84

4.4K 317 1
                                    

84

       "Ibraheem!! Kana nufin zaka iya kasheni?."

    "Ba Ibraheem ba, Ibraheem Abdallah, kokice j! domin samun sauk'i, kisa aranki baki ta6a sanin wannan Ibraheem d'inba kawai, yafi miki sauk'i".

     " iyeee, lallai d'an zaki yagirma".

      "Young tiger! Baya ja'inja da kowa". 'Yay maganar yana harbin gefen hajia babba".
       Rud'ewa tayi ta gigice daga ita har hajia khaltum d'in, su baffah kam duk rintse idanunsu sukayi, duk zatonsu khaleel ya harbi hajia babbane.
     Saiga mutuniyar taku jiki Na rawa, har taune harshe takeyi wajen fad'in " zan fad'a maka komai wlhy yalla6ai, bama saika harbeniba, ALLAH ya huci zuciyarka Oga".
           Wani murmushin mugunta khaleel yayi, yagyara zamansa yana wasa da bindigar a gefen kumatunsa, idonsa k'yam akan hajia babba.

    _kamar yanda kowa yasani sunana Laurah, innah jummai k'anwace ga Halima (Ammah), uwarsu d'aya ubansu d'aya. ayanda innah keban labari tun suna k'anana tafi Ammah k'yawu sosai, amma abin bak'inciki mutane sunfi son Ammah, sukance Ammah tanada nutsuwa da girmama mutane, innah jummai kuwa akwai rawar kai, ga rashin kunya, ko iyayensu sunfi nunama Ammah soyayya fiyeda innah, kafin innah jummai tasamu Abu sai Ammah tasami ukunsa, tun alokacin innah jummai tatashi da k'iyayyar Ammah aranta, kullum burinta tayaya zata fi Ammah komai, aganinta tunda tafi Ammah k'yau, ita yakamata tafara samun komai kafin Ammah tasamu, amma ina, kullum Ammah ce asamanta._
        _haka suka cigaba da rayuwa cikin rashin jituwa, kowa yana d'aukar hakan amatsayin fad'an sako, amma ita innah jummai har ranta takejin k'iyayyar Ammah, gidansu bawani karatun boko akeyiba alokacin, sai makarantar Allo, wata rana sundawo daga makaranta da hantsi, saisuka gamu dawani bak'o akan besfa🛵, Ammah ce kawai ta gaidashi, amma innah jummai ta6ige da k'are masa kallo, saboda lokaci d'aya yasace zuciyarta, bak'onnan ya tambayesu gidan wani mutum dayazo nema, cikin ladabi Ammah tamasa kwatance, yamata godiya dasaka mata albarka, sannan yad'auki taro da sisin kwabo yabata, amma sai Ammah tak'i kar6a, yay magiyar duniya tak'i amsa, caraf sai jummai ta kar6e kud'inan, murmushi kawai yayi yaja besfa d'insa yatafi, itakuma Ammah tashiga yima innah jummai fad'a akan kar6ar kud'inanan, tun a hanya fad'a ya sark'e tsakaninsu, har sukazo gida._
    _ALLAH yajik'an baba mai d'anwake mahaifiyar su innah, ta tambayesu abinda yahad'asu, Ammah ta sanar mata komai, fad'a baba tayima Innah jummai, sannan ta kwace kud'innan, ta aiki Ammah gidan da bak'onnan ya tambaya taje ta maida masa kud'insa. Wad'annan abubuwa dasuka farune suka saka Rufa'ee k'aunar Ammah, baiyi k'asa a guywaba yasamu Malam Saminu yayan mahaifiyarsa da wannan batu, shikuma yazo har gida yasanarma Malam yahuza babansu Ammah. Mutananda sunrigada sun gina 'ya'yansu akan tarbiyya mai k'yau, dan haka babu batun jin ra'ayin Ammah Malam yahuza yabadata. Saidaga baya aka sanar mata._
        _wannan aure shine yazama sanadin k'arin k'arfin k'iyayya tsakanin Ammah da inna jummai, domin ita sosai takeson Malam Rufa'ee aranta, gashi awannan karonma Ammah takuma kwace abinda takeso a hannunta, daga wannan karon Innah jummai tad'auki aniyar tarwatsa Ammah dadukkan farincikinta, tadad'e tanamata bitada k'ulli amma babu nasara, har itama tasamu miji tayi aure, wato mahaifina, ALLAH ya azurtasu dasamun haihuwata, alokacin Ammah Nada 'ya'ya biyu, Abdallah da ma'aruff, Innah jummai Ce tayima Ammah asiri haihuwarta tatsaya, acewarta bazai yuwu Ammah tayita haihuwar mazaba itakuma gashi da mace tafara, ALLAH ya hukunta kwayayen haihuwar Ammah biyune kawai a duniya, shiyyasa bata sakeba, domin asiri yana tasirine da izinin ALLAH. Saidai kuma ubangiji ya nunama innah jummai iyakarta, domin itama tundaga ni saitaita haihuwar mazan suna mutuwa, wannan yasakata d'aukar burun ruguza 'ya'yan Ammah biyu._
          _Tunda nafara zama budurwa ALLAH ya jarabceni dason Abdallah, har d'oki nakeyi idan yazo gidanmu, amma kullum innah jummai Na kwa6ata akan naciresama azuciyata, Dan bazata amince Na auresaba, bana saurarenta ko kad'an, dukda kullum karatunta naburin nayi kud'i yana tasiri azuciyata, Dan innah jummai batada burin daya wuce Na auri mai kud'i nima nazama hamshak'iyar mace, kodan ta nunama Ammah cewar tafita, ALLAH yatsareni daine kawai banta6a aikata siyar da mutuncinaba, amma ansha biyana kud'i nasamo budurwar daza'ayi iskanci da ita, idan nasamo kud'in kuma innah jummai bazata ta6a tambayata ina a samosuba, saima taita sakamin albarka da min kirari, *Laure, lauratun babanta, farar haihuwa adon kowace uwa*, kullum kirarinda Innah jummai kemin kenan idan akawo mata kud'i, wani zuwa da Abdallah yayi gidanmu gaida innah jummai na rud'e daganin yanda yazama cikakken mutum k'yak'yk'yawan saurayi San kowacce budurwa, tundaga wannan alokacin natada billi sai shi, inba hakaba kuma zan gudu daga gida, innah jummai namatuk'ar sona, alokacinne kuma taga yakamata ta yadda da aurenmu kodan mu mallake dukiyar da Abdallah Muke tunanin yanada ita, alokacinma shi bawani kud'ine dashiba, rufin asirin ALLAH ne kawai._
      _nasan Abdallah bays sona, an tursasashi aurenane kawai, domin yanajin maganar iyayrnsa, itakuma Ammah tayarda da aurenmune domin k'arin k'arfin dank'on zuminci itada 'Yar uwarta, batasan burin 'Yar uwartata tarwatsata baneba. abinda ya tada hankalina nida innah jummai shine haihuwar mata Dana fara, domin burinmu bai wuce nahaifi 'ya'ya mazaba danmu mallake dukiyar Abdallah, bayan haihuwar Zuwairah inada cikin shikurah muka had'u da hajia khaltum taje sibiti ganin likita itama, tundaga nan muka kullah k'awance, tacemin a Abuja take aure, yanzuma tazo Kano bikine zazza6i yakamata tazo ganin likita._
         _bayan haihuwar shukurah babu dad'ewa sai Abdallah yazomin damaganar k'arin aure, ankai ruwa rana sosai saboda Innah jummai da Khaltum suna zugani akan karna yarda nabar Abdallah k'ara aure. ALLAH ya rubuta fad'ima saita zama matar Abdallah, saigashi anyi bikinsu, tunda fad'ima tashigo gidan nahana kowa zaman lafiya, sannan duk cikin data samu saina zubar dashi ta hanyar bata magani batareda tasaniba, Dan banaso tahaifi namiji kafinni Na Haifa, bazai yuwu tagaji dukiyarsaba bayan nafita shan wahalar zama dashi, wannan rashin zaman lafiyar tamu yasaka Abdallah auro Bilkisu, nanma ansha fama kam sosai, zuwan Bilkisu gidan naso muhad'e kai da ita, danna samu nariga 6arar da cikin daduk zata d'auka cikin hikima, saboda aringa jingina hakan ga fad'ima, amma sai Bilkisu tak'i amincemin, dama can ba sonta nakeyiba._
         _Alokacin kusan tare mukayi goyon ciki mu uku, saidai namu yana gabadana fad'ima, nayi yunk'urin zubarma da Bilkisu ciki hakan bata faruba, ALLAH yarubuta saikazo duniya, rana d'aya muka haihu nida Bilkisu, amma narigata haihuwa, nahaifi mace saidai batazo da raiba, banyi bak'incikin mutuwartaba saboda macece, saima khaltum dataita nuna jimaminta, ganin ban kulaba ta tambayeni dalili, nafad'a mata ba mutuwar 'Yar Dana Haifa bace damuwata, damuwata mi Bilkisu zata Haifa?._
        _khaltum tace tabbas wannan abin dubawane aminiya, amma ga shawara, mizai hana muhad'a kai da likitan nan, idan Bilkisu namiji ta Haifa mu kasheshi kawai, banyi musuba, nan take naji Na amince dabatunta. Kud'i masu yawa muka bama likitannan sannan ya amince da buk'atarmu, bayan haihuwar Bilkisu sukaje shida wata nurse da khaltum suka sato mana jariri, aka ajiye mata d'iyata matacciya._
      _saidai kuma da'aka kawo jaririn sainaji bazan iya kasheshiba, nacema khaltum baikamata mukashe jaririnba, gara kawai narik'eshi amatsayin shine Na Haifa, kinga zuwa nan gaba samu kori Bilkisu da fad'ima, shikenan jaririnnan yazamemin sandar dukan kowa, dukiyar Abdallah tazama tamu, nan take tayi na'am da zancena, harda min jinjina. Daganan kadawo hannuna, abin mamaki kuma kak'i kar6ar nonona, daga bayama sai nonona Yakoma fidda yellow d'in ruwa, Ammah tadage akan bilkisuce zata shayar dakai, ankai ruwa rana sosai, danni zatona za'a gane alokacin, Ashe kuwa fad'ima tagane komai. Alokacin datazo mana dabatun mu maidama Bilkisu d'anta mukai mata barazana da mutuwa, harda Bilkisu da jaririnma gaba d'aya, nasan badan tsoro fad'ima tabarmuba, saidon wani dalilinta nadaban, saidai bansan wane dalili baneba, (nasan fad'ima jarumace, wannan yasakanima nake mugun shakkarta, dukda bana nunawa agabanta kuwa)._
         _wannan sirri namu da fad'ima tasani, mukagafa dolene musan yanda zamuyi tabar gidan, Idan bahakaba zata 6aro mana aikine, dama ga cikin jikinta yana bani haushi, kullum fargabata karta haifi namij, mun shareta alokacin, har zuwa wasu watanni sannan muka 6arar da cikin jiKinta, muka had'a kai da likita kuma yace dama tadad'e tana zubarwa, sannan Na ajiye mata maganin zubar da ciki ad'aki Abdallah yagani, domin nasan yanda yake da masifar son 'ya'ya dama. Munyi nasara kuwa, Dan alokacin Abdallah yasaki fad'ima, daganan muka koma burin ganin munraba Bilkisu da gidan itama, bayan muncigaba da bibiyar fad'ima muna ma rayuwarta barazana, har muka saka aka saceta dukdan dai tatsorata karta tona mana asiri watarana._
         _banta6a goyaka abayanaba, banta6a cin kashinkaba, duk wani wahalar raino da uwa kanyima d'anta banta6a yimakaba, musamman na d'akko mai raino take rainonka, sai Bilkisu itama datakeyi idan ankaika kasha nono, tsakanina dakai nad'an d'aukeka, shima nata maka mugunta kenan kana kuka, amma babu wanda yafarga da hakan, bak'aramin k'ok'ari nadinga yiba wajen danne zuciyata ina nunamaka soyayya agaban mutane, dan wlhy nagama tsanarka tuni, natsaneka saboda kaid'in d'an mak'iyyatane, natsaneka saboda kowa yana nunamaka soyayya agidannan, Ammah, bilkisu, Abdallah, hakama su zuwairah, suk motsinsu nakanka, bada son ran innah jummai nake rainonkaba, dan bata ta6a d'aukarkaba tunda take, dukda namata bayanin dalilina na d'aukarka hakan baisa taji zata sokaba, yakamatama kakula da yanda nake nunama 'y'a'yana mata soyya fiyeda kai._
       _Muncigaba da farautar cikin daduk Bilkisu tasamu amma ALLAH bai bamu nasaraba, babu dad'ewama tahaifi Rufa'ee (khaleefa), takuma yin Sultan, tayi mujahedeen, hakan yakuma haddasa wutar k'iyayyarta araina, gashi ALLAH yahananin damar d'aukar mataki, kuma nid'in haihuwar tama tsayamin cak, tunda muka haihu tareda Bilkisu tawa ta mutu bansake koda 6atan wataba har Bilkisu tayi haihuwa 5, sai bayan haihuwar Ramadan nasamu cikin Mugeedah ma, sannan kumane khaltum taja ra'ayina shiga k'ungiyarnan ta safarar yara mata, tacemin nabar wahalar banza akan jiran dukiyar daba tawaba, waddama alamomi sun nuna Bilkisu Ce zata gaje komai, inzo nanemi nakaina, harma sainafi Abdallah shahara, kamar yanda innah jummai take buri, ni inhar zan samu kud'i babu ruwana dawani tantance abinda zanyi, hakan yasaka Na sanarma innah komai, atake tabani goyon baya, dakuma jinjinamin, tanamai farincikin lokacinne zatafi Ammah komai, zata nunama Ammah itamafa karanta yakai tsaiko, ayanzu tafita komai da komai, lokaci yayi dazataga Ammah 'Yar uwarta ak'asanta, itama tadaina hawa samanta._
     _wannan farincikinne danagani atattareda mahaifiyata ya k'arfafamin guywar Shiga wannan k'ungiya, Alhmdllh nasamu abinda kuma nake buk'atar samu, hakama mahaifiyata, dannafi Abdallah komai, dandai kawai bana nunawane, naginama mahaifiyata k'aton gida, nazubamata dukkan abinda take buk'ata, daga alokacin kuma takoma saka sutturar da Ammah bata saka koda kwatankwacinta, sannan bana jira Abdallah yamin komai, dan nafisa komai, nazama hamshak'iyar mace tamkar yanda mahaifiyata tayi buri, nashahara sosai, saidai girmankane yaso durk'usar dani, domin nakula kafara shigamin hanci tuni, wannan ne yasakani d'aura d'ammarar kasheka kafin kai kaga bayana, saidai kash, Ashe har zuwa yanzu fad'ima Na bibiyar rayuwata batareda nasaniba, duk zatona ta manta da komai, kosanda tace zata dawo gidan ba kishine yasakani binta kanoba, fargabata karta dawo da abinda yawucene kawai, banta6a jin kishin saudah ba, Dan lokacin data shigo gidan nasamu hanyoyin samun kud'i, Ashe munafukace ita, shiru-shirunta Na munafuncine itada Bintu, ALLAH ya Isa tsakanina daku, ziciyata bata ta6a kawo dabaibayin da fad'ima taminba kenan, saboda banta6a tunanin wani mahaluki agidan zaisan sirrin sana'ataba, tunda komai cikin taka tsantsan nakeyinsa, hankalina bai fara tashiba saida shegiyar yarinyarcan ta bayyana amatsayin d'iyar Fad'ima, harma tsohuwarcan tahad'a aurenku, saikuma fitar dare Dana kama mufeedah nayi, rushewar komaina shine cikin mufeedah😭, tak'are maganar da rushewa da kuka....._

       Kowa kakalla awajen kallon mamaki sukema hajia babba da inna jummai, bakin Ammah bud'e tak'arasa gaban innah jummai.
      "Jummai yanzunan har lalacewar zuminci tawannan zamanin takai kiringa bak'inciki dani?, nid'infa yayarkice ciki d'aya, mukad'ai iyayenmu suka Haifa, yanzunan jummai sabodani kika rusa rayuwar d'iyarki tall guda d'aya?, saboda son ki fini kika dinga walagigi da tarbiyyarta haka? Haba jummai, miyasa baki fad'ama iyayenmu kinason Malam Rufa'ee ba alokacin? wlhy dakin fad'a saina barmiki shi, Haba jummai, miye duniyama bare abinda ke cikinta, yau INA iyayenmu? dukfa sun mutu, INA Malam Rufa'een dakikayi danshi? Yamutu tuni ya barni, mumafa dolene mumutu, inhar d'an uwanka zaita wad'annan k'ulle-k'ullen dankawai yafika, to tayaya duniya zata zauna lafiya? tayaya zuminci zaiyi k'arko aduniya? Shiyyasa babu Abu mafi lalacewa awannan duniyar kamar zuminci, hassada da bak'inciki tamaidamu mak'iyan juna, kullum burinmu muzama saman 'yan uwanmu, bamason kowa yafimu, bamason ace wane shine wane, yakamata kigane wani sirri awanan labarin jummai, *Hassada ga mai rabo takice*, kullum kina bak'incikin ALLAH ya d'aukakani samanki, burinki kifini, amma kuma ALLAH nata d'agani sama, koda kinsamu abin, sainikuma nasamu mafiyinsa tawata hanyar. kin tsaidamin haihuwa, dukda nayarda hakan tsarin ALLAH ne, amma sai ALLAH yabani jikoki, kusan talatin, ga 'ya'yan jikoki kuma, burinki ki mallake dukiyar zuri'ata domin kifini, sai ALLAH yabama d'iyarki dukiyar dazata zame muku masifa keda ita, kinraba baiwar ALLAH da d'anta, sai ALLAH ya azurtata da haihuwar ninkin baninkin d'insa, sannan yasaka soyayyar juna tsakaninsu cikin hikimarsa, kin d'aukesa Dan gur6ata rayuwarsa sai ALLAH ya shiryasa yazama shine dodon dazai dinga tsorata rayuwarki, k'arshema shine zai ruguzata gaba d'aya.
       Kin fidda fad'ima agidan mijinta sai ALLAH yabata ikon zuwa wani gida tahaifi wadda zatazama jagorar tarwatsa dukkan farincikin 'yarki da sarautar datake tak'ama da ita, sannan yahad'a Auren 'ya'yayen mak'iyanki domin yanuna miki ked'in bakomai baceba, wannan kad'an kenan daga ikonsa, cikin mufeedah ALLAH ya d'and'ana miki irin bak'incikin da iyaye kanjine lokacinda aka salwantar da mutuncin 'ya'yansu, duk wannan abubuwan kinsaka d'iyarki yinsu domin ki wargaza rayuwata, sai ALLAH ya nuna miki iyakarki, yaruguza dukkan taki rayuwar, gakunan acikin nadama dagake har ita, kai jama'a ALLAH yarabamu da hassada.

     Kowa da amin ya amsa, su Anty zuwairah suka fice suna kuka, dukda k'aunar dasukema mahaifiyarsu bazasu iya kallon su Ammah ba, ashema momy basu taso amatsayin 'ya'yantaba, maza taso ALLAH yabata su.
    Kowa da kallo yabisu, momy kuma tafashe da kuka tana fad'in innah kin cuceni, duk kece sanadin rugujewar rayuwata, dabaki d'orani akan wannan karatunba daban tashi akan dokin zuciyaba, wlhy bazan yafe mikiba keda khaltum, ALLAH ya Isa tsakanina daku, ALLAH yajik'an mahaifina, kullum nunamin yake karnabi hud'ubarki, Dan bazata kaini hanyar 6illewaba, watarana saina tsinci kaina a Dana Sani, gashi kuwa lokacin yazo, Takai 'ya'yanama NBASA buk'atar ganina, takuma fashewa da matsanancin kuka tana tari.
      Khaleel Kansa aduk'e, idonsa yayi jajur, hakama jijiyoyin Kansa sunyi rud'u-rud'u, yama rasa yanda zai fassara wannan *bashin gaba* haka, kawai gani akayi yamik'e, ya tafa hannayensa saiga Adams yashigo, Kansa aduk'e yace, "Adams kowa yafita, Ammah da baffah da Anty Mamie, mama, ummi amarya, Aysha sausu Mujahedeen kad'ai nake buk'ata".

   "OK sir".

    Adams yafitada su Tasleem, su hasnah, da 'yan uku, matansu ya sultan.
      Ahankali khaleel yatako har gaban Ammah, kowa kallonsa yakeyi da tunanin abinda zaiyi, gashi yayi k'asa da Kansa yak'i kallon kowa awajen.
    Hannun Ammah Yakama yaje har gaban hajia babba da ita, sannan yakoma bayan Ammah yatsaya, yakamo hannayenta yad'ora saman bindigar hannunsa, kaitsaye hajia babba ya saita, nanfa kowa ya rikice, baffah namasa magana amma bai sauraresaba, ita kanta Ammah jikinta rawa akeyi, azatonta khaleel zaisata takashe hajia babba ne, innah jummai kuwa kuka da kururuwar ihu tafasa akan ataimaketa zasu kashe mata d'iya.
     Dirimmm!! Sukaji fitar harbi da ihun hajia babba lokaci d'aya, khaleel yasaka Ammah rama harbinta a k'afar hajia babba kamar yanda itama ta harbi Ammah ranar.😂👍🏻

        Hajia babba Na kwallah k'ara khaleel yamatsa daga kusada Ammah, yabatta da bindiga a hannu, yajuya yafita yana hawaye, duk binsa da kallon tausayawa sukayi, inkacire hajia babba dake ihun azabar shigar bullet cikin k'ashin k'afarta, saikuma innah jummai dataje tarik'eta tana salati.
    Tarine ya sark'e hajia babba, tafara yinsa babuji babu gani, saiga jini nafitowa, amatuk'ar tsorace ta kwallah k'ara tana kallon hannunta cikin zare idanu waje.
     Adams ya kar6i bindigar hannun Ammah, sannan yayi waya akazo aka d'auki hajia babba data fara galabaita, ga aman jini, ga jini nazuba ta k'afarta, sai aminiyarta khaltum daduk ta tsure da tsoron Khaleel, tunda har ya iya aikata haka ga hajia babba air kowama saiya shafama Kansa lafiya, tunda yakasa sauraren tsawatarwa da mahaifinsa kemasa akan karyabharbi hajia babba.
    Dole suma suka fito, duk suka Shiga motoci bisa umarnin Adams.
    Khaleel kam office d'insa yashige ya kulle kansa yana kuka tamkar mace.

Haka aka maidasu gida jikin kowa a sanyaye, babu mai iya koda tari acikin motocin.............✍🏻

CIKI DA GASKIYA......!!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon