66

4.4K 316 1
                                    

66

      Duk sun fita hayyacinsu, dukda bawanima wahala aka basuba, saboda ya khaleel baice komai akansuba tunda aka kawosu wajen.
        Fitulun da aka kunna yasakasu kare idanunsu da hannu, kunsan idan mutum yadad'e acikin duhu yaga haske aii.
    'Daya bayan d'aya ya khaleel kebinsu da kallo, saida yagama nazarinsu baki d'aya sannan yaxauna bisa kujerar da Adams ya ajiye masa, crossing k'afafunsa yayi, tareda hard'e hannayensa a k'irji, fuskarnan d'am-d'am take babu alamar yasan miye dariya.
      Ya d'auke idonsa akansu, cikin murya mai tsoratarwa yace, "wanenen oganku?!".
       Cikin rawar jiki d'aya ya nuna gwaska.
       d'age gira ya khaleel yayi yana kallon gwaska sama da k'asa, " wanene kai? Waya turoka gidana?".
          "Babu". 'Gwaska yafad'a yana wani ciccijewa'.
         "hum d'an samari kafad'a cikin sauk'i kawai, inba hakaba zakayi nadamar yima Ibraheem Abdallah taurinkai, zan maimaita maka sau uku tak, wanene ya turoka gidana?!!".
         Shiru gwaska bai amsaba.
      Ya khaleel yakuma maimaitawa, nanma yay shiru, kafin ya khaleel yafad'i Na ukun Adams yace, ''karufama kanka asiri kafad'a, karka bari yafad'i na uku wlhy, zakayi nadamar dabaka ta6a yin irinsab.......
         Hannu ya khaleel yad'aga ma Adams alamar yayi shiru.....
     Shiru kuwa Adams yayi, ya khaleel yamik'e tsaye yana takawa ahankali, takalmansa na k'ara, saida yagama zagayesu sannan cikin k'araji Yace, "wanene yaturoku gidana nace?!!!!!!!".
      Duk saida suka razana saboda azababbiyar k'arar da khaleel yayi, har bangon d'akin Na amsawa kuwa.
         Har wani acikinsu yad'aga hannu zaiyi magana gwaska ya tsaidashi, cikin sauri yace, "matar babankace".
         Shiru khaleel yayi yana kallonsa, kamar bazaiyi maganaba, saikuma yace, "wace acikinsu?".
         " hajia Bilkeesu ".
     Wani kallon bakada hankali amma ya khaleel yamasa, iska yafurzar daga bakinsa, ya taka k'afar gwaska da k'arfi, har saida tayi k'ara alamar yasamu targad'e ko tsagewar kashi, " inhar baka fad'aminba, haka zantabin ga6o6in jikinka ina karyasu d'aya bayan d'aya, kwanaki ✌🏻 nabaka kacal".
      Yakuma taka k'afar yafice abinsa, gwaska kuma yasaki k'ara yana rik'eda k'afarsa ta dama da ya khaleel yataka.
     Duk tsoro kama sauran  yaransa yayi, lallai yau sunga maza ba mazare ba.
     Kashe fitulun Adams yayi yafice shima da sauri.

_______________________________

           Aysha Na idar da sallar azhur tafito falo, Dan tun tana sallah takejin ana kwad'a sallama.
         Idanu tazaro waje, tareda daka tsalle ta rungume Afrah, ''ALLAH nazata dawasa kikeyifa".
      Dariya Afrah tayi tana rik'e ha6a, "oke Aysha Dama k'alau kike kika zabga k'arya?".
        Kichin Aysha tanufa tana dariya, " kinga ajiye zancen nadawo tukunna".
      "Tom jeki dawo"..
   Ahankali afrah takebin hotunan Aysha Dana ya khaleel dake falon da kallo. Aranta tana jinjina dacewar da ma'auratan biyu sukayi.
    Mintuna k'alilan saiga Ayshan tadawo, ta ajiye tiren hannunta gaban Afrah.
      " humm k'awata bismillah, towai harma kintashi aikine? Naganki yanzu".
        "Inafa, hankalinane yatashi nace baradai nafara ganinki sannan, da k'yarma nasamu Oga yabarni wlhy. Ina angon namu to?".
           "Wlhy yanzunnan yafita, shinema yahanani zuwa aiki saboda yana gida, shiyyasa nayi k'aryar banida lfy fa".
        Dariya Afrah tayi, " a lallai. Soyayya ruwan Zuma, mumafa baradai muyi aurennan".
         "ALLAH ya shiryaki, aigara kuyi musha biki to".
     Nan suka zauna sukasha hirarsu, har bayan la'asar sannan Afrah tatafi. Alkairi mai yawa Aysha tamata kuwa.

___________________________

      Da yamma lik'is hajia babba tadawo gidan, yawancin yaran duk suna babban falo, kowa da uzurin dayakeyi, kamar yanda suka saba suka gaidata.
   Ad'age ta amsa musu da nuna halin ko inkula agaresu.
    Sinrigada sun saba da hakan, shiyyasa babu Wanda yadamu, suka cigaba da harkar gabansu.

       A 6angarenta kuwa Aleeya tazo ta rungumeta, tana mata oyoyo, cikin washe baki hajia babba ke amsawa.
         'Dakinta tanufa danta watsa ruwa, Aleeya kuma takoma ta zauna tsakiyarsu hasnah dake tura mata pictures d'in ya khaleel a system d'inta.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now