46

4.2K 345 1
                                    

46

      Aysha ta k'ank'ame jikinta tareda takurewa amurfin mortar, sai rawar sanyi takeyi, saboda bak'aramin ruwane yadakesuba awajen.
      Ya khaleel ya gallamata harara yana d'auke lap-top d'insa dake tsakiyarsu, takuma k'ank'ame jikinta, harda rumtse ido, dan azatonda dukanta zaiyi.
         Tsaki yasaki mai k'arfi, dububeki, dawani kanki kamar curin dankalin Hausa, afuska kamar kinada wayo amma wawuyace ashe, atunaninki ko ina ake nuna jarumta? Amatsayinki Na  mace bak'ya tunanin had'ari fiyema da wannan? To dabamu zoba mikike tunani zai faru?!!!!, yay maganar a tsawace.
          Aysha takuma k'ank'ame jikinta tana hawaye, wlhy ya khalee......
        Ki rufemin wannan d'an banzan bakin naki kafin nazubar da hakwaran cikinsa amotarnan, aii sai kin fad'amin ubanda yasakayi biyo hanyarnan ak'afa Stupid girl kawai.
      Acikin ranta tace idan kazubar da hakwaran kaika huta aii, nibanga dalilin wannan bala'iba haka, bakaji tausayinaba ka isheni da jarabarka.
      Adai-dai nan suka iso k'ofar gate d'in gidan, Emanuel yay horn d'an gwari yabud'e.
     Motar bata gama tsayawa da k'yauba Aysha tafita da gudu tayi cikin gida.
    Kwafa ya khaleel yay shima yafito bayan Adams ya bud'e masa k'ofar.
         Drivers d'in gidan yashiga kwalama kira, sunata hada-hadar tafiya masallaci saboda magrib data kawo jiki.
         Ahanzarce suka k'araso gareshi, Dan sunsan shid'in zumane, ga zak'i ga harbi, gashi yanayinsa ya nuna a harzuk'e yake.
        Gaidashi suka shigayi, batareda ya amsasuba yace wanene yake kai yarinyarcan Aee'sha wajen aiki?.
        Jikin lawwali Na rawa yace nine wlhy yalla6ai.
       Wani kallo ya watsa masa, idan an idar da sallar isha'i ina nemanka.
     Maganar daya fad'a kenan yajuya zuwa cikin gida.
          Adams ya kalli su lawwali daduk hankalinsa yake atashe, wainikam wacece yarinyarnan awajen boss? Duk nasan k'annensa, amma ban santaba.
         Itace zai aura, cewar sadisu murya a sanyaye.
    Ido sosai Adams yazaro, aransa yace kutttt shiyyasa Oga yarikice, ashe antynmuce? Lallai kingama morewa y'an mata wlhy.
           Kayansa ya kwaso yamik'ama sadisu danya shiga dasu ciki.

Afalo ta Tatar damafi yawan mutanene gidan, jikin Anty Mamie data fito daga kitchen tafad'a tana kuka, a'a Aysha lfy kuwa? Ina kikaje hankalinmu dukya tashi, lawwali yace yaje d'aukarki baigankiba?.....
       Anty Mamie nafa kirashi wayarsa akashe, shinefa......
     Shigowar ya khaleel takatse mata maganartata.
   Yaran gidan sai sannu da zuwa suke masa Dan tsawon wata 1 baya k'asar.
        Adak'ile ya amsa musu, saboda ransa a6ace yake.
    Anty Mamie tace a'a babana ko tare kukene?.
      Kansa ya jinjinama Anty Mamie.
    To lfy duk naganku ajik'e haka? Mike faruwane? Mu kun sakamu aduhu aii, ita tashigo tana kuka, kaikuma rai a 6ace?.
         Muryarsa cikeda d'aci yayma Anty Mamie bayanin komai, kowa afalon ya tausayama Aysha, amma yanda ran ya khaleel d'in ya6aci sai abin yabasu mamaki.
     Aysha tace ALLAH Anty Mamie tausayi tabani shiyyasa Na taimaketa, kumafa badan niba dazasu keta mutuncin tan........
      Idan bakima mutane shiruba ALLAH saina zaneki yanzunnan, ke mara hankalin inace? Miyasa bazakiyi kamar yanda tayiba? Zaki wuce ki canja kaya kosaina k'ara kummura wannan janaren fuskar takine?, yay maganar yana matsowa kamar zai mazgeta, Ta k'ank'ame Anty Mamie kuwa.
      Baffah dake tsaye yafito dashirin zuwa masallaci tareda y'an uku da Nuriddin yayi murmushi, Dan yaji dad'in yanda khaleel d'in yanuna kishinsa.
       Maganarsace tasaka kowa juyowa gareshi, yace to ya Isa haka, mu'azzam amata hak'uri tayi kuskure, kuje kucire kayan jikinku kar mura takamaku.
           Aii baffah fiyema damura saita kamamu, duk ruwannan nayau akanmu yak'are saboda sakarar yarinyarnan, yay kwafa tareda shigewa 6angarensu.
     Girgiza kai baffah yayi yana murmushi. Yaja hannun k'ananun y'ay'ansa suka nufi massalaci.
     Suma sauran kowa d'akinsa yanufa, Anty Mamie kuma tatafi da Aysha d'akinta itama.
         Duk abinnan dake faruwa mama nad'aki kuma tanajiyo komai, ita sotayima khaleel d'in yazane ayshar wlhy.
   
Anty Mamie tahad'ama Aysha ruwa mai zafi sosai, kije kiyi wanka Aysha, kid'an shiga ruwan kona minti gomane.
      Tana hawaye tajinjinama Anty Mamie kanta.

CIKI DA GASKIYA......!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora