5

5K 362 1
                                    

CIKI DA GASKIYA.......!!
        {🔪wuk'a bata hudashi🗡}

         Bilyn Abdul ce🤙🏻

0⃣5⃣

     A kwana atashi babu wuya wajen ALLAH, yau kwanan Aysha 10 cif agidan Alhaji Abdallah Jigawa.
    A tsawon kwanakinnan ta fiskanci k'alubale da dama, dakuma wasu abubuwa dasuka danganci mutanen gidan, taga abubuwan ban haushi, taga naban mamaki, taga naban dariya, taga Na birgewa, taga Na al'ajabi.
       a6angaren dangantakarta da gidan kuwa tazama cikakkiyar 'yar aiki, Dan kowacce hidima da'ita aciki, saidai abinda batada sani akansa shine, kotanadaga cikin jerin masu albashi? Kokuwa itad'in 'yar tayice kamar yanda gwaggo bintu ta ambata aranar dasuka shigo gidan.
     Babban kuma abinda kecin zuciyarta shine rashin tantance al'ummar gidan da matsayinsu, sunayen k'alilanne aciki tarik'e, suma dantaji ana ambatane.

Yauma kamar kullum sungama tik'ar aikin gyaran gidan, ko'ina yayi fes sai d'aukar ido yakeyi, ga k'amshin tiraren wuta natashi.
    Bishirah data gama dai-daita gudun AC falon takai dubanta ga Aysha, to muje na gama, kinga muma ZAMU huta kafin sudawo su 6ata.
    Murmushin yak'e Aysha tayi da tausayin Kansu, tanamai jin zafin katsewar karatunta da zama haidimar wasu adalilin maraici, dayanzu tana cikin jerin masu Shiga ss1, amma k'addara tadad'e da guntule wannan burin nata, tana rok'on ALLAH daya k'yautata rayuwar sauran 'yan uwanta karsu tsinci Kansu cikin hali irin nata.
    ALLAH yasa iyayen ruk'onsu sucigaba dajan akalar tarbiyyarsu da iliminsu kamar da.
    Dukda tana k'yautatamusu zato, dantasan gwaggo Asma'u da uncle Ahmad bazasu kasance irin gwaggo bintuba, to barema kawu bilyamin dake amsa suna tamkar mahaifinsu.
    Damadai itace batayi dacen uwar rik'oba kafd'insu, shiyyasa kuwa yafi nuna tausayi akanta.......
      Firgigit tadawo hankalinta saboda zingurar da bishirah Tamata.
      Aysha tunanin mikikeyine haka?, yakamata kisaki jikinkifa, ai yanzu kinzama 'yar gida, gakida kwana har goma acikin garin Abuja.
      Ajiyar zuciya Aysha tayi.
    Bishirah tace, "jekiyi wankan saikizo nabaki labarin 'yan gidannan.
      Cikeda d'oki Aysha Tace, " Dan ALLAH da gaske kikeyi?.
    Wlhy kuwa da gaske.
   Da Sauri Aysha tatashi tafad'a wanka, Dan yanzu komai NATA yadawo d'akin bishirah, tsakaninta da gwaggo bintu gaisuwace kawai, Dan bawani janta takeyi ajikiba.

_____________________________
       *_Alhaji Abdallah Jigawa family's_*

           Alhaji Abdallah Rufa'ee jigawa shine cikakken  sunan maigidan, d'an asalin jihar jigawane a garin ringim, ALLAH yayima mahaifinsa Malam Rufa'ee rasuwa dadad'ewa.
   Alhaji Abdallah yana sana'ar saida carpets ne a babbar kasuwar wuse dake Abuja, ahankali ubangiji yacigaba da bud'a masa harkokinsa harya bud'e kamfaninsa na kansa, Wanda yasami had'in guywa da k'asar Turkey, Alhamdullah  kasuwancinsa yabunk'asa matuk'a ak'asar, yanzu haka sunada reshen kamfanin a Kano, Lagos, sokoto, Jigawa.
     Matansa uku da 'ya'ya 21.
    Hajiya Laurah itace uwar gida, wadda sukan kira da hajiya babba, yaran kuma suna cemata (momy). cikakkiyar 'Yar bokoce dantayi karatu mai zurfi, ko kad'an hajiya laurah batason talaka, macece mai tunk'aho da tak'ama, shikansa Alhaji Abdallah nuna masa isarta takeyi, tad'auki aikinta sosai da muhimmanci, kokad'an babu maijin dad'in zama da'ita agidan, saboda halayyarta, musamman hajia Bilkeesu. Yaranta 6, Zuwairah, Shukurah, Ibraheem khaleel, Hameedah, Hasna, Husnah.
    Sai Hajiya Bilkeesu, tanada yara 11, Rufa'ee, ALLAH yamasa rasuwa wata uku dasuka shige sakamakon had'arin mota zaije jigawa. Yanzu akwai 10 Sultan, Mujahedeen, Amatullah, Ramadan, Zunnurain, Muslim, Muhseen, Amal,  Tasleem, UmmuNoor. Itakam tanada hak'uri, ga kawaici da sauk'inkai, kowa natane, batada k'yamar talaka, saima tazauna tayita hira da 'yan aikin gidan, gatada taimako, batayi karatu mai zurfiba, iyakarta Secondary aka aurama Alhaji Abdallah ita, tana yarinya d'anya, kobayan aurensu batacigaba da karatuntaba, danhaka bata aikin komai saina kula da mijinta da 'ya'yanta, wannan yasa suka taso cikin tarbiyya. Alhaji Abdallah nasonta sosai saboda k'yautatawarta agareshi da mahaifiyarsa. Yaran gidan nakiranta (Aunty Mamie).
      Sai amarya hajia saudah, itamadai balaifi akwai girman kai, amma batakai hajiya babba ba, itamadai ma'aikaciyar Ce, Lauya ce maizaman kanta, ita wata irin mutumce dabata damu da damuwar kowaba, cikikam harda 'ya'yanta, (shiyyasa yaranta duk sunfi shak'uwa da Aunty Mamie) takan bama aikinta muhimmanci fiye da komai, kakan dad'ema baka ganta cikin lamuran gidanba, hajiya babba taso suhad'ema hajiya bikeesu kai itada hajia saudah, amma hajia saudah tace ita ba wannane agabantaba. Yaranta 4 Hafeez, Shuhudah, Maleekah, Nurudden. Itakuma suna cemata Ummee Amarya.
    Mahaifiyar Alhaji Abdallah tana nan gidan taredashi, itace tsohuwar dakika gani, anabata kulawa sosai agidannan, babu maison abinda zai ta6ata, idan kika cire hajiya babba da 'ya'yan tokowa jiyake da'ita, ya khaleel ne kawai halinsa ya banbanta ayaran hajiya babba, danshi babu ruwansa.
   Wannan shine tak'aitaccen tarihin gidannan. Kinada tambayane??.

Ajiyar zuciya Aysha tasauke, cikin kafe bishirah da kallo tace, tambayata biyuce zuwa uku. Tafarko suwaye sauran yara uku danagani dakuma 'yanmata biyu?.
       Dariya Bisheerah tad'anyi, cikin tsokana tace Ashe kinfahimci labarin sosai?, 'yan mata biyu dakika gani, Hamdiyya da Naseeba yaran k'anin Alhaji Abdallah ne, uncle Ma'aruff, suma suna nan zaune awajen Aunty Mamie, karatu sukeyi anan sudasu Amal.
   K'anan su uku kam yaran aunty Amatullah ne, 'yan uku, suna k'asar Japan itada mijinta, shine aka kawosu nan gidan saboda school.

Jinjina kai Aysha tayi alamun gamsuwa, tacigaba da fad'in yaran hajiya babba fa? Dan uku nagani yanzu agida?.
     Eh, biyu sunyi aure, Anty zuwairah tana Lego's itada mijinta, sai Anty Shukurah tananan abuja, amma yanzu suna kasar Jordan shekara uku kenan, wai mijin natane yake karo karatu, yaya khaleel kuma bansan takamaimai k'asar dayakeba, Dan shi yanzu zai iya cemikima yana Najeria, anjima kuma kiji yabar k'asar, haka yake yawo k'asashen duniya saboda yanayin aikinsa.
 
    "Aikin mi yakeyi?."

Wlhy ban saniba Aysha, amma naji sunacewa ko d'an sandane, kamardai haka naji su iya hama nafad'a kwanaki. Amma kwanannanma zakiji yazo k'asar saboda hutun k'arshen shekara dakuma meeting na family dasukeyi.
            Shiru Aysha tayi, Dan haka kawai tasamu kanta da fad'uwar gaba, Bishirah ta ta6ata tareda fad'in shikenan kin gama tanbayar taki?.
    Jiki amace Aysha tad'aga mata kanta, kafin Bishirah tace wani Abu kiran da Rabi kemusu yakatseta.
    Atare suka amsamata, sannan suka fito inda take.
    Kichin suka shiga domin tanadar abincin rana, yaran gidan sunkusa fara dawowa, yaukuma aikin hajia saudah ne. Itakam tanama wajen aikinta.
      Duk ranakun aikinsu itada hajiya babba 'yan aikine keyin komai, sa6abanin Anty Mamie dakan tsaya ayi komai da ita, shiyyasa yaran kanyi farincikin aikinta, Dan koba komai zasuci mai dad'i da tsafta...............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin