80

5.2K 325 1
                                    

80

.Alhmdllh su khaleel sun sami taimakon gaggawa a asibitin general hospital, dukda su taheer sunso awuce da khaleel d'in Na station nasu, amma baffah yanuna musu Subari akaisa wannan d'in tunda bashi kad'ai baneba.
Shida Aysha d'aki d'aya aka kwantar dasu, gadonsu kusada juna.
Ammah jar wuya kam itakad'ai🤣.

Kowa kagani a familie d"in yana cikin wani yanayi, kowa da sak'e-sak'en da zuciyarsa kemasa akan abubuwan mamaki dasuka faru yau, Wanda tunani ko hasashen su baffah baita6a kaisu nanba, balle irinsu Sultan dabasu San komaiba.
Ko Anty zuwairah bazata iya dogon labari akan haihuwar khaleel ba, Dan gaba d'aya batafi 6years ba lokacin, to bare kuma Anty Shikurah.🤷🏽‍♀
Anty Mamie kam ita kanta daza'a bata gadon kwanciya zatayi, harma a zurara mata ledojin jini dana ruwa, ko'a mata allurar barci tasami Hutu Na wucin gadi, k'ila tunaninta zai dawo dai-dai, ayanzu kam kallon komai takeyi tamkar mafarki zuwa anjima zata farka taga ba hakaba🙅‍♀.
Bawan ALLAH baffah, shiruma maganace gamai hankali, shikansa dauriyace kawai da juriya, amma kallon komai yakeyi tamkar acikin barci ko shirin film, kokuma labarin hik'ayoyi Na marubuta, zuwa anjima komai zai tsaya yaga dukba hakabane.

Haka sukaita zaman asibitin suna dakon jiran farkawarsu suduka ukun, babu mai damuwa da yunwar cikinsa acikinsu, Dan babu Wanda yake a cikin duniyar mutane balle yatuna akwai ci da sha, kowa ya lula cikin gajimaren tunani, masu kukan zuci nayi, masu hawayen fili nayi, masu rad'ad'i da k'unar zuciya nayi, kowa tambayar zuciyarsa yakeyi miyasa hakan tafarune? Miyasaka Momy aikata haka?, babu Wanda yata6a kawowa aransa hatsabibancin Momy yakai koda quarter d'in hakama, kowa ya d'auka masiface dai tazafin kishi da yanayin halitta kawai, Ashe lamarin Na Momy yagama gawurta.
Babu maibasu amsoshinsu, saidai sukaita juyasu da tattaunawa a zukata, dukkansu fatansu ayanzu bai wuce farkawar su khaleel ba gaba d'aya.
Ganin yanda lokacin yatafi, har 8 Na dare baffah yace suje gida hakanan, subarshi shidasu Mujahedeen, idan suka farka za'a sanar musu.
Gara suje su nemama yara abinci, dansu khaleefa sai kukan yunwa sukeyi, saidai asayi biscuit abasu, yara babu hak'uri, biscuit baya d'aukarsu suka fara k'ananun kuka.
Badan sun soba suka tattara suka tafi, Zunnurain da Musleem suka tafi kaisu gida.
Akabar baffah, Ramadan, sultan, Muhseen, mujahedeen, hafiz anan.

Haka kowa yashiga gidan tamkar anmusu mutuwa, jikin kowa a sanyaye, duk da abinci dasuka Tatar 'yan aikin sunyi hakan baisa wani yadamu da Neman abincinba, yara kawai sukaci su Affan, dakuma yaransu ya Sultan, sai Ummunoor da Nuriddin.
Amma irinsu tasleem ai duk haka kowa yanemi guri yazauna, suka d'ora tunaninsu daga Inda suka tsaya.
Abindama Yakuma basu mamaki shine uban matakan tsaro dasuka Tatar agidan, tako ina anguwar da gidansu zagaye yake da ainahin police dakuma police Interpol, hakama asibiti dasuka baro, ko'ina matakan tsarone, musamman d'akinda khaleel da Aysha ke kwance, babu kuma Wanda ya Isa yashiga d'akin sai doctor Faisal kawai, ko nurse d'aya ba'a amince da itaba, shikansa doctor Faisal d'in akwai sa'idon ma'aikata akansa yake shiga.

_______________________

Su Momy yaukam za'ayi kwanan sel, gashi ba'a had'ata da aminiyar tataba, kowa d'akin da'aka ajiyeshi daban.
Kallon inda zata kwana tayi kawai saita fashe da kuka🤣.
Akan dindinyar sumintine, ga uban zarnin toilet d'in dake d'akin da wari, ga d'an karen sanyi daya fara busawa alokacin, k'afarka kawai kasaka a Simintin sai tsigar jikinka tatashi bare kuma kwanciya, sauk'inma da sauk'in sauro, saboda sanyine sauro baya zama, amma akwai Baban sauro awajen, shine kud'in cizo, irin 6ula-6ula d'innan, wad'anda dasunji kamshin mutum zasu fara gudun fanfakak'e Na k'ok'arin isowa gareshi susha jini, su sanyinma bai koresuba.
Kasa kwanciya hajia babba tayi, ko rayuwar yarinta datayi gidansu 'yan gatane, bare kuma rayuwar gidan mijinta Alhaji Abdallah daba'a cewa komai.
Zarya taitayi ad'akin, ta zauna, ta kwanta, tamik'e tsaye, babu style d'in dabatayiba ranar, gashi tanata fama da toshe hanci sabida wari, daga k'arshe dole tahak'ura da toshen hancin tafara damuwa da inda zata kwanta tasamu barci, dukda d'umbin damuwa da juya abinda yafaru d'azu da zuciyarta keta mafan yi, towai yama akayi bata ta6a d'ago shirinsu mamaba?, kenan batayi aiki da hankalintaba? kokad'an bata ta6a kawoma ranta wani agidan zaisan tana cikin wata k'ungiyaba, Dan sosai takeyin taka tsan-tsan ko 'ya'yanta bata basu fuska tananba balle su fahimci wani Abu, Ashe ita tana shukane a idon makwarwa bata saniba.
"Kai!! Jama'a🤦‍♀, miya faru danine haka?".
Hajia babba tafad'a tana dafe kai, batada mai bata amsa, danhaka tashare kwallar data cika mata ido, wlhy datasan wannan ranar zatazo mata da hakaba, datun khaleel yana jinjiri zata kasheshi, datayi dukma yanda zatayi kar wata mata tasake nak'udar haihuwa agidan.
Haka taita k'ullawa da kwance wasik'ar jaki maicikeda dak'ik'anci🙀😹 har garin ALLAH ya waye.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now