87

4.5K 278 1
                                    

87

'Dakin taron tsit yake, da alama khaleel ake jira kawai, Dan kowa ya hallara, kayan hannunsa ya ajiye tareda had'e hannayensa waje d'aya alamar ban hak'uri da Lattin dayayi🙏🏻.
       Duk manyansa ne awajen, shikad'aine k'aramima, kwazonsa da jajircewarsa akan aikice tasakasu shigo dashi cikin meeting d'in, Dan abinda za'a tattauna akai shine jigonsa.
      Bayan bud'e taro da addu'oi suka fara abinda ya tarasu kai tsaye.
     Jawabai sosai akayi, mafi yawa tashafi k'ungiyar su momyne kuma.
     Khaleel aka bama damar tashi yayi jawabi akan nasarorin dasuka samu, dakuma abubuwan da aka kama k'ungiyar dasu.

        Bayan khaleel yayi gaisuwar ban girma agaresu, yayi add'u'oi, sannan yafara jawabi cikin nutsuwa a harshen nasara ingilishi.

        _"munkama mutane 57 dake cikin wannan k'ungiya, tareda bindugu 16, sai hodar ibilis (cocaine) datakai nauyin cg 1800,0 dawani abu, sannan akwai kwayoyi masu had'arin gaske suma masu yawa, saikuma yara 'yammata damuka ku6tar awani gida su 84, wasu acikinsu anyimusu viza za'abar k'asar dasu, akwai kuma 21 damuka samo a wasu k'asashe guda biyu"._
      _har yanzun muna farautar kusan mutane 109 dake k'ashe daban-daban tareda yara kusan kimanin 800 da aka fitadasu tawasu hanyoyi daban-daban ak'asarnan. Akwai uku cikin wad'anda suke hannunmu suna kwance babu lfy acikin asibitinmu, saikuma 26 da suka mutu tawasu dalilai, wasu aciki mune muka harbesu, wasukuma sunmutune kawai, akwai mutum d'aya da aka bashi guba yamutu, Wanda munan muna bincike akan hakan, insha ALLAH kad'an garage mukawo sunayen masu hannu acikin kisan nashi."_
        Saikuma mutun kusan 78 dawasu k'asashe suka samu kamawa 'yan Nigeria, wad'anda aka tabbatar sunada alak'a da k'ungiyar, suma munata k'ok'ari wajen ganin mun kar6osu, andawo dasu nan gida Nigeria ammusu hukunci dai-dai dalaifinsu. Da akwai mutane 13 ahannunmu dasuka fito daga k'ashen k'etare suma, wasu k'ashen suna buk'atar mubasu 'yan k'asarsu domin sumusu hukunci a k'ashensu, to badai muce musu komaiba har yanzu, munanan muna tattaunawa akan batun dai.
     Saikuma jami'an tsaro dasuka fito a fannoni daban-daban guda 11 damuka samu cikin wad'an nan criminals, bincikenmu kuma ya tabbatar akwaima wad'ansu dabasu halarci wannan taronba aranar da'a kamasu, kuma gaskiya acikin manyane, dole saida had'inkan Ku za'a samu Damar kamasun, dukda akwai shirin damukeyi ta k'ark'ashin k'asa akansu.
     Wannan shine bayanan da k'ungiyar tashafa, saikuma wad'anda basuda alak'a da k'ungiyar, muna shirin mik'a wasu kotu.
    Suma d'in zamu shirya kaisu kotu acikin next week insha ALLAH.
       AKWAI mutane uku dake hannun hukuma sss, d'aya d'an k'ungiyarne, biyu kuma laifinsu daban, munason suma subamusu danmu saka d'ayan cikin 'yan uwansa.
        Yak'ame tareda salute Nasu Baki d'aya, sannan yadawo wajen zamansa ya zauna.
      
Gaba d'aya aka d'auki tafi, jikake raff raff raff!!!.

         Lallai dolene hukumar police Interpol tamik'a gagarumin jinjina dayabo akan wannan gwarzon ma'aikaci nata, wannan hukuma da Nigeria harma da duniya  baki d'aya bazasu ta6a mantawa da Ibraheem Abdallah ba, j! gwarzon ma'aikacine dayakamata ayi koyi dashi akowanne fanin d'ammara Na kaki, yakawomana nasarori masu yawan gaske, Wanda bamu kad'aibama duniya gaba d'aya dolene tayi alfahari dashi, yaje k'asashen duniya daban-daban yagudanar da aikinsa cikin nasarori, sannan wasu k'asashen sun gayyacesa domin taimakonsu duk Dan kwazonsane kuma, wannan k'ungiya damuke magana akanta ankai kusan shekaru 16 ana bincike akanta, amma bamu samu wani bakin zareba saida aikin yakoma hannun j!, jinjina agareka Ibraheem Abdallah, ALLAH yacigaba da haskaka rayuwarka kaji, ALLAH yasa ka d'ore ahaka kar watarana ka canja.
    Gaba d'aya aka amsa da ameen.
    Yacigaba da fad'in akwai ganawa da shugaban k'asa daza'ayi gobe a fadarsa, kowanne hukuma taza6i mutane uku dazasu wakilceta, sannan annad'a Wanda zaizama kwamitin shugabancin wannan zama baki d'aya.
    Mudai anan J! Yana ciki, sannan kuma shine shugaban wannan kwamiti gaba d'aya dazai jagoranci wannan zama har fadar shugaban k'asa.
   
Nanma aka d'auki tafi gaba d'aya, kowa yayi na'am da hakan, saidai fuskar mutum biyu babu alamar sun amshi zancen, kuma koda khaleel yake bayani babu alamun jindad'in bayanan nasa, babu Wanda yakula da hakan sai khaleel da hankalinsa ke akan kowa, tunda dama yana zargin wasu manyansu acikin k'ungiyar, akwai guns kusan 6 acikin wad'anda suka kar6a duk Na jami'an tsarone, sannan ankama wasu acikinsu masu kaki.
   
   Haka sukaita tattaunawa, kowa yana kawo albarkacin bakinsa, da hanyoyin dazasubi domin dak'ile ta addacin da'akeyi acikin gida da k'asashen k'etare ana zubarma da Nigeria mutuncinta.
      Har 1:30pm suka kai ad'akin taron sannan aka tashi, amma khaleel yariga kowa fitowa, bama arufe taron dashiba yanemi excuse saboda time d'in sallah yayi, wad'anda suke musilmai awajen sai kunya Takamasu, dansu ko alamar tunawa da za'a shiga time d'in ibadarsu basu nunaba, saima k'ara 6ararrajewa suke suna sakin bayanai.
   Shi dai khaleel yamusu sallam yafito, akan idan basu kammalaba har aka idar da sallah to zai dawo, idankuma sun tashi shikenan.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now