78

4.4K 322 1
                                    

78

Su khaleel sunada yawa sosai, amma dukda haka su hajia babba sunfisu yawa, danma ankama wasu aciki, sauk'in d'ayane bakowa keda makami acikinsuba.
       Dukda jikin ya khaleel a sanyaye yake, kuma baisan daliliba, amma hakan baihanashi aro jarumtaba ta musamman ya k'arfafawa kansaba, daboda gudun Matsala.
     Acikin kwarewar aiki suke shiga wajajen, duk wanda akayi karo dashi kuwa cikin dabarar aiki suke gamawa dashi, basuda mafitar data wuce kashesu, saboda suma suna samunsu kashesun zasuyi tunda akwai nakamai a hannunsu.
    Bawai k'aramar k'ungiya baceba, k'ungiyace data tara manyan mutane, masu muk'amai kala-kala, ga dukiya sun tara, saboda business kala-kala dake gudana cikin k'ungiyar, kuma Na manyan kud'i.
      Karya wuyan wani da khaleel yayi bayan nannad'e kansa aleda yasakani rintse idanu, sosai tsoro yashigeni, danganin yanda zukatansu khaleel suka gama bushewa, basajin komai wajen kisan garatan nan.
     Matsalar da aka samu shine cctv camera dake aiki acikin d'akin taron, wadda su khaleel basusan da itaba.
        Wad'anda suke kulada cctv camera d'inne suka ankarar da 'yan k'ungiyar.
   Tashin hankali kenan, wai Wanda ba'a saka masa rana, kusan shekaru 29 k'ungiyar Na aikinta. Amma basu ta6a gamo da makamancin tashin hankalinnanba, saidai amusu tsinci d'ai-d'ai badai gaba-da gababa, don ko kad'an basu aminta wani yafidda sirrinsuba, komai cikin ilimi ake yinsa.
      Hargitsewa hall d'in yayi, masu makamai suka fara d'ana kunamin bindugu, irinsu Momy kam sai neman wajen 6uya.
     Musayar wutane yafara gudana a tsakaninsu, bakajin komai sai k'arar harbe-harbe.
    'Yan jarida kam dasu khaleel sukazo dasu sai d'auka sukeyi, lamarin kaikace film ne wlhy.
     Shirin ma'aikaci da d'an ta'adda bazaizo d'ayaba, dukda gawurtar k'ungiyar su hajia babba takai taringa bama matasa training saboda gudun zuwan rana irin wannan ta kota kwana.
       Tiyagas su khaleel suka fara jefawa cikin hall d'in, dama su sun d'auki matakan kare kai, dandanan wajen yakacame da tari da atshawa, gashi hayak'in yana saka hawaye, masu ciwon asma kuwa saidai addu'a kawai.
      Jefa tiyagas yaba su khaleel damar shiga hall d'in, dukda haka akwai masu taurin zuciya dake harbi har yanzun.
     Amma haka su khaleel sunata samun nasarar cafke wasu, Dan k'ungiyar ta tara maza da matane, harda wad'anda tunaninka bazai ta6a kawo maka ganinsuba awajen, saboda Girman milki ko dukiya.
      Akwai k'ofofin fita da dama acikin hall d'in, wannan ne yabama wasu dama sulalewa, amma ina, wannan shine angudu ba'a tsiraba, dankuwa cikinsu khaleel wasu sun bisu.
    Acikin masu guduwa kuwa harda hajia khaltum da hajia babba.
             Lamarifa yaci tura, komai yagama hargitsewa, acikinsu khaleel dayawa sun sami harbi, 'yan k'ungiyar kam ba'a magana, bayan wad'anda aka antaya barzahu akwai masu harbi a sassa daban-daban.
     Kusan awanni 3 aka d'auka ana Abu d'aya, lamarin kamarma bazai k'areba, kowa yafita hayyacinsa, Dan babu Wanda baiji jikiba, ansami cafke mafi yawa acikinsu, wad'anda suka samu raunuka akafiddosu waje, gawawwakinma haka duk an fiddosu, wad'anda suke k'alau kuwa handcuff aka saka musu, duk aka fito dasu waje, 'yan jarida sunata aikinsu.
     Ya khaleel yafara bin ma'aikatansu yana dubawa, Dan a tantance wad'anda suka mutu, dakuma rauni, duk a wahalce suke.
    Khalee yace, "amma akwai wad'anda babu acikinmu?".
       ''yes Sir! Wasu sunyi yunk'urin guduwane, shine suka bisu".
     "OK!, yakamata azuba wad'annan amotocin da aka kawo, suma akirasu aji?".
      " OK sir".

      Wad'anda basa wajen aka shiga kira, wasu suce sun kamasu, wasukuma suce sunadai binsu binsu abaya har yanzu, amma suna buk'atar k'arin ma'aikata.
       Taheer dai cayayi ahad'ashi da khaleel.
        Faruk yamik'ama khaleel wayan cikin girmamawa.
        A kunne yakara batareda yayi maganaba, daga can Taheer yace, "sorry sir idan bazaka damuba kazo da kanka, wasu mutane hud'u sun shiga gidanka, bazai yuwu mushiga babu izininkaba".
      " gidana kuma Taheer?".
      "Yes sir?".
    ''OK ina zuwa, kubani k'ank'anin lokaci".
        
     Saida khaleel ya tabbatar anzuba sauran a mota, wad'anda suke buk'atar k'arin ma'aikata aka tura musu, wasu kuma suka tafi da motocin wad'anda aka kama, ma'aikatasu kam tuni anyi gaba dasu Dan basu taimakon gaggawa.
    Ya khaleel kansa yasamu raunuka, amma bai damu da kansaba, Na k'asa dashi kawai yake son abama kulawa.
    Key d'in mashin yakar6a ahannun wani ma'aikacinsu, yanufi gida zuciyarsa Na dukan 100-100 saboda fargabar abinda zai Tatar, kenan zarginsa yazama gaskiya, acikin gidansu akwai mai mu'amullah da k'ungiyar? jiyake tamkar zuciyarsa Zata kama da wuta saboda bak'in ciki da fargabar wanda zai tarar amazaunin d'an k'ungiyar.
    Ak'ofar gida yay gamo dasu Taheer dake tsaitsaye, basu shiga gidanba, saboda girmama ogansu.
     Bai tsaya garesuba, horn kawai yayi d'an gwari yabud'e masa gate yashige da mashin d'in, suna su Taheer duk sai suka shiga.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now