83

4.7K 314 0
                                    

83

"Kinga nutsu muyi magana mana".

       Cikin kuka tace, "bazan ta6a nutsuwaba ya khaleel, sai mahukuntan k'asarnan sunyi tsawatarwa akan 6arnar dake faruwa ga mata, gidanjen aure bamu tsiraba, kullum mace tana fama da damuwa, idan zaka zauna da mata dubu to wlhy d'ari tara acikinsu dukzasu fad'a maka suna zaman aurene saboda 'ya'yansu, ammafa badan jindad'i agidan aurenba, kullum mace saidai ta karanta tattali da soyayya a cikin novels, shiyyasama wasuma suke ganin zak'ewar writers wajen rubuta yawan tattali da soyayya anovels, sabida su basa gani agidajen aurensu, shiyyasa mata sukafi kowa yawan kallon films, saboda anan kad'ai suke ganin ana sayyaya maiban mamaki, ba'a barmu agidaba, ba'a barmu amakarantaba, lectures da students 'yan uwanmu kullum suna farautar mutuncinmu, sunsan dukkan hanyoyin dad'in baki dazasubi domin janye hankalin yarinya su lalatata, lectures kullum suna kadamu a jarabawa idan mun hanasu kammu, sukan bama wadda tabiya buk'atarsu koda bata cancanci samun wannan makinba, ta wannan hanyar anruguza rayuwar wasunmu bada sonsuba, a offices ba'a barmu ba, kullum manya nasama damu farautar rayuwarmu sukeyi, idan kin bada had'inkai a k'ara miki girma, idan kin bijire a k'ask'antar dake ko'a koreki daga wajen aikinma gaba d'aya. K'ananun makarantu Na primary da secondary nanma mata basu tsiraba, komin k'ank'antarki sai'an samu malamin dazai dinga bibiyar mutuncinki, kan hanya kullum taremu ake ana mana fyad'e, yaranmu da manyanmu, amma koda ankai kotu babu wani Abu da alk'alan sukeyi, k'arshema sai a koro k'arar ace bakuda shaidu, idan kuwa an yanke masa hukuncin to bazai wuce Na shekaru uku ba, kuma harda tara, daya biya taran shikenan sai'a sakeshi ya tsira, itakuma ya haddasa mata bak'incikin dahar tamutu bazata ta6a mantawaba, hakama iyayenta, yanzu kuma abin bak'inciki anmaidamu tumakin ciniki akowacce kasuwa, daidai farashinka daidai aljihunka, dakabiya saika kama, shikenan kasamu dabban tirkawa, kullum kabata dusa domin tattalinta, itakuma yunwa da kwad'ayi yasakata lashewa, ribarka sada ita kazuba kud'in aljihu, kokuma kaita ga mahauta su yanka maka, aimaka filla-fillah da namanta kazo ka soya kanaci ahankali kana nishad'i.
    Haba ya khaleel, shin maza sunmata uwace ta haifesu? Inhar uwa nada daraja a idanunsu baikamata sudunga keta mutuncin sauran mataba, kosun manta sun haifi 'ya'ya matane? Sun manta matane abokan rayuwarsu? Sunmanta Nana Aysha macece? Sun manta Aminatu (mahaifiyyar Manzon ALLAH s,a,w) macacece? Sun manta Nana Maryam macece?, sun manta Nana fad'ima macece?, sun manta Nana khadeejah macece? Sun manta..... Sun manta dayawa?, shin miyasa darajar kimar mata tafad'i awannan zamanin???.
    Mata wannan tanbayar daku nake, kune yadace Ku amsata ba mazaba, domin kune lalacewar kanku, banta6a ganin gidan karuwai Na mazaba, banta6a ganin namijin da suturarsa ta mutunci ta banbanta data banzaba, haba mata, atunaninku shigar banzace wayewa? Atinaninku tallata kankune mutunci?, kwad'ayine da son asani yajefa mata duk cikin wad'anna had'arin Na rayuwa, kuzauna kuyi tunani, kuyi tunanin gyarawa sannan maza suji Shankar keta mutuncinku, kucirema zukatanku kwad'ayi dason burga inhar kunason tsira da muncinku wlhy, idanfa 6era nada sata, daddawafa nada wari, sai bango yatsage k'adandagare kesamun gurin kwana, duk Wanda yakwana lafiya shiyyaso, wani lokacin laifinmu yafi namazan yawa, bazaki ta6a ganewaba saikin nutsu akan kura kuranki..............

        Da sauri yatareta tafad'o jikinsa, saboda juwar datayi hajijiya da ita, ak'asa suka zube, rungumeta yayi dak'au yana shafa bayanta, muryarsa a tausashe yace, "kiyi hak'uri hakanan A'eesha, tabbas da ace mata nada irinki dabasu tsinci kayinsu ahalin dasuke cikiba yanzu, namiki alk'awari insha ALLAH zanyi amfani da aikina wajen kawo gyara, koda ban gyara dukaba zanyi iya bakin gwargwado, nasan baza'a rasa mai irin burinaba dazai d'ora daga inda natsaya, ki kwantarmin da hankalinki, kinga bake kad'ai baceba, banason babyna yafara fuskanta damuwa tun yana ciki kema INA buk'atar lafiyarku kinji.
     Kanta ta jinjina masa, tana cigaba da zirar da hawaye, shikuma yana share mata, saida yaga tadawo cikin 'Yar nutsuwa sannan yad'auketa suka nufi d'akinta, shirin barci sukayi suka kwanta bayan khaleel yamusu addu'a, dukda yana buk'atarta haka ya hak'ura danya kula yau masu rigimarne akusa, shi baima ta6a tunanin haka A'eesha takeba, Ashe itama akwai zuciya, jiyayi k'aunarta nakuma ratsa dukkan sassan jikinsa da 6argo, ya furzar da huci tareda k'ara k'ank'ameta😉💋.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now