25

3.2K 313 0
                                    

2⃣5⃣

             Indai Dan Maman Hafsat kika dage dak'in yarda da aurenan yakamata ki amince yanzu Maman Aysha, tunda kindaiji itama d'in tagoyi bayan kiyi aurenki.
    Itama kuma inhar ta amince nid'in M. Basher yanada burin aurenta, kuma tasan zancen tunda anfad'a mata, sabodake kuma tace bata aminceba, tunda yanzu kema gashi zakiyi saikuyi hak'uri kawai kiyi. Auren shine mutuncinku, Dan Yaya Abubakar bazai ta6a dawowaba, dolene kuma yaranku saida tsawatawar namiji.
        Mama ta share kwallar data cika mata idanu, nifa kawunsu aurensane bazanyiba kam, dacanma damuke da kuruciya ban zauna da uwargidansa lfy ba bare yanzu, banason yawan fitina gsky..
     
Kafin kawu bilyamin yace wani Abu sunji ana kwala sallama a tsakar gida.
    Fitowa sukayi suduka, saidai ganin manyan hajiyoyin yasakasu tsayawa suna kallonsu da mama ki.
    Itakam mama tunda taga hajia khaltum da hajia Laura ta shaidasu, wanan yasa tamaida kallonta ga kawu bilyamin tana fad'in kagani ko, wanan shine abinda nakeso kugane kaidashi kawunsu.
           Wacece ita?.
Matarsace mana, kanagani tundaga Abuja tawanko k'afa harzuwa Kano sabodani.
        Aii na'isa kenan, hajia babba tafad'a cikin kakkausar murya tana k'arasowa wajen mama, tanunata da yatsa tana fad'in Fad'ima! Kamar yanda gidan mijina yafi k'arfin zamanki abaya, ayanzuma wlhy yafi k'arfinki, duk aure auren Abdullah babu Wanda bataiminba sama dake, saiko waccan bak'ar dagar Bilkeesu, itama kuma gaf nake dayin maganinta, kunhad'a plan keda ita akan ki koma, hhhhhh kunyi kuskure wlhy, Dan baki Isa komawa wanan gidanba kisaka aranki!!!.

   Ke kam wacce irin macece haka?.
    Kawu bilyamin yay maganar wa hajia babba.
       Harara ta ballamasa amma bata tankaba.
    Mama tace, "kawunsu yi shirunka, aii baki yafad'a kuma dolene abashi amsa daidai dashi".
       Hajia Laurah kinyi kuskuren tunanin kin Isa hana fad'ima komawa gidan Abdullahi, kema kinsan wacece fad'ima, kuma haryanzu ina nan yanda kika sanni ban canjaba, adakam kinyi nasanar raboni da gidan Abdullahi, wanan kuma k'addarace darabon haihuwar 'ya'yan da ALLAH bai k'addaro zasu zama nasaba.
      amma kinsan wani Abu kuwa? adakam babu tunanin komawa gidansa ataredani kodaya buk'aci hakan, amma a yanzu kodan Na nunamiki ked'in banza a banzace zankoma.
    Kishirya tarbar fad'ima amatsayin kishiya nanda sati d'aya rak Laurah.
    Kuma kiyi hanzarin barinmmin gida kafin nasaka afiddaki awani yanayi.....
             Hajia khaltum ta hayayyak'o cikin masifa, itakam hajia babba saidai antayama mama kallon banza takeyi.
     Da sauri mama tadakatar da hajia khaltum. A'a 'Yar kore! Tsaya matsayinki, kinsanni ba hak'urine daniba yanzu saina sassa6a miki kamanni. Kama kanki tunkafin asamu matsala, kuma karku bari Na aikata abinda nafad'a muku.
      Mama tai shigewarta d'akinta, su Umma da kawu bilyamin suna take mata baya.
    Aifa su hajia babba sai zabga jaraba akeyi, dacin mutunci wasu mama.
   Babu Wanda yasake kulasu, harsuka kai aya sukabar gidan, hajia baba arikice take da kalaman mama dantasan zata iya aikatawa, wanan kad'anne daga aikin fad'ima, adad'inma bata raga mataba Dan ita bata d'aukar raini.
     Dama ajirgi sukazo, kuma ajirgin suka koma.

Mama kam kaitsaye tasanarma kawu bilyamin ta amince.
   Koda yakira baffah yafad'a masa duk yanda komai yafaru sai baffah yayta farinciki. Shikam zuwan hajia Laurah yamasa rana, badan karya takalo tsiyaba dahar k'yautar kud'i zai mata, ya tabbata badan hakan tafaruba fad'ima bazata ta6a amincewaba, tunda har Ammah da inna sukai mata magana amma tabasu hak'uri.
    Sun tsaida komai, ranar sati kuma za'a d'aura auren😂.

Yeee baffah yaci nasara, is a gold! 💃🏻 is a goooooal!!!, shaku shaku is a goal!  One corner is a goal!!💃🏻💃🏻💃🏻, zamusha bidiri yasin.

Team, baffah & mama😂😂💪🏻.

     *_Bayan sati 1_*

Masha ALLAH an d'aura auren baffah da mama, m. Bashir da Ummah, wanan aure kam yabama mutane dayawa mama ki, amma ansaka albarka sosai aciki.
    Sunce babu wani biki dazasuyi, Umma ma zatayi zamanta ne agidan, mama kuwa sai Abuja.

Agurguje please🤧

           Hajia babba tatada hankalin kowa agidan, wanan yasaka ya khaleel 6acin rai, suna dawowa daga d'aurin auren baffah yad'iba kaya kala uku yay tafiyarsa gidan Taheer.

Kwana uku kuma da d'aura auren mama tatare, sunsha kuka itada Umma, Dan Umma da matan kawu bilyamin ne sukad'ai sukamata rakkiya, sai gwaggo Asma'u da gwaggo Asubi k'anwar mama.
     Sun sami tarbar arzik'i daga wajen Anty Mamie da Ammah, amma hajia babba kam lamarin sai addu'a, umme amarya kam koma ganinta basuyiba.

To mama dai tatare agidan baffah. Saimuce ALLAH yabada zaman lfy.
    
Keda hajia babba kam masu karatu sunci karki raga mata😂🤐.

Masoyan hajia babba amin afuwa🤣🙌🏻.

__________________________
      *_Bayan wani lokaci mai nisan zango_*😬

Abubuwa dayawa sunfaru awanan lokuta dasuka shud'e, masu dad'i damarasa dad'i, Na dariya dana kuka.
     Aciki harda kammala karatun Aysha, tasamu sakamako mai k'yau, yanzunkam inhar tasamu dama zata wuce da karatuntane zuwa high school, (college University) saidai bamuda tabbacin hakan zai iya faruwa kam, Dan bamusan misu Anty glory ke shirya ma rayuwar ayshar ba.
     Har yanzu tana nan da dagiya akan addu'a, tak'ara girma da k'yau, saboda yanayin abinci mai inganta jiki, dakuma canjin muhallin zama.
     Meerah ma dai alhmdllh, matsaloli sunmata sauk'i saboda su Anty glory suna zaton soyayya takeyi da Naufal.
   Itadai batacewa komai, Dan baita6a cewa yana sontaba. Amma suna samun kulawa awajensa itada Aysha, dukda kuma har yanzun baisan komai dangane dasuba. Shi azatonsama tare suke dawani nasu anan k'asar.
       
Tashin hankalinsu yanzukam bai wuce kwanakin aikinsa dasuka taho gangarar k'arewaba, yana shirin komawa Canada.
           Abin nadamun Aysha kam, idan ta tuna ya Naufal zai barsu har kuka takeyi.
    Ita kanta meerah dauriya kawai takeyi amma tana cikin damuwa, gashi takula su Anty glory sunata k'ule-k'ulle akan Aysha, amma tagaza gane namiye?.
    Sosai yanzu Anty glory tamaida hankalinta wajen kula da ayshar da koya mata abubuwa kala-kala, gyaran jiki bata abubuwa Wanda meerah tasan basu dace da ayshar bama gaba d'aya.
    Tarasa ina zata saka kanta danta samu hanyar ku6tar da Aysha, danta d'auki alk'awari bazata ta6a bari su Anty glory su ruguza rayuwar ayshaba kam.

Yau duk suna gida, babu Wanda yakwana a waje, kid'ane ketashi acikin gidan, kowa da harkokin dayakeyi, Aysha dai hankalinta nakan game acikin IPad d'in da Ya Naufal ya saya mata, gaba d'aya Attention d'inta yatafi ga game d'in, sai sakin murmushi takeyi saboda yanda take enjoying d'in game d'in.
          Meerah sai kallonta takeyi cikin tausayawa, kokad'an bata damu da tata rayuwarba, Dan tuni tasan tazama tarihi wajen rugujewa, ta Aysha ce agabanta ayanzu.
     Amma takula kuruciya tasaka Aysha shagala da mance abinda aka kawota yi, kodan saboda kulawar datake samune awajensu?. oho.
        K'arar doorbell yadawo da meerah hankalinta, hakama su Lyn, Happy taje tabud'e, ganin Anty kubra yasakata sakin ihu da rungumeta.
    Suma sauran duk fitowa sukayi Dan ganema idonsu.
      Babu Wanda baiyi murna da ganin Anty kubra ba, sai Aysha da meerah, Dan Aysha tana ganin wadda akema ihun takoma wajen zamanta tacigaba da game d'in ta.
   Garama meerah tayima Anty kubra dariyar hak'ori.
       Yanzuma Anty kubra tare take da 'yanmata biyu wad'anda zasukai 17-18, saikuma k'aramar yarinya dabata wuce 15 ba, zasuyi kai d'aya da Aysha.
       Bak'aramin mama ki Anty kubra tayiba da ganin yanda Aysha takoma, sai ta6ata takeyi tana yabawa. Itadai Aysha batace da ita k'alaba Dan tagama tsanar Anty kubra daduk wani mai irin halayenta, wlhy daza'a bata dama zata iya salwantar da rayuwar Anty kubran.

Kwana biyu dazuwan Anty kubra saiga john yazo, bak'aramin tashin hankali Aysha da meerah suka shigaba awanna karon, Dan basuda tabbacin Aysha zata tsira, tunda dama cayayi bayan ta mammala karatu, kuma tagama kusan 4weeks ma kenan.
     tunda ya iso gidan idonsa nakan Aysha, sai had'iyar yawu da lashe la66a yakeyi saikace tsohon maye, tarema sukazo da abokansa biyu, suma duk turawane.
      Aysha dai tashige d'aki ta 6uya, hankalinta yatashi, sai yau tadawo daga shagalar datatafi Na manta abinda aka kawotayi, gatanda Anty meerah ke bata da ya Naufal ya dulmiyata a mantuwar ko ita wacece?.😭

Shigowar dataji anyi yasakata k'ara sautin kukanta, azatonta anty meerah ce.
        Saidai ta6a kafad'arta dajin muryar  john yana fad'in hii baby, miye matsalarkine??.
    Yasakata d'agowa abirkice, ta watsa masa manyan danunta dake a rikice.
     Jiyayi gaba d'aya tsigar jikinsa yatashi, Aysha ta takaloshi gaba d'aya, yay saurin kai hannu danufin rungumota.
    Zabura tayi zata gudu ya damk'ota tafad'o cinyarsa.
      A'uzubillahi minashshaid'anirrajimm!!!! Aysha tafad'a da k'arfin.
    Yayinda shikuma john yamatseta yana wata dariyar rashin mutunci, danshi baisan mi ayshar ke fad'aba.........✍🏿

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now