17

3.8K 307 0
                                    

1⃣7⃣

    
          Wasu matasan 'yan matane sukazo tarbar su Aysha, sun rungume juna suda anty kubra cikin nuna alamun sunyi murna da ganinta, suduka biyun bak'ak'en fatane, amma jindad'i da sauyin rayuwa yasakasu komawa fresh, haske kawai turawan zasu iya nuna musu.
       d'aya ta kalli Aysha cikin fara'a tace,  "woow Beautifull babie!! Tayi maganar tana shafa kumatun Aysha, tana tambayarta yatake? cikin harshen turanci.
      Murmushin yak'e Aysha tayi, amma takasa amsata.
    Anty kubra Ce tasanar dasu Aysha batajin turanci.
   Abin yabasu mamaki, amma saisuka basar, itama besi sukayi welcoming nata, itakam ta amsa musu yanda yakamata.
    d'aya acikinsu take tuk'a motar, sai surutu suke zubawa da Anty kubra, itadai Aysha batajin komai, besi kam tana sairarensu.
          Had'ad'd'en gida suka sauka, tundaga waje komai yabirge Aysha Dan babu abin kushewa.
     Cikin gidanma komai yagamaji 100%, saidai kowane Bango yasha lik'e-lik'en abubuwa kala-kala, wani Na birgewa, wani naban haushi, (rayuwar turai sai ahankali) suntarar dawasu 'yan matan ak'alla hud'u agidan, duk suna zaune afalo, d'aya ta tadakai da cinyar hamshak'iyar matar dake zaune cikin wando da riga, dukda tanada 'Yar k'iba kayan sun matuk'ar mata k'yau.
     'Yanmata biyu suna gefe suna game d'in lido, yayinda d'aya ke karatun English novel.
     Gaba d'aya suka taso suka rungume Anty kubra harda matarnan.
       Sai murna sukeyi, matarce takama hannun Aysha tana fad'in kubra kincika alk'awari gaskiya, dama John yanata damuna bebynsa-bebynsa.
        Dukda harshen English suke magana, shiyyasa Aysha bata fahimtar komai. Ita gabad'ayama hankalinta nakan kallon 'yan matan, kaf d'insu babu mai shigar arzik'i, watama daga ita sai pant & bra, saiwata shegiyar Riga shara-shara data d'ora asama, wadda sakatama bashida amfani tunda bai rude mata komaiba.
             Besi kam ko'a kwalar rigarta, saima birgeta da 'yanmatan sukayi.
      Sudukansu bak'ak'en fatane, kuma Aysha Na k'yautata zaton duk 'yan Nigeria ne.
       
Bayan su Aysha sun huta sunci abincin da Aysha tacishi akan dole, danjin yunwa zata hallakata, sauk'intama akwai snacks aciki.
     Wanka sukayi kowanne aka bashi kayan dazai saka Dan dagasu sai handbags dama sukazo, hajia kaltum tace ba'a buk'atar suje dakomai.
          Aysha takalli kayan idonta cike da kwallah, yama za'ayi tasaka wad'annan kayan amatsayin sutura? Kai bazai yiwuba gaskiya, zaune tayi abakin gadon d'aure da towel tazabga tagumi.
   Jin anta6ata yasaka d'ago manyan idanunta dake cike da gashi gazar-gazar tana kallonta.
      Cikin maganar kurame budurwar ketambayar Aysha lfy?.
    Itama tamayar mata Cewar babu komai, batason kayannan.
    Shuru budurwar tayi tana kallon Aysha, zuwa can tace to wad'anne kikeso?, cikin harshen Hausa tayi maganar.
   Wannan yasaka Aysha kallonta a kid'ime, dak'yar ta iya d'aga baki tace Dama kinajin hausa?.
       Murmushi mai ciwo budurwar tayi, cikin halin ko in kula da tambayar ta aysha tace karki damu akanjin Sanin wannan, gawad'an nan wando da rigar kisaka, nasan rigar zata kai miki har guywa, saiki d'ora wannan rigar sanyin Asama Dan akwai sanyi ak'asar gaKi bak'uwar shigowa.
    Jinjina kai Aysha tayi, jikinta a sanyaye tad'auki kayan zata koma toilet tasaka.
    No dawo kisaka anan mana, ni fitama zanyi, batajira cewar ayshaba tafice abinta.

     Binta Aysha tayi da kallo harta fice, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana girgiza kanta, kai bata yarda wannan matar bahaushiya baceba, jibifa shigarta, gajeren wandone iya cinya Na jins, yayi masifar matseta, sai 'Yar Riga dabatakai ko cibiyartaba, tashare hawayen dasuka gangaro akan kumatunta, oh ni Aysha, wace irin rayuwa kuma aka kawoni nayi anan? Nida akace zanje nakula da matar aure mai ciki, amma ankayoni gidan gardawan 'yanmata, wlhy gara gidansu hajia babba sau dubu, koba komai addininmu d'aya yarenmu d'aya k'asarmu d'aya, ya ALLAH kayi dubi ga marainiyar ALLAH, karka basu damar cutar dani ubangijina.
    Tana kuka tana shiryawa, tagama tsaf tasaka hijjab d'inta, sallah tagabatar batareda tasan ya lokacin yakeba, Bakuma tadamu da sanin inane gabas.

Zaune suke suduka afalon, kowa yana introduced d'in kansa.
       Babbar hajiya tace sunanta Anty Glory, amma anakiranta Anty Glo...
      Suma suka fara nuna Kansu kowa nafad'ar sunanta, tafarko tace Happy, 2 oyilola, ana kirana lola, 3 Serah, 4 Queen, 5 Shelyn, ana kirana Lyn, 6 meerah.
    Aysha takafeta da edo tana maimaita meerah a la66anta, wadda tamata hausace d'azu, wannan yakuma tabbata 'Yar uwartace bahaushiya kenan?.
     Ta6ata Anty Glo.... Tayi alamar tafad'a itama.
    Ahankali  tace Aysha.
     Anty kubra tace zaku iya kiranta sholy.
   Kallonta Aysha tayi dasauri, Anty kubra ta maka mata harara.
   K'asa Aysha tayi dakanta.
   Daga nana fira suka cigaba dayi, itadai Aysha batajinsu bakuma tasaka baki.

Da daddare maimakon Aysha taga kowa Na Neman makwanci saitaga su Lyn sunata wanka da kwalliyar kece raini.
    Kowaccensu cikin shigar rashin mutunci tafito, sukazo suna sumbatar kumatun Anty Glory tareda mata bey.
          Inakuma zasu wad'annan??. cewar Aysha azuciyarta, saidai babu mai bata amsa.
    Ganin tafara barci Anty Kubra tace taje takwanta a d'akin meerah inda tayi wanka d'azun.
   Tashi tayi tatafi tabarsu sunama besi magana.
   Koda taje d'akin bata kwantaba, saitayi alwala taita nafilfili abinta daneman agaji wajen ubangijin talikai, dukda ita bata fahimci komaibama har hanzun.

____________________________
       Tunda yafito k'ananun security suketa k'ame masa, hannu kawai yake d'aga musu, Taheer nabinsa abaya shida Emanuel.
   d'akinda Oga David yake aka bud'e suka shiga, did'im da duhu tamkar dare, saida Ema yakunna wasu fitulu masu hasken tsiya (irin wanda inhar aka haska idonka dasu saika daina gani nawucin gadi).
   Da sauri Emanuel yagarama ya khaleel kujera guda d'aya tal dake acikin k'aton d'akin, Oga David yanacikin wani keji, (dolene mukirashi keji kasancewar k'arfunane irinna cel kamar baca azageye tsakkiyar d'akin), Oga David yana zaune rashe-rashe a galabaice, kansa aduk'e alamar yana gyangyad'in wahala.
       K'aramin fito ya khaleel yayi tareda d'an buga k'arfen da key.
    Da sauri David yad'ago, ganin ya khaleel ne yasashi aro jarumta ya yafama kansa, murmushi maikama dayak'e yayi, murya agalabaice yace, "halan kasamu TV ne? Kazo katasani gaba, waimiyasama kakawoni nan wajen? Ko salon naka business d'in kenan?.
      Wani murmushin k'asaita ya khaleel yasaki tareda shafa kwantaccen gashin sajensa dabai cika yawaba saboda askewa dayakeyi, baice komaiba sai ID cat d'in aikinsa daya nunama Oga David.
     Cikin d'age gira yajanye abinsa yana fad'in why not idan kanason mud'ora daga inda muka tsaya a business d'in namu.
          David yay dariya, yaro kana wasa da Lion fa.
        Ya khaleel yata6e bakinsa cikin salon ko inkula yace ayya had'in yayi daidai kenan, ga Lion, ga kuma young tiger🐅.
       David zai sake magana Taheer yadaka masa razananniyar tsawar datasa bakinsa rufewa 6am.
    Murmushi kawai ya khaleel yayi, cikin muryar data k'ara razana David yace Chubuzor Obinar! Suwaye abokan kasuwancinka?.
         Babu.
Abinda David yafad'a kenan yay shiru.
    Ya khaleel yatsura masa manyan idanunsa masu shegen kwarjini, acikin razananniyar murya yace waye Alhaji Alasan kwangila!!?.
     Wata zabura David yayi, yanayinsa kad'ai ya isa yanuna maka yarazana dajin sunan, amma dayake ance d'an iska d'an iskane bakinsa Na rawa yakuma cewa bansanshiba.
   Ran ya khaleel yafara 6aci, yakula sai an d'umama jikin David zai basu had'inkai.
   Ganin yanayinsa yasaka taheer fad'in kafad'a masa David kafin yanzun kayi nadamar turjiyarka.
    Wata dariyar rashin mutunci David ya kece da ita, cikin dariyar yanuna Taheer, kai d'an k'arami!. da oganka nake magana bakaiba, bar manya suyi zancensu wannan ba shigarka baceba.
     Tsawa ya khaleel yadaka masa Short up!!!!!!!!!.
        Yanda yay maganar cikin k'araji saida ya girgiza hantar securitys d'in dake waje.
       Taheer yace azuciyarsa David kashiga uku, tunda harkayi gangancin saka ran j! 6aci haka........
    Kwala kiran Samuel da ya khaleel yakeyi shine yakatse tunanin Taheer.
    Cikin tsawa ya khaleel yace Sam..... Kaida Mahfouz ku koyama shegennan ladabi!!, dayasan yanda zai ringamin magana!!!!.
     Jikin Samuel narawa yace, "OK sir, sorry sir! Tareda Salute.
       Bai tankaba  yafita a harzuk'e.
    Taheer kam kujerar da ya khaleel yatashi yaja yazauna danson ganin yanda za'aci uban Oga David.........

___________________________
          Akusan tsaye Aysha takwana tana fad'ama ALLAH damuwarta da rok'on yakareta. Su meerah kam basu dawo gidanba sai k'arfe 5 Na asuba, Aysha Na sallar asubahi tashigo d'akin. Kallo d'aya zaka mata kagane abuge take. Bin Aysha tayi da kallo cikin mamaki da kad'uwa, itafa tamanta anamayin sallah, takaudakai cikin k'unar rai tafad'a kan gado ko takalmi bata cireba.
    Aysha ta idar da sallah tajuyo tana kallon meerah dake kwance rubda ciki, tausayinta Yakama Aysha, dantakula kamar tanacikin damuwa tun ajiya.
     Addu'a tayi tacigaba dayin azkar d'inta.
    
       Darana Aysha da besi sai Anty kubra da Anty Glory ne kawai ke warkajaminsu agidan, amma duk sauran 'yanmatan gidan wuni sukayi barci, (dare yazame musu rana, rana tazama darensu).
 
      

Bayan sati biyu...........✍🏿

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now