65

4.5K 300 0
                                    

65

        Dariya yakeyi sosai harda kwanciya, saida yayi mai isarsa sannan yad'ago yana kallon yanda take kuka tana cigaba da gasa bakinta.
           "Hhhhh wato nima za aima d'iyata?, kuttt aini 'yatama bazata biyo halinkiba yarinya, ita bazatama mijinta rashin kunyaba".
         " aikoda batayiba sai mijin yamata, Dan abinda babanta yamin ALLAH zai sakamin akanta".
       Wlhy yakula yarinyarnan kokad'an batada hankali, k'uruci dangin hauka kenan, kar6ar handky d'in yayi daga hannunta yana fad'in "to yanzu yaza'ayi nagoge laifina dankar nima ama d'iyata".
         Hararsa Aysha tayi, tace, " saika bani hak'uri alku'an, sannan kadainamin mugunta, kakuma fad'amin inda ka kwana jiya, saikuma waccan gwaggon tad'azun datajamin wahala wacece ita?".
        "Lallaima yarinya, wato jaridancinki akaina zai fara aiki kenan?, irin wad'annan tambayoyi haka? Wanne kikeso Na amsa aciki to?".
       Kuma turo bakin tayi, " tab duka mana, inkaki amsawa duka babu makawa sai anma 'Yar baba".
        "Tofa, wace 'Yar baba".
     "'Yarka mana, tunda bansan sunan dazaka saka mataba, saikawai nace 'Yar baba kafin lokacin".
      " uhhm hakane kumafa, to amma wazai haifamin 'yarne?".
       "Yo oho maka🙈".
        " a'a, miye najin kunyar to? Kefa kika fara maganar da kanki".
      "Nidai Dan ALLAH mubar wannan zance, kabani amsata".
         "Zanbaki amsarki aii, amma shima zancennan dolene muyishi, Dan nimafa baby's nakeso dawuri, amma ninaga kamar jiya bakiyi sallar magriba ba? Saikuma yau naganki normal, miya faru?".
        Fuskarta arufe har yanzu tace, " jiya d'innefa naji marata tafara ciwo, kuma duk lokacin dazayi Period inayi dama, nazata yazone shine nad'an dakata saboda yanamin wasa damacan, tom bayan fitarka kuma Dana duba sainaga normal nake, shine nacigaba da sallah na".
           "Amma yakama kije wajen doctor, Dan idan period yanama mace wasa wani lokacin infection ne, kokuma wata matsalar".
     Cikin zare ido Aysha tace, " a INA kasani?🤥.
       "Guntuwar dariya yayi, yace, ''INA ruwanki".
        Shiru Aysha tayi, Dan ita wlhy wani abun Na ya khaleel mamaki yake bata.

       Robar cinyarta ya sauke k'asa, yazame ya kwanta yad'ora kansa bisa cinyarta, dukda kujerar 2seat ce, amma haka yay manège.
         "Kinsan ina naje jiya?".
     " a'a, 'Aysha tafad'a da girgiza kai'.
    "Humm club Na kwana".
      Wata zabura tayi, had'eda ture kansa daga cinyarta, rankwashi yasakar mata akai, " kinutsu mana".
     Yay maganar yana hararta tareda maida kansa.
    Itakuma tadafe kai saboda zafi, mugu kawai, tafad'a zuciyarta. Amma afili batace komaiba.
     "Aikinefa yakaini, saboda abubuwan dasuka faruwa awajen yasakani warin giyarnan, amma mijinki baita6a jin koda d'and'anon giyaba aharshensa, ke ko Na sigari ma".
           _"A'eesha! Mutanene kawai basu fahimtaba, amma babu Abu mai saurin rusa rayuwa da ruguzata irin shaye-shaye, shaye-shaye na tarwatsa rayuwar mutum, zakiga inhar mutum yana shaye-shaye komai Na rayuwarsa ya durk'ushe, barakiji, shaye-shaye 6arna d'ayace dake jagorancin dukkan wata asara. Inhar mutum yana shaye-shaye zai iya aikata *zina* da uwarsa, k'anwarsa, yayarsa, surukarsa, k'anwar matarsa, yayarta. Zai iya fyad'e wa 'Yar wani, yarinya ko babba, domin baya tareda tunaninsa. Shaye-shaye yana saka mutum *sata*, zakiga inbasu samu kud'in dazasu shaba sunama iyayensu satar kud'i, kokuma sud'auki nawani, Dan burinsu bai wuce susami abinda zasu shaba yasakasu a wannan mayen. *Addinin* masu shaye-shaye yanada rauni, Dan wani lokacin za'ayi sallah suna cikin maye, basuda nutsuwar dazasuyi karatun Alkur'ani, basuda hankalin yin azkar Dan kariyar jikinsu, basuda lokacin yin azumin nafila Dan Neman lada, basuda nutsuwar tuna ubangijinma gaba d'aya, sai inbasa cikin maye, zakiga wasunsu akwai k'ok'arin sallah, amma inda ake samun matsalar wani lokacinma acikin mayen suke ibadar. mai shaye-shaye zai iya yin *shirka* yana cikin maye, awannan surutan nasu Na banza yayinda suke abuge zasu iya fad'ar duk abinda yazo bakinsu. Mai shaye-shaye, baisan darajar kowaba aduniya, harta da *iyayensa* dasukayi sanadin zuwansa duniya, Dan zai iya cin zarafinsu komai girman tsufansu kuwa, bazai ta6a tausaya musuba, Dan bashida cikakken tunanin tausayinsu, saidai idan sun ajiye yasace, gashi kullum yana cikin saka zukatansu bak'inciki da 6acin rai, alhalin fushin iyaye akan 'ya'ya bala'ine, amma shi baimasan yana kuskurenba ballantana yanemi gafararsu. Mai shaye-shaye zaki sameshi baisan ciwon kansaba, Dan bazai iya Neman nakansaba ballantana al'umma suyi tunanin amfana dashi watarana. Mai shaye-shaye koyayi ilimi saikinga ilimin yazama Na banza domin babu mai amfanuwa da iliminsa takowanne fanni. Mai shaye-shaye zakiga duk Inda yashiga ana tsangwamarsa, ba'ason zama dashima, babu maison abota fashi sai irinsa, babu mai wata k'yak'yk'yawar alak'a dashi koda acikin gidansune, babu mai damuwa dasakashi cikin al'amarin familie saboda bashida nutsuwar da za'a a samu k'aruwa dashi koda a shawarane. Mai shaye-shaye zakiga ko iyalinsa k'yamarsa sukeji, kokuma mijinta baya sonta, ke idanma macece da mijinta yasani zai iya sakinta nan take, idan budurwace tarasa mijin aure, namijinma akan raba aure, idan kuma saurayine babu mai bashi 'yarsa, saidai k'addara, zakiga 'ya'yan irin wad'annan suna girma cikin bak'inciki da tsanar iyayensu azukatansu, Dan basu barmusu wani tarihin dazasuyi alfahari dashiba harsu bigi k'irji wajen kwarmanta ahalinsu acikin k'awaye ko abokai. Mai shaye-shaye zakiga k'arshensa mutuwace abola, bayan mutuwar tasa kuma babu Wanda zai damu da tattauna wani abun alkairi NASA da mala'iku zasuyi guzurin tafiya dashi yayinda ruhinsa ya Isa wajen ubangiji, babu mai bak'incikin mutuwarsa Dan bai amfanama al'umma komaiba, baima amfani rayuwarsaba ballantana tawaninsa. Mai shaye-shaye kulum lafiyarsa raunine da ita, gashi cikin k'angin rayuwa Na k'ila wak'ala, Dan ciwuwukane zasuma dukkan illahirin jikinsa dafifi takowacce ga6a, ciwon huhu. Hanta, kansa, olsa, dadai sauransu. ga d'umbin zunubi wajen ubangiji, Dan wlhy bazai k'yalekaba, tunda bai halliceka dankazo kayi shaye-shaye ba, ya haliccekane danka bauta masa, yamaka dukkan Ni'ima amma kagaza gode masa, duk duniya babu Addinin dayake goyon bayan shaye-shaye, saidai son zuciya yasakamu aikatawa"._
       ''To kinga Dan ALLAH miye ribar shaye-shaye gamai hankali?".
               Gashi idan suka fara dawuya kiga sun bari, sai k'alilan wad'anda ALLAH ya tsame, zakiga mai shaye-shaye yanata cewa gobe, jibi, gata, duk zai bari, amma saiya kasa iya Barin saboda kururuwar shaid'an dake jagorancin rayuwarsa.
    Kinga maganin ayi aikarma afara kenan, ALLAH dai ka shirirya mana zuri'a, ka tsaremu daga rikicin duniya da k'yale-kyalen cikinta.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now