11

4.2K 337 4
                                    

11


         Aminiya anya kuwa wannan shawaran naku yayi? Yakamata kubarta taje taga iyayrnta, tunda ansanar dasu karatu zataje.
         Humm Amihiya bazaki ganebane, yarinyar tanada wayo, idan muka bata damar zuwa gida, tofa zata 6allo mana aikine, ninaga kamar tausayi nason canjakifa.
     Bahaka baneba, shikenan nagamsu, yanzu jirginmu zai d'aga nanda 3days.
      daga nan magana hajia babba da hajia kaltum sukeyi k'asa-k'asa wadda banajin komai nikam.

_______________________
       Sosai gidan yake da matakan tsaro, da ido yaringa k'irga zaratan k'artan da aka baza a tsakar gidan kawai, cikin 30seconds yagama nazarinsu, kowanne rik'e yake da makami mai had'arin gaske, jirasuke ace kulle suce Ca's.
       Gyara zaman space d'in idonsa yayi, yad'auki jakarsa yafita amotar.
    Gaba d'aya idon k'attan nan nakansa, cikin takunsa Na bajinta tareda samun cikakken training yak'arasa inda yake k'yautata zaton nanne k'ofar Shiga gidan, ananma akwai k'artai hud'u dasuke sanye cikin bak'ak'en kaya, babu alamar Rahma a fuskokinsu ko kad'an, kowanne kuma yatoshe da bak'in space.
     Kafin ya khaleel yakai ga k'arasawa garesu aka dakatar dashi.
    Wata basarwa yayi tareda huro iska daga bakinsa, yay wata tsayuwar giginya awajen cikeda isarsa.
    Mutum biyune suka k'araso inda yake, bincikensa sukayi sosai, harcikin jakar dake hannunsa, sun tabbatar baya tareda komai sannan suka barshi yashiga.
    d'aya acikinsu yaymasa jagora..
  Babban falone Wanda yak'awatu da kayan alatu masu birgewa, basu tsaya ananba, saida suka wuce falo uku kuma ko'ina da 'yandaba, sannan suka k'arasa ga k'afar wani dogon bene, ananma sunwuce faluka biyu sannan suka Isa fadar Oga David.
     Bak'aramin mamaki abin yabama ya khaleel ba, to wai tayayama d'an iska kamar David yatara yarannan majiya k'arfi haka?....
    Da wannan tunanin aransa suka k'arasa, da wani k'aton mutum suka fara karo, saikuma sauran masu tsaronsa.
     Yana zaune bisa kujera ta alfarma, yayi crossing k'afarsa, agabansa teble ne dake shak'e da kayan giya kala-kala masu tsadar gaske, zamu iya kiransa matashi Dan ashekaru bazai wuce 40-42 ba, daka gansa kaga cikakken inyamuri, farine tas, amma daga gani Na kantine.
    Wani kallo yakebin Khaleel dashi maikama Dana son Sanin kai waye!?, shima dai khaleel kallonsa yake cikeda nazari.
    Cikin muryarsa Mara dad'inji (kunsan dai ibo akwai k'atuwar murya😹)lol, yace young man waye kai?.
      Murmushin gefen baki khaleel yayi, datakumsa Na Isa da k'asaita yak'araso Inda Oga David yake.
   Batareda anbashi izinin zamaba ya juya kujera yazauna.
     Sosai salon ya khaleel yabirge Oga David.
     Ya khaleel daya zauna shima saiyayi crossing k'afarsa kamar yanda Oga David yayi.
     Wata tsawa masu tsaron Oga David sukaima khaleel. Amma amamakinsu ko gezau, saima wani k'asaitaccen murmushi daya sakar musu.
    Hannu Oga David yad'agamusu alamar subarshi, yakalli khaleel dake kad'a k'afa yace, "young man waye kai!?".
      Khaleel ya shafa sajensa tareda zare space d'in idonsa, k'afarsa yasauk'e k'asa, saida yaja 1minute sannan yace, " young tiger!!."
        Wata mahaukaciyar dariya Oga David yakece da ita, saida yayi mai isarsa su khaleel Na kallonsa sannan ya tsagaita, cikin rainin wayo yace really?.
      Ya khaleel yay guntun murmushi, k'afarsa yamaida ya hard'e yana fad'in yes! of course!!.
    Da Sauri masu tsaron Oga David suka nuna khaleel da bindugunsu, sai huci suke ko.
    Oga David Yakuma d'aga musu hannu yana fad'in cool down my boys.
     Duksaida sukai kwafa sannan suka janye bindugunsu.
    Khaleel kam bakinsa yata6e yana k'ara gyara zamansa, sai kara tamke fuska yakeyi.
     Barasa Oga David yad'auka, yazuba haif cup yamik'ama ya khaleel.
   Gira d'aya ya khaleel yad'age sama tareda yimasa alamar thanks.
    Oga David ya k'ank'ance idanu yace miyasa?.
     Murmushi ya khaleel yayi, cikin salonsa yace banashan barasa.
    'Yar dariyar bakada wayo Oga David yayi, sannan yafara shan kayansa, murya a kausashe yace mike tafe dakai wajena?..
     Business!.
  Business nami? Kasanni kasuwancina dayawa.
       Ayya namaka murna David d'an kasuwa, ni nazomaka da business d'in hodar iblis.
       Cikin mamaki Oga David yake kallon ya khaleel, young man waya nuna makani.
      J ya wulk'ita idanunsa yana huro iskar bakinsa, cikin salon yarda dakai _yace, "sunanka David, wasu nakiranka Davido, wasu kuma D-bay, sunanka Na yare Chubuzor, cikakken sunanka chubuzor Obiner, anhaifeka a jihar Enugu state, ak'aramar hukumar Ezeagu local government, awani k'auye Ugwuakulu, dadynka manomin rogo da kwara ne, mom naka tana sana'ar yin manja, Ku uku iyayenku suka Haifa, sauran matane, kayi primary & secondary naka a k'auyenku, daga nan kazo cikin Enugu state a University Ensuka, kana karatunka fannin medicine, bakada k'ok'ari kokad'an, saima k'ungiyar 'yan  coltezing daka bud'e, kuna fashi kuma, rashin k'ok'arinka yasa aka koreka a school._
    _Wannan ya6atama babanka rai yakoreka shima daga gidansa, tundaga wannan lokacin kabar Enugu state kakoma Lagos state kazama rik'ak'k'en d'an fashi da makami, har kwangilar kashe wasu ake Baka, kahad'a gawurtacciyar Daba mai had'arin gaske, kasamu kud'i sosai, kasamu d'aurin gidin wasu k'usoshin gwamnati  kafara safarar miyagun kwayoyi da safarar yara zuwa wasu k'asashe ana bautar dasu, wasukuma suna karuwanci_
    Bak'aramin daskarewa Oga David yayiba azaune, gabad'aya yagama raina Kansas.
    Ya khaleel yay murmushin mugunta yad'age girarsa yana fad'in kagamsu da sanin dana maka yanzun?, 🤨.
   Nibana business sainasan dawa zanyi, saboda tsaro ba tsoroba.

Cikin gadara da isa khaleel yace kokana buk'atar k'arin bayanine?.
   Ayanda yaymaganar saiya fusata Oga David, yawani huro hanci, tareda k'ara kumbura fuska, shima cikin nasa salon namasu ido atsakarka ya bushe da dariya yajuya jajayen idanunsa.
    Tuni j yagano Oga David yanabama yaransa umarnine da idanu, kafin yayi wani yunk'uri sunyi attack nasa da bindugu.
       d'an murmushi khaleel yayi, yaduk'e k'asa tamkar zai gyara takalminsa saiya zaro bindugu har 2, da sauri yad'ago yanuna Oga David da d'aya tareda d'ana kunamar bindigarsa🔫, d'ayar kuma yana nuna yaran, cikin tsawa yace, " wlhy koku sauke bindigunku kokuma Na tarwatsa kansa yanzunnan.
    Cikin Oga David yabada wani k'ululu saboda tsoro, yatabbata khaleel zai iya tarwatsa kannasa,, idanumsa duksun firfito waje, nuni yakema yaransa akan subi ubarnin khaleel.
    Ransu duk a6ace suka sauke bindugun k'asa.
   K'arar harbi naji Wanda yasakani razana, Dan ban lura dawaye yayiba, saida nakai dubana kan khaleel sainaga shine ya harbi wani yaron Oga David dayay yunk'urin harbinsa a kaikaice.
    Wannan harbin shine yajawo hankalinsu taheer dake a waje sunajiran kota kwana, gidan suma suka danno kai.
    Dagananfa akafara musayar wuta, ga isakar hadarin dagarin yahad'a yafara tasowa.
   Al'amura sun tsananta, bakajin komai sai k'arar harbi, Dana wuk'ak'e.
       A cikikam khaleel yana cikin Risky, shikad'ai cikinsu, sauk'insa d'ayama yadamk'e Oga David yayi attack d'insa, suna tsoron Harbin khaleel su sami ogansu, dawannan damar yataso k'eyar Oga David suka fito, ya kulle sauran yaran ad'akin, falonma dai wani yak'inne, karokam iya karo akeyi, nidai inadaga waje cikin tsoro masu karatu🤧😳.

Kimanin 2hours ana Abu d'aya, sannan saigasu khaleel sun fito, dayawansu sunsami raunuka, youseef ma harbi yasamu akafad'a, shikansa khaleel anyankeshi da wuk'a ahannu.
     Ansaka yaran Oga David amota, yawancinsu dukda mugun raunuka, Oga David harbi biyu yasamu, k'afarsa da cinya, sai zabga ihu yakeyi kuwa.
       Anguwar tayi tsit, kowa yana cikin matuk'ar tsoro saboda harbe-harbe daya karad'e anguwar, harsuka kwashesu sukabar anguwar babu Wanda yalek'o waje...........🖊

   Nace matsorata kawai😂.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now