41

3.9K 304 1
                                    

    41  

  
       Fadeela dake bayan Aysha tace, "gwaggo! Dama kece babu lafiya?, ina mama taganoki?.
    Duk atare tajero tambayar.
    Da k'yar Gwaggo bintu take fidda numfashi, da yak'en dole wa Fadeelah, Aysha kam takasa cewa komai, jitake tamkar takashe gwaggo bintu kawai kowa yahuta.
       Wani mugun plashing yashigo wayarta, saikuma sak'o yashigo, samun kanta tayi da ciro wayar daga post d'in hannunta taduba.

      _karki yarda kiyi wani abunda zai nuna gwaggonki tayi wani mugun Abu akanki, hakan tamkar wargaza aikinmune, ki kiyaye, so kisan yanda zaki nuna komai normal tsakaninki da ita saboda sister d'inki, karki 6atamin aiki._

Abinda aka rubuta kenan kuma an 6oye number, Aysha takuma maimaita sak'on a karo Na biyu, cikin mamaki tace wanene wannan?......
     Muryar gwaggo bintu ta tsinkayo tana fad'in Aysha da gaske kece? Kece kika dawo garemu? Tayi maganar tana rushewa da kuka.
     Da sauri Aysha taje ta rungumeta, ta fakaici idanun su fadeelah tafad'a ma gwaggo bintu magana a kunne, _gwaggo kada kiyarda ki nuna wata alamar dazata gane kin saka rayuwata agarari, wlhy inba hakaba sai an  kasheki, kinuna murnar dawowata daga karatu, Dan ALLAH ya juya zalincinku agareni yazama alkairi nayi karatun._.
       Su fadeelah dabasu San abinda ke faruwaba suka Shiga lallashinsu, fadeelah ta janye Aysha daga jikin gwaggo bintu tana bata hak'uri.
     Bak'aramin mutuwa jikin gwaggo bintu yayiba, tabbas maganar Aysha ta shigeta, _(nace karan bana aishi ke maganin zomon bana gwaggo bintu😂)._
      Aysha takoma kusada gwaggo bintu ta zauna, bishirah jitake tamkar cinye Aysha dan murna, suna rik'eda hannun juna, kai Aysha wlhy kin canja, ilimi dad'ine dashi, kamar bakeba wlhy😁.
           Dariya Aysha tayi, wlhy nima duk kin canja mini bishirah, kinzama babbar budurwa, halan kinkusa aure ma?.
    Hhh saura wata 2 ma.
   Eyeee Ashe zamusha biki, ALLAH yasanya alkairi.
   Ameen fadeelah ta amsa.
    Sund'an dad'e a sibitin, amma gwaggo bintu takasa sakin jikinta, sai yanzu nadama da Dana Sani ke k'ara yawa a zuciyarta, taci amanar d'iyar zumunta, gashi wadda tasata aikata hakan y'arta ta azabtar da ita, tunda ta kwanta asibitinnan babu jinin hajia babba ko d'aya daya lek'o dubata, bare ita hajia babban, lallai tayi kuskuren dabatasan tushen gyarashiba, afakaice taketa share hawaye, Wanda Aysha Ce kawai talura dasu.
     Aysha taja bishirah gefe suka zauna.
    Bishirah nikam bayan barina gidannan miya farune?.
    Humm abubuwa dayawa sun faru Aysha, ciki harda Auren da alhaji ya k'ara, tas bishirah takwashe komai tafad'ama Aysha, har zuwan gwaggo bintu Lagos da dawowarta, harda sanadin kwanciyarta a asibitin.
    Aysha tace ALLAH ya kyauta.
    Itama bata 6oyema bishirah komaiba, tabata labarin komai akan abinda yafaru da'ita, kuka sosai bishirah takeyi harda majina, tad'ora mata bayani akan amaryar alhaji mahaifiyartace.
     Bishirah kinsan miyasa na baki labarin sirrina kuwa?.
    A'a saikin fad'a Aysha.
    Saboda ki taimakeni, kuma Dan ALLAH ki rik'emin sirrina, zan d'auki fansa akan hajia babba da sauran mutanen k'ungiyarsu, amma hakan bazai faruwa saina samu wasu sirrika atareda ita.
    To Aysha wane taimaki kikson namikine?.
    Kawo kunnenki.
Aysha tagama fad'ama bishirah abinda nikam banjiba🤷🏽‍♀.
    Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan al'amuran rayuwa dakuma yanda zasu 6ullowa komai kafin auren bishirah.
   Hango fadeelah dake nufosune yasakasu mik'ewa suna dariya.
   Aysha tace yi hak'uri yaya fadeela munbarki ke kad'ai, kinsan andad'e ba'a had'u baneba.
    Batace komaiba sai juyawa tayi sukabi bayanta.
    Koda suka koma basu dad'eba sukamusu sallama, Dan itama gwaggo bintu suna saran sallama yau da daddare.

_____________________________

    K'arar dasukajine tasakasu farga da abinda ke faruwa, da sauri babban yaron Barau modibbo yalek'o, ganin jami'an tsaro yasakashi rikicewa, yunk'urawa yayi danufin guduwa amma sai hakan ya gagareshi, sakamakon harbinsa da Joseph yayi a k'afa.
       Da sauri ya khaleel dake la6e kusadasu yafito shima, saukar harbi yaji a hannunsa Na haggu.
    Da sauri yadafe wajen tareda kallon saitin da'akayo Harbin, barau modibbone, yakuma Harbin ya khaleel a ciki, amma bata shigaba, saboda rigar dake jikinsa mai kare shigar bullet.
    Ganin haka barau modibbo yajuya da sauri zuwa wani d'aki.
      Cikin sassarfa ya khaleel dawasu ma'aikata suka take masa baya, dukda d'an Karen azabar da hannunsa ke masa, ga jini tuni yafara jik'a yellow d'in rigarsa.
    Neman duniya sunrasa inda barau modibbo yake, babu binciken dabasuyiba agidan, amma babu ko alamarsa.
      Basusan ya silale tawata k'ofaba yabar gidan tabaya, dama antanaji k'ofarne saboda irin wannan ranar.
      Saidaga baya ya khaleel yafarga da k'ofar, cikin cije le6ensa yatura Waldrop dake wajen gefe, cikin nazarin k'ofar yace, Taheer inaga yagudu ta Nan.....
    Awahalce yake magana saboda jiri daya fara gani, sakamakon jinin dake zuba a hannunsa.
   Suduka suka k'araso wajen da sauri, wasu fita sukayi, inda k'ofar ta kaisu harcan baya, alamar tashin motarsa suka gani, wannan ya tabbatar musu cewa yagudu.
     Dawowa sukayi inda ya khaleel yake dafeda hannunsa, sai faman lumshe idanu yakeyi.
    Da sauri Adams yak'araso wajensa, sunma manta boss yasamu harbi, youseef ne ya yago bedsheet d'in gadon da hanzari Adams yakar6a ya d'aure hannun ya khaleel Dan tsaida zubar jinin.
    Basu wani 6ata lokaciba sukabar gidan da gawar wad'anda ya khaleel ya kashe, saikuma yaraonsa dasuka kama.
       Dr Abraham sukakira, yace yana General hospital, suyi hak'uri su sameshi a can, Dan sun fad'a masa boss ne yasami harbi.
    Da sari Adams ya amsa da to, Emmanuel muje general hospital.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now