81

5.1K 325 0
                                    

81

Alhmdllh jikinsu yayi sauk'i sosai, maganar 'yan dubiya kam ba'a cewa komai, manyan ogannin ya khaleel Sai zuwa sukeyi dubashi, hakama wad'anda suke k'asansa, abokan baffah ma da matansu, koda yaushe asibitin FAM da mutane, saidafa idon securitys nakan kowa, gudun kar a cutar da ogansu.
    Ammah ma tanata samun lfy, Dan bakinnan yana nan rad'am🤣bai mutuba.

    Nagafa gayyar fans dadama awajen sunzo gaisuwa, su o'e akaita washemin hakwara😁, naganoki to😂, kunjifa su madam son gulma anbaza kunne aji wacece, to nak'i fad'a d'in😏.

     Da safe aka sallami su ya khaleel, amma banda Ammah, aikam tasaka rigima akan bazata zaunaba, aii k'afarta k'afar ironta, itafa baza'a barta a wannan asibitiba babu iro wani yabiyo dare yasakata abuhu.
    Anta lallashinta, aka nuna mata akwai securitys za'a bari suna tsaronta.

      "Yo duk tsaron mutum yakai ALLAH ne?, nidaifa bazan zaunaba, duk wad'annan dakake gani iro yafisu jarumta, ganinsa yasakasu wannan zazzare idanun, dasunga yatafi gida gyangyad'i zasu farama mutane, har aje asaceni basu saniba."😏
         Babu Wanda bai daraba awajennan.
    Ya khaleel yataka ahankali gaban Ammah, hannunta yakama tasakko daga gadon batareda yayi maganaba, shiya taimaka mata takama sandunan dazatayi tafiya.
       Saida tarik'e da k'yau sannan suka fara tafiya ahankali, tana d'an d'ingisawa, suka fice.
    Kowa da kallo yabisu, baffah yay murmishi tareda kallonasu, " to tsayuwar mi mukeyine? Saimu tafi aii, Dan mu'azzam sunyi gaba da Ammah, muskilancin nakusa har yanzu, shiyyasa baza'a mana maganaba".
          Duk d'an darawa sukayi, sannan suka tattara komai suka tafi.
     Amotar Sultan suka iske Ammah da khaleel.
      Kowa saiya shiga mota, Anty zuwairah tabud'e kusada khaleel tazaunar da Aysha, sannan takoma gaba ta zauna kusada Ya Sultan dazaiyi tuk'i.
     Juyowa ya khaleel yayi yakalli Aysha data raku6e jikin murfin motar, talumshe idanunta.
      Tausayintane yakashi, ahankali yasak'alo hannunsa tabayan k'ugunta ya kwantota jikinsa.
     d'ago idanunta tayi ta kallesa, shima idonsa nakanta, ya d'age gira d'aya tareda k'anne idonsa d'aya.
    'Dan murmushi Aysha tayi, tamaida kanta gefen hannunsa ta kwantar.
    Yad'anyi murmushi, tareda sumbatar kanta ahankaki.
     Duk abinda sukeyi Anty zuwairah da ya Sultan Na kallonsu, murmushi kawai sukayi, amma babu Wanda yace komai.
        Ammah dai batasan wainar da'ake toyawaba, hankalinta nakan danna wayarta, Wai tana neman number uncle ma'aruff.😹
        Bawata tafiya mai nisace takaisu gidaba.
    Suna zuwa mama tace Aysha da khaleel suwuce 6angarensu kawai.
   Babu Wanda yace komai, khaleel yakama hannunta suka tafi.
     Tsaf suka tadda ko ina, da'alama kullum sai'an gyara ko ina.
    Aysha tazube saman gadon tana sauke numfashi, Dan har yanzu jikinta babu wani k'arfi.
    Kallo khaleel yabita dashi kawai, baice komaiba yafara k'ok'arin cire kayan jikinsa.
    Aysha nadaga kwance take kallonsa, harya gama, yad'auki towel ya d'aurama k'ugunsa, sosai Aysha taga ramar da ya khaleel yayi akwana ukunnan.
     Ruwan wanka maid'an zafi yahad'a, sannan yafito.
     Idon Aysha alumshe taji and'uketa cak.
    Da sauri taware idonta akansa, yad'age girarsa duka yana kallonta, bazata juri kallonba, sai kawai ta lumshe idanunta.

       Atare sukayi wankan, konace yamusu, Dan duk khaleel ne k'arfin komai, Aysha duk batada wani kuzari ajikinta.
     Dakansa yadawo da'ita cikin d'akin, yad'an Mirza mai, yasaka jallabiyya milk color mai gajeren hannu. Ayshama tad'an dage ta shafa man, amma duk awahalce, burinta kawai ta kwanta.
    Tana gamawa khaleel ya taimaka mata ta sanya doguwar rigar daya  ajiye mata mara nauyi sosai, fara mai adon bak'ak'en furanni, batada hannu, sannan anmata d'inkinne kamar Na yara, rigar tamata k'yau, iyakarta kwaurinta, batakai k'asaba👗.
     Ita kanta saikuma kallon kanta takeyi amadubin, tasan rigar tagama amsar jikinta, kaikace saida aka gwadata aka d'inka, danma tad'an rame, tana mamakin a ina ya khaleel keta zak'ulo kayanan d'ai-d'ai hakane?.
      Bata samu amsarba, saima ajiyar zuciya data sauke, sakamakon jin hannun ya khaleel acikin sumar kanta yana warwareta, dukta cirkud'e saboda rashin samun gyara Na kwana biyu.
    Sai matse baki da rik'e hannunsa Aysha keyi, zafi takeji sosai, amma baice komaiba yad'auki cumb yana taje mata, bayan yasaka mai sosai, dukda haka zafi Aysha keji, sai shiii take fabaki tana rirrik'e hannunsa, amma muguntar khaleel saida yaga gashin ya warware sannan yamaida ribbon d'in ya d'aure mata a tsakkiya.
     Sai tunzura baki Aysha take gaba, wai ita zafi.
    Yatsansa yasaka ya d'alli bakin.
    Da sauri tadafe da hannayenta sabida zafi, tuni idonta sun cika da kwalla kuwa, murmushi yayi, yaduk'o ahankali yasumbaci bakin bayan ya janye hannunta akai.
      Harya cire bakin amma saiya maida.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now