausa harshe tace, "ya Ramadan kazo kacire motarka zan fita, dankayi blocking d'ina.
    Yawancinsu duksaida suka kalleta.
    Cikin 6acin rai Ramadan yace, " ank'id'in fitsararriya, kebaki iya gaida kowaba? Nangurin dukba yayyanki baneba, yaymaganar yana nuna sauran 'yan uwansa.
    Baki Hameedah tamurgud'a tana k'unk'uni.
     ran Ramadan yakuma 6aci, yace Dan Uwarki mikike fad'a?.
      Baki takuma murgud'awa.
   Yatashi afusace zai fallamata mari.......

Karka kuskura kata6amin yarinya....
      Maganar hajiya babba tariski kunnuwansu, kowa yamaida Kallonsa gareta. Tacigaba dafad'in Dan Uwarka Bilkeesu ita tahaifamin 'yarne? dazaka ware kwanji kadakarmin ita?, wlhy koda wasa karwani shege yak'ara wannan kuskuren, inba hakaba rayuka zasu 6aci, kajimin shegen yaro.
       Ramadan ya kalleta, amma momy kinaganinfa abinda takema mutane? Mu sa'annintane? Tazo tawuce bata gaida kowaba, kosu ya Mujaheed fa bata gayarba......
      Tobazata gayar d'inba, kokuwa dolene saita gaishesu? Sud'in ubantane? Bare ace yawajaba agareta saita gaidasu?.....
     Har Ramadan yabud'e baki zaiyi magana......hajiya Bilkeesu takatseshi da daka MASA tsawa.
     Ramadan!!! Karna sakejin maganarka anan, kaje kacire motarka tafita.
       Idonsa jajur yace, "amma Aunty......
     Dakatamin, nace karka sake magana ko, wuce kajanye motarka.
      Saida ya watsama Hameedah harara sannan Yakoma wajen zamansa yafigi key d'in motarsa a dinning yafita.
      Hajiya babba da Hameeda suka take masa baya, hajia babba nak'ara zazzaga masifa da zagin Aunty.
      Girgiza kai kawai Aunty tayi, tak'arasa dinning d'in Tanama sauran fad'a. cikin ladabi Sultan yace, " kiyi hak'uri Aunty, wlhy laifin yarinyarne, kinsansudai basuda kunya.. 
       Komadai miye kukama girmanku, banason fitina kunsani.
    Hak'uri sukaita bata suduka.

Hayaniyarmi nakejine?.....
     Ammah dake fitowa 6angarenta tafad'a. dattijuwar kwarai kenan mai lafiya da tsawon kwana.
     Aunty tarissina tagaisheta, cikeda kulawa ta amsa, tad'ora dafad'in Bilkeesu mike faruwa?.
         Murmushi Aunty tayi, babu komai Ammah.
     Wane babu komai, bayan naji muryar fitinanniyarnan tana shegantamin jikoki, wlhyfa aka k'ureni zand'au mataki agidannan, amma nasan maganin 'yar banza.
    Hak'uri Aunty tabata, hakama yaran, sannan suka gaidata cikin ladabi, itakuma ta amsa tanamai farinciki da d'unbin k'aunar jikokin nata, masu matuk'ar sonta da tattalinta.
      Su Aysha dake la6e suna kallon komai suka saki murmushi, Dan tsohuwar taburge Aysha.
     Ramadan Na shigowa falon Baffah yafito cikin shigarsa ta kamala, wato farar shadda mai d'inkin 'yar ciki da malun-malun, tasha aiki sai maik'o takeyi.
   Duk abinda ke faruwa yana jiyosu daga 6angarensa, wanka yakeyi shiyyasa bai fitoba.
     Kallon Ramadan yayi, yace INA Hameedan?.
      Baffah tafita, cewar Ramadan a ladabce.
    Jinjina kai yayi, amma baice komaiba, yak'arasa Inda Ammah take yagaidata, yaransa mata suka gaisheshi, ya gaisa da mazan tun bayan dawowarsu masallaci.
    Yakai dubansa ga Aunty, da ido yaymata magana, tareda ban hak'uri.
      Tayi murmushi da nuna jin kunyarta gareshi.
   Dayawan yaran sunga soyayyar iyayen nasu, wannan yasakasu murmushi, sunajin sanyi dak'ara k'aunar babansu harma da mamansu dukda ba dukansu Aunty tahaifaba.
     Baffah yak'araso yazauna a dining d'in shima aunty tahad'a MASA break d'in. (Haka yakeyi, inhar yana gidan cikin iyalinsa yakecin abinci, wannan ak'idarsace).

  
Aysha sai juya lamarin gidan takeyi azuciyarta, itadai agidansu tatashi taga mahaifiyarta da kishiya, amma Bahaka taga anayiba, kuma suma yaran Kansu a had'e yake, babukuma Wanda ya Isa ya raina wani acikinsu, akwai Respect d'in nagaba tsakaninsu, idankace kuma zaka kuskure kaci uwaka, Dan Umma da mama kowanne tanada ikon hukunta d'an kowa, shiyyasa bakowa yake banbance yaran gidanbama.
     Itakam tanason k'arin bayani gameda wannan family.
    Haka taita tunani harsuka kammala aikinsu.
    Basu samu gidan yayi hankaliba saida kowa yafice, yaran wasu suntafi aiki, wasu schools, hakama hajiya babba da hajiya saudah duksun fita.
   Daga hajiya Bilkeesu sai Ammah, saikuma su 'yan aiki mazansu da matansu.
   Shima mai gidan yafice tuni.............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now