77

4.4K 325 1
                                    

77

Yana fita a can baya wani d'aki da doctors kanyi meeting yanufa bisa jagorancin Taheer, dukkan nurse's d'in da doctors anhad'asu awajen, shigarsu babu dad'ewa doctor Faisal ma yashigo.
        "Amma zaka ganeta j!?".
       "Zan iya ganeta insha ALLAH, saidai inbata nan".
      " d'aya bayan d'aya nurse ke tasowa mazansu da matansu, ya khaleel Na kallonsu, amma harsuka k'are babu komai kama da ita, sai wadda tashiga Na farko kawai, danhaka aka tsaidata ita.
        Bayan kammala dubawa babu ita aciki ya khaleel yamaida hankalinsa kan d'ayar nurse d'in, yayi masifar had'e fuska.
     yace, "k wace nurse ce tashiga bayanke? Nasan kin santa?".
        " wlhy yalla6ai ban Santaba, danni inagama dubata nafita kuma duk kuna tsaye, saida nasanarma doctor cewa barci takeyi, amma wlhy bansan wacece takoma d'akinba bayan fitata".
      Ran ya khaleel bak'aramin 6ace yakeba, ya maida hankalinsa akan doctor Faisal. "Doctor tabbas kowacce wadda ta aikata tana cikin ma'aikatan asibitinnan, dan haka nikoma wacece nabada awa 50 kacal anemomin ita".
       Yajuya yafice daga d'akin.
    Kowa da kallo yabishi, tabbas kowa yasan yau ma'aikatan asibitinnan sunshiga tarkon khaleel saidai ALLAH.
    Dayake su Anty Mamie ma duksun ganta, dole saidaisu aka cigaba da duba har masu shara da goge-goge, tunda abune Na laifi, cikinsuma za'a iya samu.
     Khaleel kam yama bar asibitin shida doctors d'insu nawajen aiki, su doctor Abraham, amma saida yakuma saka tsaro mai tsauri azagayen d'akin da Aysha ke kwance sannan suka tafi.
     Gidansu sukaje, su Ammah duk suna harabar gidan, shirin tafiya asibitin sukeyi saiga motarsu khaleel, dakatawa sukayi harya fito.
    Suduka babu wanda bai tsorata da yanayin khaleel ba, har Ammah, Dan sunsan idan yana cikin irin wannan Fushin komaima zai iya faruwa, sannan komin kusancinka dashi bazai d'aga maka k'afaba, kuskure k'ad'an wani zaimasa yaci dukan banza.
    Babu Wanda ya isheshi kallo acikinsu yaja zugarsa suka wuce 6angarensa.
         Afili Ammah tace, " lallai gidannan gab yake da kamawa da wuta, tabbas inaji ajikina akwai gagarumin Abu dazai faru".
       Kowa kallonsa ya maida kanta, amma batasake furta komaiba, kujera tanema ta zauna.
    Suma duk sai suka nemi wajen zaman.

     Su khaleel suna shiga yace, bincike mai k'yau nakeso, Dan tabbas akwai abinda bamu saniba, ajiya A'eesha bataci wani abuba agidannan, kowa ya shaida haka, amma dai ina zuwa.
    Waya yaciro yakira Ammah, babu dad'ewa saigata tazo.
      Suna zazzaune, itama saita nemi waje ta zauna. khaleel yace, "Ammah kamar yanda bincike ya nuna a 6angarenki Aysha take kwana, kuma kinfi kowa Sanin dukkan wani motsi akanta, shin jiya ko taci wani abinci kafin meatpia?".
      Ganin yanda khaleel keyin magana ya tabbatarma Ammah ba fagen wasa ko sanayya akeba, yana fagen aikinsane, danhaka itama taci Serious.
      " tabbas yalla6ai a 6angarena Aysha take, kuma saboda juna biyu datake dashi bakomaine takeciba, wanima idan taci amai takeyi, ajiya bataci wani abuba, idanma ban mantaba da rake ta karya, kuma har kaje kataho da ita bataci wani abuba a 6angarena, ban saniba ko zuwanku anan d'in taci".
         "Anan ma bataci komaiba, koda mukazoma barci tayi, sai around 1 tatashi, meat pia ne kawai nasan ankawo taci, shima gutsura d'aya kacal tamasa, bama ta had'iyaba, ta furzar dashi. Kamar yanda doctor Faisal yace k'arfin gubar yana fara aikine cikin mintuna 20 kacal ajikin Wanda yaci, daga barinmu nan zuwa 6angarenki zaikai minti ashirin kafin A'eesha ta suma. Abinda Yakuma d'aure kammu shine, babu wata guba ajikin meatpia d'in Dana kwashe atsakar d'akinnan, Wanda A'eesha tazubar, kuma acikinsane taci. Wannan shine yarud'ar damu, akan son Sanin mi A'eesha taci?".
      Dr Abraham yace, " sir, inabuk'ar ganin raken datasha".
       Da hannu khaleel ya nunu masa ledar rake da fleet dasuke a falon, Wanda suna nan Inda suka barsu tun a jiya.
      ''Yauwa, kozamu iya ganin inda aka 6arar da meatpia d'in?".
     Nanma Kansa ya jinjina musu, yamik'e suka bishi baya, harda Ammah.
     'Dakimsa da abin yafaru sukaje.
     Tangaran d'in d'aya fashe yana nan, Dan khaleel meatpia d'in kawai yatsince yabar fasashshen kwanon.
       Wata Na'ura suka saka, wasu Na haskawa, Dr Abraham kuma nasaka wani d'an tsinke, kusan mintuna 7 Dr Abraham yace kozamu sami ruwa?".
        Ammah Ce tafita da Sauri, babu dad'ewa saigata tadawo da ruwa.
     K'ar6a Dr Abraham yayi ya yayyafa awajen daduk suke zaton meatpia d'in yazuba,  sannan yasaka wani Abu kamar sirinji yazuk'e ruwan, aka tattara fasashen kwaonon aka zuba a Leda, d'an lallek'awa sukayi kozasuga koda wani guntun meatpia ne ad'akin, amma basu ganiba kuwa, sai can wani acikinsu yatsinto wani d'an mitsit a akusada wardrobe, shima da Alama dije bata Ganshi baneba, dukda dai k'ank'antarsa takai akasa ganinsa musamman idan mutum ba'a cikin nutsuwa yakeba.
     'Daukarsa sukayi suka saka awata Leda aka d'aure..      Yo bandama dai binciken tsiya irinna ma'aikaci  mizasuyi da wannan 6allin abun, saikacefa yaro mai k'yuya yabaka Abu da k'yar😂, gaba d'ayafa baifi Girman wannan gyad'arba👉🏻 (🥔).
     Amma haka suka d'auka Dan zai iya Zame musu wani madubin dubawa.
      Daga Nan fitowa sukayi, raken fleet Dana ledama Duk suka d'auka aka tafi dashi.
       Asibiti suka koma, suma su Ammah asibitin suka tafi.
      Sai lokacin Ammah taji cewar ankuma zuwa har Inda Aysha take kwance anbata gubane.
     Kutt Amman iya bala'i kuma, aikam tashiga zazzaga masifa asibitinnan, catake ALLAH ka tona asirin kowanne tsinanne ke keson kashemin jikata, ALLAH katona asirin matsiyaci.
         Bak'aramar sukan zuciyar Momy adu'ar ammah keyiba, jin Adu'arnan take tamkar tana k'onata da garwashin wutane, Dana tun d'azun arikice take, tarasa hanyar dazata bar asibitin, Dan tafa kula kwa6arsu zatayi ruwa, sotake taje su tattauna plan F, kafin agano yanda Aysha taci guba dakuma wadda aka bata, dije takirata tasanar mata su khaleel sunje gida dawasu doctors kuma taga bincikene Na bin kwakwkwafin tsiya sukeyi, ALLAH ma yasota sanda dije takira wayar tata tasami k'arfin dakewa kamar babu komai ta amsa mata, bama zaka ta6a zargin dawani take wayaba, saboda iyafis dake kunnenta, sauraren dije kawai tayi, amma batace uffanba.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now