71

4.9K 327 0
                                    

71

               Da dariya ya isa 6angarensu, yacire kaya yashiga wanka, can k'asan zuciyarsa kuwa tana cikin nishad'i, yayinda gefe guda kuma yake tunani akan matar da taheer ya tabbatar masa tana cikin gidansu, dadai Aleeya zuciyarsa ke zargi, amma idan yatuna da cewar ance kwannanta uku agidan saiyaja tsaki, afili yace, "to wacece wannan?".
     Haka yayta sak'awa da kwancewa harya kammala wankan yafito, gaba d'aya kwakwalwarsa a dagule take, abubuwa biyu sun gitta masa a ranar farin cikinsa, ranar data kasance yadace yayta murmushi har washe garinta.
       K'aramin tsaki yaja, sannan yahaye gado yakwanta danya d'an huta.

____________________

        Farkawar Aysha tasaka ammah saurin isowa gareta, sai sannu take mata, Aysha kuma tana d'aga kai da k'yar, ta yunk'ura zata tashi taji hannunta yamata nauyi, dakatawa tayi tabi hannun da kallo.
    Ammah tace, "karki tashi. Bara nakira iro yazo yacire miki, shima nazata bama zaiyi nisaba aii".
      Aysha dai batacewa Amman komaiba.
          Kiran ya khaleel Ammah tayi, bayan tagano Alamar data sakama number sa da k'yar, harta yanke bai d'aukaba, kunsan dai Ammah babu sauk'i, tacigaba  da doka masa kira babuji babu gani.

        Tun yanajan k'aramin tsaki cikin yanayin barci, harya bud'e idonsa ahankali, sosai kirannan yatakurasa, batareda yaduba wake kiransaba yad'aga yakara akkune, a muryar barci yace, "hallo! Please wanene".
         ''Iro nice, kazo kacirema Jikata wannan ruwan ta farka".
        Da sauri yatashi zaune, ''Ammah kina nufin A'eesha ta farka?".
     "Eh, kana inane?".
" ganinan zuwa".
     Bai jira cewartaba ya yanke wayar, sakkowa yayi daga gadon yashiga bathroom, mintuna kusan 5 yafito.

*******
        Da sallama yashigo, haryanzu Aysha Na kwance Ammah ta hanata tatshi, yak'araso da saurinsa, gaban kujerar ya durkusa saitin fuskar Aysha, idonta Na a lumshe yasaka hannu yana shafa kwantaccen gashin goshinta, ahankali ta bud'e shanyayyun idanunta, wad'anda ciwo yasakasu komawa k'ananu kuma sunyi d'anja.
            Sassanyan murmushi yasakar mata, sannan ya sumbaci goshinta, ta kuma lumshe idanunta tabud'e ahankali bisa fuskarsa.
        "Babiena ya jikin?".
       Cikin mamakin sunan daya kirata dashi, muryarta can k'asa tace, "Alhmdllh."
     " masha ALLAH, bara kiga acire ruwan tunda yak'are" kanta ta jinjina masa kwai.
      Yacire ruwan sannan ya taimaka mata tatashi zaune, daidainan Ammah tafito daga kichin d'aukeda kula k'arama. Sannu itama tama Aysha, sannan tazauna gefenta tana tambayarta ina kemata ciwo yanzu?.
          Aysha tace babu komai, saidai bakinta d'aci.
     "Karki damu shima zai daina watarana?".
        Nanma kanta kawai ta d'agama Ammah.
    Ya khaleel yad'an murza hannunta dake cikin nasa, tajuyo ta kallesa. Gira d'aya yad'age mata, yace, " mizakici yanzu to?".
        Janye idanunta tayi daga kansa, tad'an jingina kanta da gefen hannunsa, Dan zaman yafara gundurarta, cikin dadishewar murya tace, "dama zan samu dafaffen gyad'a".
       Murmushi yayi yace, " saikuma mi?".
     "Shikad'ai ya isheni ya Sadauki".
      Yashafe fuskarta da hannunsa Na haggu, " haba my Sholy kidai fad'i wani abun bayan gyad'an, kinsan bakici komaiba".
      Ta d'ago idanunta tana kallonsa, fuskarta a yamutse tace, nidai gyad'an is OK, idan kuma za'a samu zogale ahad'amin dashi to".
         Ammah dake kallonsu cikeda sha'awa dajin dad'i tace, "Abu mai sauk'ima kuwa, bara ajenan gidansu Ameenu arok'o zogalan tunda sunadashi, barama dakaina zanje aii".
     "Yauwa Ammah jar wuya, shiyyasafa nake yinki akoda yaushe, dolene nasiya miki motafa".
     Baki ammah tawashe. "Lah iro gaske ko wasa?".
         " ahaf aii dagaske nakeyi ammah, amma sai nanda k'arshen shekara idan ALLAH ya kaimu, yanzu abubuwa sunmin yawa".
         "Yo konanda shekara biyune aii zanhak'ura iro, kaidai kawai kacika alk'awari idan munkai daranmu".
      "Insha ALLAH zancika ammah".
       Ammah tafita anata washe hakwara ya khaleel zai saya mata mota.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now