10

4.6K 317 6
                                    

1⃣0⃣

      Alhaji Abdallah Jigawa zaune gaban mahaifiyarsa Ammah yazo gaisheta kamar yanda yasaba akowace Safiya.
   Sund'an ta6a hira sannan yace to Ammah bara nayima Musleem d'in magana yazo yakaiki asibitin kafin rana tayi ko.
    Eto babu laifi yazo d'in, waini ina iro? Tun jiya da yamma bansake sakashi a idonaba, koya komane?.
     Haba Ammah, yaza'ayi mu'azzam yatafi baki saniba, kinsan aikin nasu, jiya bayan isha'i yake sanarmin zaije wani aiki, to inagama a can yakwana Dan badashi mukaje masallaciba da asuba.
      To ALLAH ya taimaka, amma dai yakamata yarannan amusu magana sufito da matayen aure, baikamata kahad'a gurguzun samari agidaba harsu wajen 7, idan wani ya iya tsare kansa wanifa acikinsu bazaiyiba, kanaganin yanda aketa magana awajen taronnan.
    Kiyi hak'uri Ammah zanmusu magana, nima zaman nasu haka ya isheni, musammanma mu'azzam da sultan da mujahedeen.
   A to kadai k'ok'arta, ayanzu ko hafizu aka bama mata zama zasuyi bare su iro masu shekaru 30.
      To Ammah zasuyi insha ALLAH kwanannan.

*_Hotel_*
           Tsaye yake a tsakkiyar d'akin cikin d'an hanzarinsa namasu kuzari yake shiryawa, sanye yake da kaya bak'ak'e irinna police d'in 9ja, saidai akwai abubuwa dasuka banbanta Dana sauran police d'in, bak'aramin k'yau kayan suka masaba, k'yawun haibarsa da cikar kamala irinta nagartaccen ma'aikaci ta bayyana gareshi, abinka da dogon mutum kuma k'ak'k'arfa, gakayan sund'an kamasa, anutse yake d'aura bak'in agogo a tsintsiyar hannunsa, yad'anja gajeren tsaki tareda gyara zaman belt d'in k'ugunsa daya zauna d'am kamar dashi aka haliccesa.
     'Yar jakar dake gefen gadon yabud'e, wata 'Yar k'aramar bindiga yafiddo tareda mata serves da bullet sannan yasak'alata agefen k'ugunsa, yad'auki bak'in space ya mannama idonsa, dubansa yakai ga agogon hannunsa yad'an ta6e baki tareda shafa kwantaccen sajensa, Wanda baicika yawaba saboda yanayin aikinsa.
      Wata bak'ar riga naga yad'auka akan gadon yasaka, abayanta an rubuta *_(POLICE INTERPOL)_*

😨tofa masu karatu, 'yan sandan duniyafa kenan?👨🏼‍✈🤔, Ashe ya khaleel babban gwaskane?.🤥.

Wayarsa k'irar Nokia dake wringing yad'auka, akunnensa yakara, bansan mi'akacemasa daga canba, nadaiji yace, "no kacigaba dabinsa abaya, amma kada kayarda yagane kana binsa, akwai Joseph da youseef suna binka abaya kaima, gamunan tahowa nida Adams da Emanuel da taheer, kakula sosai banason Marsala kaima kasani......kitt ya yanke wayar yana murmushin mugunta dafad'in  Devid kazo hannu.

     Ak'ofarsa tafita yahad'uda zaratan bodyguard d'insa su hud'u, saluting nasa sukayi, shima kad'an yak'ame jikinsa tareda nuna musu hanya, matsawa sukayi yawuce gaba sannan suka take masa baya.
      Agaban wad'ansu bak'ak'en jibga jibgan motoci sukaja birki.
     Matasan samari 3 dake jingine jikin mota d'aya suka iso gareshi da hanzari, suma k'amewa sukayi tareda Sara masa, shima yayi kamar yanda sukayi.
      Kallon fuskar abokin nasu sukayi, sukaga babu alamar wasa ataredashi, yau a ogansu yafito ba abokiba, Dan har aka bud'e masa mota yashiga bai sake kallon Inda sukeba, dama gashi yatoshe idanu dabak'in Google😎.
     Suma Shiga tasu mortar sukayi, motarsace agaba tasu Na binsu.
      Shikad'aine zaune a sit d'in baya, masu tsaronsa d'aya Na driving d'aya nagefen mai zaman banza, laptop Ce acinyarsa yana aiki, fuskarnan acinkushe, babu alamar sauk'i ko sassauci.
     Suraj! Kayi amfani da number Adams kaganarmin Inda yake
    Karon farko danaji daddad'ar muryarsa ayau, muryar khaleel batada sanyi sosai, kuma batada hargagi, tana tsakatsaki.
     Cikeda girmamawa Wanda yakira suraj dake gefen driver yace OK sir.
        Ganinayi suraj ya manna wani Jan abu🔴k'arami dabai wuce girman ma6alliba ajikin glass d'in motar, saiga rubutu yawatsu akai.
   
Mamakine yasakani zaro ido waje😨, araina nace cigaba.
     Ahaka Suraj yagano inda suke, yajuyo yana fad'in sir! Suna Jesse Jackson street, gidana 47.
     OK.
Ahaka Suraj yayta nunama driver hanya, (nidai yau nazama 'Yar k'yauye gaskiya🤕)
     
Gogan nakukam har yanzu idonsa nakan laptop harkokin gabansa kawai yakeyi hankalinsa kwance.
        Ajikin wata church suka tsaya, d'ago manyan idanunsa yayi yanason sanin dalilin tsayawar tasu, hango Adams yayi yana nufo inda suke yasakashi had'iye maganarsa tareda maida kansa ga laptop d'insa.
     Adams daya k'araso yabud'e motar yashigo.
    Da sallama Adams yashigo, ya amsa masa cikeda k'asaitarsa, har yanzu kuma bai d'agoba.
    Adams yace, "Weldon sir!".
           Yauwa kaima sannu yafad'a batareda yad'ago d'imba har yanzu.
    Adams yasan halin kayansa, Dan haka yafara koro bayaninsa kawai, sir naga inda suka shiga, suna gidan Na 116 gefen haggu, saidai nakula gidan yanada fasifar tsaro, Dan Devid yanada matasan yara 'yan daba masu had'arin gask.........
    Hannu yad'aga masa........ Aiko Adams yay tsit tareda had'iye maganarsa, jikake mukuttt, harda wata 'Yar munafukar zufa data tarumasa agoshi, dukda AC dake aiki amotar kuwa.
     Ahankali yad'ago yana kallon Adams, yasaki wani k'ayataccen murmushi, *Wanda nasan yakashe 'yanmatan group d'ina😆😜* lol.
        Duba nan yafad'a tareda turama Adams laptop d'in agabansa.
    Sosai Adams yazaro ido waje, tabbas yagama yadda ogansu kwarone, shita hidimarma saka farar Court yakeyi ajikinsa, bayan yazare rigarsa ta sama, yazaro bindigarsa dake k'ugu yatura cikin takalminsa, sannan yasake gyara zaman wandonsa, duba yakai kan agogonsa tareda furzar da huci yajuya yana kallon motarsu Taheer dake gefensa, dasauri driver yafita yabud'e masa motar sannan suma sauran suka fito.

Adams daketa binsa da kallon kamar yasamu magiji,🖥, ahankali yafurta ALLAH yak'ara lafiya sir Ibraheem Abdallah j, tabbas kai jarumine acikin jarumai, ga gaskiya da rik'on amana, Kasan aikinka sosai, kuma ka yarda da kanka, kamar yanda muma muka yarda da aikinka 100%.
    J! ALLAH yakare manakai aduk inda katsinci kanka aduniya baki d'aya👍🏻......

Hhhhhh to amin Adams, irin wannan kirari haka😅, mudai saimun gani ak'asa zamu yaba nida masu karatu😉. Koya kukace Fan's??🤷🏽‍♀.

Yanzuma saida su youseef sukayi salute nasa sannan Taheer yamik'a masa wata madidaiciyar jaka da key d'in mota.
        Yace, ''kuzama ready fa, Dan banyi zaton komai zaitafi cikin sauk'iba.
   Atare suka had'a baki wajen fad'in OK sir!!.
       d'an harar yamusu sannan yabar wajen.
      Atare suka murmusa dansunsan dalilin hararar tasu.
      Wata k'aramar mota fara mai masifar k'yau dake gefensu yabud'e yashiga, yalumshe idanunsa ahankali yafurta ya ALLAH!.
     ya sauke sassanyar ajiyar zuciya, adu'oin samun nasara sannan yayma motar key.
     Ahankali yake tafiya yana kallon gine-ginen da nazarin numbers d'in gidajen anguwar, harya Isa gida mai number 116, yacije le6ensa nak'asa tareda zare glass d'in idonsa, kallon tsaf yayma gidan har tsawon 2minutes, guntun murmushi yayi yamaida glass d'in sa.
     hankalinsa kwance yake danna horn, kaikace gidansa  yazo.
    Ba'a bud'e gidanba, amma wani matashin saurayi Fari yafito yana k'arema motar kallo.. 
   Da hannu j yamasa inkiya dayazo, babu musu saurayin ya iso ga motar
           J yasauke glass d'in fuskarsa cikin salon nuna shima tantirine yace, "hii my guy yane?. Oga Devid ko yana nan?.
    Saida saurayin yak'arema j kallo ya tabbatar shima d'an tashane. (Dan j yasaka wata hular gashi, kaikace kansane, bashida maraba da 'yan isakan guys).
    Saurayin yayma j alamar yana zuwa.
    Wani lallausa murmushin samun nasara Ibraheem Abdallah j yayi, ya hango nasara amatakin farko.
     Babu dad'ewa dashigar saurayin gidan, aka bud'e masa gate.
    Still saida yasaki murmushin gefen baki sannan yaharba motar zuwa cikin gidan.............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now