44

3.9K 312 0
                                    

    44

       Bak'aramar fad'uwa gaban gwaggo bintu yayiba, tuni har zufa tafara ketowa a sassan jikinta, tuna gargad'in daya matane yasakata saita kanta da sauri, murya adake tace fad'ima Wanda ya kai Aysha karatu yace karna fad'a.
    Bara namiki dallah-dallah yanda zaki fahimceni, lokacin danazo da Aysha gidannan kowa ya tausaya mata, sannan kuma Aysha tacigaba da tayani y'an ayyukan gida nakeyi, wannan yasakashi kirana gefe yamin tanbayoyi akan Aysha, ban 6oye masa komaiba Na sanar masa, shine yace zai taimaka mata taje makaranta, abinda yasa aka danganta tafiyar tata da taimakon mai ciki danku barine, nasan kai tsaye Yaya bilyamin bazai yarda Aysha tatafi karatu wata k'asaba.
    Amma Dan ALLAH ki fahimceni, shi yace domin ALLAH yayi, shiyyasa bayason kowa yasani.
      Ajiyar zuciya mama ta sauke, danta yarda da zancen Na gwaggo bintu.
   Tace, "to amma miyasa tunda Aysha tatafi karatu bakizo kano ba? Har bikinsu Hafsat amma babuke?.
     Hakane, hakan tafaru sakamakon Lagos danaje kulada zuwairah d'iyar hajia babba, tasamu ciki yana bata matsalane daga Bayama ta haifu d'an babu rai, wlhy fad'ima nasha wahala awajenta itada y'ay'anta, wannan dalilinne yasaka harnayi jiyyarnan a asibiti.
     To bintu rayuwa sai hak'uri aii, gashi yawuce kamar ma ba'ayiba.

Aysha dake jikin k'ofa la6e tasaki ajiyar zuciya tareda fad'in Alhamdllh.
    Da sauri tabar jikin k'ofar danjin alamun mama zata fito...

_____________________
       Hankalin barau modibbo atashe yake sosai, Dan antabatar masa jirgi bazai tashi dashiba, hukumar shigi da fici ta k'asa tayi seizing d'in passport d'insa.
      Baigama fita daga wannan rikitarba yaga alamun rufe asusun bankunansa da akayi gaba d'aya, zuface tafa keto mata addukan sassan jikinsa, cikin sassarfa yake fitowa daga airport d'in tamkar zai kifa k'asa, yaransa biyu nabinsa abaya, sukansu akid'imen suke🤣.

_______________________
             Muna saurarenka j, tund'azun ka kiramu amma kayi shiru ka kasa magana, shin meke damunkane haka? Nifa tunda safe nafuskanci bakada walwala gaskiya.
           Ajiyar zuciya ya khaleel ya sauke, cikin cije le6ensa yace hakane Taheer, inacikin matsala gaskiya.
       Joseph yace matsalarmi j!?, idan akan kama barau modibbo ne aimun d'akko hanya, ko yanzu mukaso kamashi zamu kamashi.
       Ba wannanne matsalarba Joseph.
      To miye? Cewar youseef?.

Aure!.

Aure!! Kuma? Kakeson yi?.
         d'an Harar Taheer d'in yayi, ya gyara zamansa sosai, muryarsa cinkushe da d'aci yabasu labarin komai daya faru, dan ya yarda dasu, bashida abokan dasuka San sirrinsa sama dasu d'in, suma duk kukansu shi suke fad'amawa.

          Gaba d'aya suka kwashe da dariya, sai faman ta6awa sukeyi, tsantsar farinciki ta bayyana a fuskar kowannensu, Youseef yace alhmdllh j!, gaskiya mundad'e bamuyi makamancin farincikin nanba, dama kullum damuwarmu zamuyi aure mu barka, abin Na matuk'ar cin zuciyarmu, lallai Ubangijinmu ya kar6i addu'oinmu, ALLAH nun gode maka.
                   K'aramin tsaki yayi yana Harar youseef d'in, kai Malam bamaganar wasa nakeyibafa, ya ina fad'a muku damuwata zaku maidani wani shakatafi?.
       Nifa banason aurennan, kuma bansan hanyar dazanbi Na yakiceshiba saboda baffah, please kubani shawara mana.
               Amma miyasa baka son auren j!?.
    Saboda bana sonta Joseph.
      Tab, nifa kana bani mamaki wlhy, tokai wa kakeso kuwa arayuwarka? Banta6a ganin kayi budurwaba tunda nake, shin bazakayi aure baneba arayuwarka, kome? Katuna addininkufa yabaku damar auren har mata hud'u, kaiko ko d'ayarma ka kasa kayi, badole baffah yaza6a maka da kansaba.

         Kunga duk wannan cecekucen baima tasoba, j! Kafad'a manane danmubaka shawara?.
          Khaleel ya jinjina kansa.
      To inhar shawararmu kake nema, kama iyayenka biyayya, tunda kagadai bawata kakesoba barema kace saboda soyayyartane, insha ALLAH darajar biyayyar dazakaimusu nangaba saika sota fiyema da tunanin mai hankali.
     Kaga saura 4weeks kawai bikin Joseph, daga nan saina youseef, nima Dady yasanarmin zuwa jibi za'a saka ranar aurena, kai kad'aine dama damuwarmu, to ALLAH ya yaye mana, kawai kayi hak'uri musha biki please, dukda bansan yarinyarba, nasan baffah bazai maka za6in banzaba wlhy, eyeeee angonba, harfa kafara k'yallin goshi Na angwanci.😜😆.
     Taheer yak'are maganar da tsokana.
    Gaba d'aya suka kwashe dadriya, amma banda khaleel Wanda yaja tsaki yana fad'in d'an iska kawai, aikai matsalarka kenan mtsoww!.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now