75

4.5K 329 1
                                    

75

Yau dai babu laifi Aysha antashi dad'an k'arfi-k'arfi, saidai tunda farar Safiya tatashi da jarabar son rake, Ammah na zaune afalo tana shan kunun tsamiya, k'a'idane kullum Safiya saita shashi, idan 'yan tsiyarma Na kanta saida k'osai, haka takecewa tagaji dawad'an nan maik'on banzan😂.
       Aysha tafito daga d'akin Ammah, dakaganta dukta rame, sai uban haske data k'ara, har wani yellow-yellow takeyi, kusada Ammah ta zauna tana sauke numfashi.
   Amma tabita da kallo, sannu indo, kai wannan ciki nabaki wahala, gashi ALLAH ya had'aki da birkitaccen miji, ni tsoroma nakeyi karki haifo irinsa".
      Murmushi Aysha tayi.
     Tace, ''kai Ammah, kedai kullum kintaso ya khaleel gaba, kemafa doguwarce, awajenkima yakwaso tsawon, nibama wannanba, ina zan samu rake dan ALLAH Ammah?".
          Ammah ta kur6i kununta tana ta6e baki, kai wannan ciki naki yacika shegen hange-hange, shiyyasa nacemiki ina tsoratar miki haihuwar irin iro, Dan yahalin cikinki ya halin dogon banzarcan".
       Baki Aysha taturo gaba, "duk kigama fad'a saina sanar masa gulmarsa dakikeyi".
       " yo kifad'a mana, angaya miki tsoronsa nakeji, dagake harshi saina had'aku nayi k'uli-k'ulin kubrah daku".
     Dariya sosai Aysha keyi, hakama Musleem daya shigo kusan mintuna hud'u, maganganun Ammah akan kunnensa suka faru.
         Hararsa Ammah tayi, "to kaikuma d'n kwairo wakakema dariya?".
     Had'e fuska musleem yayi, " waike Ammah kowama agidannan saikin saka masa sunan banzane? Nifa shiyyasama Mafison kitafi jigawa".
        "Yo basai ka kainiba d'an banza bakwai, aii dai gidan d'anane, babukuma mai iko dashi sama dani, faratun banza kawai".
     "oho dai, farin aka gani aka rud'e". Yamik'e yana hararta, "nikingama tafiyata, Anty Aysha bara nasa akawo miki raken".
        " yauwa ya musleem, ngd sosai, Ammah kinji dad'inki, kedai dakowama karawa kikeyi, ya Sultan ne kawai bakwa fad'a".
      "Aishi Sultan mutumin arzik'ine, ba irinkuba, amma d'aya bayan d'aya zanyi maganinku, d'an banzancan zigawa zanyi amasa auren dole kwannan, kekuma aure zansa iro yak'ara, kuma 'Yar k'auye zan za6o masa wadda haushi zaiyi kamar ya karsa....
     Tsayawa Aysha tayi da dariyarta, ta had'e fuska tamau, mi Ammah zatayi ba dariyaba, afili tace, " ja'ira, ashedai kinason dogon banzan can mai zuciyar tsiya, amma lokacin auren hardasu kuka".
     Shiru Aysha tama Ammah, daga waje akayi sallama.
    Ammah tace, "kowaye shigo kaji, d'akin tsohuwa aina kowane".
       d'aya daga cikin drivers d'in gidanne, har k'asa ya durk'usa ya gaida Ammah, yamik'o leda viva, gashi inji musleem yace akawo".
     Aysha najin haka takar6e da sauri, yauwa sannunka.
     Rakene mai yawan tsiya aciki, irin wanda aka yanka k'ananunnan aka d'aura afarar Leda, Ammah tayi dariya, ''yoshi wannan duk raken yasiyema mai tallan ko?, saikiyata sha har kigaji".
      "Wlhy kuwa Ammah, dama mafarkinsa nayi a barcin asuba d'innan Dana koma, bara kiga nayo brosh nadawo".
         ''Dama bakiyi burushi ba kikazo kika zauna kinata had'iyar k'azamin yawu?, ke indo kirage k'azantafa".
      " k'yadai jidashi Ammah, aikinsan idan nayi brosh babu abinda zanci amai nakeyi dai", batareda tatsaya jin mi Ammah zataceba tashige bedroom, Mufeedah Na kwance d'ai-d'ai tana shak'ar barcinta, dama ita cikin nata sai saka barci.
      Brosh Aysha tayo tadawo falon, tatarar Ammah tazuba mata raken cikin fleet bayan ta wanko matashi, ankuma ajiye roba na zuba datti.
    "Yauwa Ammarmu, shiyyasa nake yinki sosai-sosai".
        "Kedai kika Sani" cewar Ammah tana shigewa kichin d'inta.
    Aysha tama bayanta gwalo, tafara shan rakenta, harda mik'e k'afafu kamar tasamu gasashshen kifi🤪.
     
           Tayi nisa sosai da shan rakenta, harwani lumshe idanu takeyi Dan dad'insa datakeji, ya khaleel yashigo da sallama, sanye yake cikin k'ananun kaya, blue dogon wando da oxblood d'in sheart, sunmasa k'yau sosai, kwarjini da cikar kamalarsa ta k'awata k'yawun haibarsa, yad'an rame kad'an saboda yawan tunani da cud'ewar aiki dasuka tasoshi gaba.
   Kokad'an Aysha bataji sallamarsaba, idonta alumshe tanata shan rakenta, dariya tabashi, Dan haka yajin gina da bango yana kallonta, sai murmushi yakeyi, ganin abun bana k'are baneba yafiddo wayarsa a aljihu yashiga mata video. Oho Aysha batasan yana yibama, Ammah Ce tafito daga kicin taga abinda ke faruwa. "Iro mikakeyi haka?".
     Harara yazuba mata, "waya sanya dakene jar wuya?, kinzo kin 6atamin show", 'yay maganar yana save d'in video dayayma Aysha'.
    Itama idanu tabud'e da dauri, kokad'an batayi zatonsa yanzunba, danta manta yau Saturday, babu aiki.
           " kai iro ka kiyayeni wlhy, naga kwana biyunnan jaraba kakeji, nimafa Na iyata mota-mota, bar ganinka sangamemen k'ato batsoronka zanjiba ehe😏".
       Yanda tayi maganar da murgud'a baki, saita bama ya khaleel dariya, yasanta da nacin tsiya, idan tafara nacin maganarnan yinin yau babu sauk'i.
    Yace, "hakanefa jar wuya, ni nama manta kece, kinga zauna muyi hirar arzik'i".
     " ato inda arzik'in kazo basai ayiba, nidama nemanka nakeyi".
      "To gani Ammah ta".
      Aysha dai dariya kawai take musu, Dan ita lamarin nasu dariya yabata, Ammah da ya khaleel tamkar tom & jerry haka suke.
    Khaleel kam dukkan hankalinsa nakan Aysha, sauraren Ammah kawai yakeyi, sosai dariyarta take narkar dashi, dama kwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi, yamatso kusada ita yana fad'in " a lallai kinji sauk'i, hardasu dariya?".
     Murmushi Aysha tamasa mai kashe zuciya, tace, ''Alhmdllh, yau natashi babu laifi, harma inajin zan koma aiki ranar Monday".
      Girarsa d'aya yad'e yace, "da gaske?".
     Jinjina masa kai kawai tayi.
     " to ALLAH yak'ara lfy". 'Yay maganar yana kuma shigewa jikinta, Dan Ammah tashiga bedroom yin wanka. Murya can k'asa yake mata magana, "waya siya miki rake da safiyarnan".
        Kuma narke masa tayi ajiki tace, " ya Musleem mana, wai ina kashigene jiya, har nayi barci baka dawoba, bayan wahalar danasha tun wajen 6pm Nake amai, saida doctor yazo yasaka min k'arin ruwama".
      Da sauri ya kalleta, "da gaske kikeyi".
      " ALLAH kuwa".
Tausayinta ne yakuma kamashi, azuciyarsa yace kai uwa dabance, (ALLAH ne kawai zai biya mahaifiya gaskiya), Ahankali ya sumbaci goshinta, "sorry kinji my pretty na, yanzu inane kemiki ciwo?".
       " babu ko ina, yau dad'an sauk'i aii".
        "To Alhmdllh, kinga yau agida zan yini, yakamata mud'anje 6angarenmu muyi hira ko? Naduba babyna mu gaisa dashi".
          Aysha bata gane nufinshiba, tace, " idan Ammah tayi fad'a fa?".
       "Babu wani fad'a dazatayi, tashi mujema kafin tafito".
      Kamardai Aysha bazatajeba amma yamata wayo tabishi, shiya d'auka mata raken fleet d'in dana ledan, tacan baya sukabi dankar agansu, sai 6angarensu.
    Komai fes Aysha ta iskeshi, Dan kullum sai Maleeka da Tasleem sunje sun gyarashi, afalo suka yada zango, suka zube bisa doguwar kujera, ya khaleel ya kwantar da Aysha bisa cinyarsa tana shak'ar daddad'an turarensa, sai lumshe idanu takeyi, Dan wani barcine taji yana fisgarta.
         Idonsa akan fuskarta yana shafa kwantaccen gashinta da hannunsa Na dama, Na haggun kuma yana kan shafaffen cikinta maikama da babu komai aciki, " my pretty badai barciba?".
     Bud'e lumsassun idanunta tayi akansa, saikuma tamaida tad'an lumshe takuma bud'ewa, muryarta harta fara sark'ewa tace, "ALLAH barci kawai naji nafaraji".
      " lallai 'yar gata, rakenfa to?".
     "Nakuma k'oshi".
Guntun murmushi yayi yana kauda kai daga kallonta, itakuma tamaida idonta talumshe.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now