54

4.8K 348 2
                                    

54

   
      ......Anty zuwairah ce tafara ganinsa tace, "yauwa khaleel aigara dakazo, yau saina zane mara kunyar matarka a gidannan, ita hartayi balagar aikama da momy zagi?".
     Shiru yayi yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya, Anty zuwairah tace, "wai bakajin minace? naji kayi shiru".
    "Naji". 'Yafad'a yana cigaba da tafiya hanyar d'akinsa'.
    Sudai su mufeeda baki yamutu, sunyi tsit.
   K'ofar d'akin nasa yamurd'a zai shiga yajita 6am. Mufeeda tace, " ya khaleel tana cikifa ta kulle kanta saboda tasan batada gaskiya".
        K'ala baiceba, sai harara daya bankama mufeedar, tayi k'asa da kanta tana k'unk'uni.
   Yafara kiran " Aee'sha! Zoki bud'e k'ofar nan".
    Dukda tagane muryarsace saida tace, "wanene?".
     "k'aniyarkice, kibud'emin k'ofa nace!!". 'Yay maganar a tsawace'.
          Batareda tabud'e k'ofarba ta jingina ajiki ta fashe da kuka, ''ALLAH ya khaleel nabud'e dukana zasuyi, nikuma tsoro nakeji, kace sutafi sannan saina bud'e".
      Huci yafurzar daga bakinsa. yace, "Aee'sha karki bari raina ya6aci, kibud'emin k'ofa, babu wanda zaimiki wani Abu acikinsu ina nan".
     " har Anty zuwairah? ". 'Aysha tayi maganar tana kuka'.
     Cikin tsawa yace, "k! Wlhy zan sa6a miki idan baki bud'emin nan da 3minutes ba!!".
     Su Anty zuwairah kam duk dad'i yakamasu, sunsan saiya yima Aysha dukan mutuwa. k'ilama ya saketa saboda zagin momy datayi, kai da sunji dad'i kuwa.😂
         Aysha kam saida taga minti ukun daya bata sunkusa cika sannan tabud'e k'ofar.
    Yana niyyar Shiga su Anty zuwairah suka tashi suma, hannu yad'aga musu alamar su dakata, sannan yashige, yamaida k'ofar yarufe harda Murza key.
     Aysha tak'ara k'arfin kukanta, tana ja da baya dafad'in wlhy ya khaleel ni ban zagesuba, sunema suketa zagin Abbana, ALLAH Anty mufeeda Ce tahad'a".
     Ko kallon Inda take baiyiba, ya ajiye jakkar laptop d'insa da hula akan gado, fuskarnan a murtike, babu alamun wasa, yafara cire ma6allan rigar Uniform d'insa, saida ya 6alle tas sannan yafara k'ok'arin zare belt d'insa.
    Aysha tanacan jikin Bango tana kuka, duk zatonta dukanta zaiyi da belt d'in.
      Ganin yacire komai, dagashi sai vest da boxer ta rintse idanunta, ya zauna akan sofa yana kwance igiyar takalminsa, sannan yazare har sock's d'in, yana mik'ewa Aysha tak'ara k'ank'ame jikinta, azatonta kanta yayo, saitaga yashige toilet.
     Ajiyar zuciya tasauke da baza idanu kozataga key d'in, bataso yafito ya sameta a d'akin, kuma tana tsoron fita sabodasu Anty zuwairah.
       Suna falo kuwa sai cika da batsewa sukeyi, suna jiran jin hukuncin da ya khaleel d'in zai yankema Aysha, amma sai sukajiyo tsit, sunsan wani lokacin idan yanacin uban mutum baya barinsa yayi kuka, shiyyasa sukad'an k'ara jira.
        Inda yabarta anan yafito ya sameta, sanye yake da lemon green d'in rigar wanka, hannunsa rik'eda k'aramin towul yana goge Kansa zuwa fuska, da'alama wanka yayo.
    Aysha tana ganin Yakama igiyar rigar zai kwance tazame k'asa, tareda cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana rera kuka a hankali.
    Kallo d'aya yamata ya d'auke kansa, cigaba yayi da shafa mai, yasaka k'ananun kaya marsa nauyi dabazasu takura masaba, yad'an yafesa turare.
     Inda Aysha take zaune yanufa, yad'auketa cak, aikam tafasa masa k'ara, tsawa yadaka mata, tayi saurin to she bakinta da hannu.
   Su Anty zuwairah dake falo suka fashe da dariya, harda tafawa, su duk zatonsu ya khaleel Na punishing d'in Ayshane.
       Ya d'orata visa gadonsa, ya haye shima tareda rungume kayarsa, ya lumshe manyan idanunsa dake cikeda barci, mutsu-mutsu Ayshan tafara, yabud'e ido dak'yar Dan barci harya fara figarsa, "k wlhy inbaki nutsuminba zan dakaki ad'akinnan, sannan Na turaki waje su Anty zuwairan suyi duk yanda sukaso dake, stupid girl kawai".
       Tsit Aysha tayi, takoma ta lafe a k'irjinsa, Yakuma rungumeta da k'yau, yamaida idanunsa ya lumshe, cikin lokaci k'ank'ani barci ya d'aukesa.
     Aysha tabud'e idanunta dasukasha kuka, duksun mata nauyi, fuskarsa take k'arema kallo, yanda yake barci cikin nutsuwa, numfashinsa nafita ahankali, fuskarsa tayi fayau ko'a fili bata zama haka Dan tamkar yana murmushi, wani dad'i ya mamaye zuciyar Aysha, wai itace kwance visa k'irjin ya khaleel yau? abinda ko'a mafarkinta bata ta6a zaton faruwarsaba, "ya ALLAH Na gode maka da wannan k'yauta, shima ALLAH kasaka MASA sona, fiyeda yanda nake sonsa".
   Haka taita tunane-tunane itama har barci 6arawo ya saceta.
            Afalo kuwa bayansu Anty zuwairah sunji ihun Aysha da tsawar da ya khaleel yaymata sai Anty zuwairah tace sutashi suje, tasan khaleel zai tunkud'o k'eyar Aysha har gaban momy, bayan yagama kir6arta, da wannan shawarar suka koma cikin gida, tareda kaima momy dadd'an labari, wai khaleel nacan na zane Aysha, harda kulle k'ofa.
    Momy taji dad'i sosai, har zuciyarta tad'an huce, amma dolene tad'auki matakin gaggawa, inba hakaba Aysha zata musu 6arin makauniya agidannan.
     Anty shukura kam hankalinta yatashi, batareda sanin kowaba tanufo gidansu Aysha, tsit taji falon, harta juya amma hankalinta yakasa kwanciya, komawa tayi tacan bayan d'akunansu, talek'a window d'in ya khaleel, kwance ta hangosu manne da juna suna barcinsu hankali akwance, murmushi tayi dafad'in Alhmdllh.
     Cikin nishad'i takoma tacigaba da harkar gabanta, tana mai k'arajin k'aunar khaleel d'in aranta, da halayensa masu matuk'ar birgeta.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now