50

4.6K 317 1
                                    

50

     Jama'a sunata shirye-shiryen tafiya Abuja, domin rakkiya ga Aysha.
     Itakam tanacan k'uryar d'aki sai zuba kuka takeyi, gabad'a tausayin kanta takeyi, tasan tana son ya khaleel, amma shi takula baidamu da itaba ko kad'an, jibafa tunda aka d'aura aurennan bataga idanunsaba, ahaka za'ayi rayuwar aure kenan?.
       Hayaniyar jama tafara jiyowa suna fad'in mitocin d'aukar amarya sunzo, gabantane yacigaba da fad'uwa, kukanta yak'aru, har rawa jikinta keyi saboda tashin hankali.
    Ahaka gwaggo Asma'u tashigo ta sameta, "haba Aysha, kekuwa bazaki daina kukannan bane hakanan? Kowafa dahaka yafara, yanzu y'an uwanki basun kwana gidan nasu mazajen ba, kinsandai tafiya babu fashi aii, kikamaje wata k'asar kikayi hak'uri zama babu mu bare nan gaki ga Yaya fad'ima, kinga tashi ki saka wannan hijjab d'in da nik'af kinji, yihak'uri bar kukan hakanan?".
    Haka taita lallashin Aysha harta kuma sakata ta k'imtsa, ankai Aysha tayi sallama da dangin mahaifinta tsofaffi maza da mata, aka kaita wajen Umma wadda takasa magana sai kuka itama, dak'yar aka 6an6are Aysha daga jikin Ummah, mama ankaita tayi sallama da ita, (ita sai zuwa jibi zata koma abujan).
      Haka akafita da Aysha tana 6arzar kuka, sanye take cikin atanfa ruwan zuma mai duhu da ratsin ruwan shanshanbale mai haske, hijjab d'intama ruwan Zuma, sai bak'in nik'af, tana kallon kowa tacikin nik'af d'inta, dukda har yanzun tanata kwarar da hawaye kuwa.
      Gabanta yafad'i lokacinda idonta ya sauna akan ya khaleel dake jingine da wata farar mota, rabonda taganshi harta mantama ita, sanye yake cikin shadda galila ruwan sararin samaniya, (sky blue) ya murza hula kalarta, hakama takalmansa, agogonsane kawai bak'i, yayi masifar yin k'yau, mayun idonsa k'yam akan Aysha da fuskarta ke lillu6e da Nik'af, dukda baya ganin fuskartata hakan baihanashi cigaba da kallontaba, baka Isa gane wane yanayi yake cikiba.
    Gwaggo Asma'u tace, "wainikam ko wancanne angon? Naga yakafe d'iyar tawa da idanu?".
     Dariya meerah tayi, tace, "gwaggo shine kuwa wlhy".
    Kai masha ALLAH, "ALLAH yabada zaman lfy dai".
     "Ameen ya rabbi gwaggo".
    Duk Aysha najinsu.
           Zungurinsa Sameer yayi, da sauri yamaido kallonsa ga Sameer d'in, yad'an sauke siririyar ajiyar zuciya.
        Sameer yace, " haba alhaji, gidankafa zataje, irin wannan kallo haka?".
       Baki ya khaleel yad'an ta6e, "kai nifa karkamin Sheri, ba kallonta nakeba, kawai tunanin yatafi wani wajene daban".
      "Hhhh j!, J! Ikon ALLAH, Na Aysha bada kanka asare kajegida kace yafad'i, d'ad'ina dakai komai naka akwai tsari, kana tunanin shan angwancine kenan?".
     "Hhmm wlhy Sameer kaima ka canja, yakamata Papa yamaka aure gaskiya".
     Dariya Sameer yasaka, hakan yayi dai-dai da isowar Joseph wajen, j! Zaka shiga motar amaryane? Kozaka tafi daban?.
          "Haba saikace wani kai, mubaha akeyiba, bakagama da y'an uwanta suka shigaba?".
    "Aii nazata zaka zauna agabane?".
    "A'a".
Tom saiku tafi kaida su Sameer  ko?.
       "Nifa karka had'ani da wad'annan, kasan zasu takuramin da surunsune wlhy".
      Dariya sukayi, Sameer yace, ''aikam zamu barka a kano wlhy".

___________
      Kowa yagama shiga, motocin sun wadata alhamdllh, y'an anguwa anata d'agama amarya Aysha hannu, wadda tacusa kanta akan cinyoyinta tana kuka.
   To Aysha ALLAH yabada sa'ar zaman aure.
      
Kunsan miya faru?.
     Harmun fara tafiya saiga gayyar motocin y'an CIKI DA GASKIYA...FANS, group 1,2,3,4, wai daga baya zasu tsaya kada abokan ya khaleel suk'ara irin najiya🤣.
    Ammafa antara matsota😂.

Abuja

       Sun Isa Abuja 2:pm dai-dai, saboda babu laifi sund'anyi gudu, kasancewar harabar gidan akwai mutane motocin suka tsaya ak'ofar gida, ta amaryace kawai tashiga cikin gida.
    Anty Mamie dakanta tazo tafiddo Aysha, Wanda ganin Anty Mamie yasakata kuma rushewa da kuka, lalashinta tashigayi.
       Anma bak'i tarbar mutunci, amma hajia babba da Anty zuwairah ko lek'owa basuyiba, Anty shikurah komai itakam tana aciki, ankai amarya Aysha d'akin Anty Mamie, kafin da daddare amaidata 6angarenta.
       Daga ita sai ifteehal a d'akin, saikuma wasu y'an uwansu su uku, zee da Saleema da Mimi. Hirarsu sukeyi cikin nutsuwa, amma Aysha batacewa uffan, tana kwance kangado tana saurarensu dabinsu da ido.
          Amal takawo musu abinci.
   Sukad'ai sukaci, amma Aysha ko saukama tak'iyi daga gadon Anty Mamie.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now