89

3.7K 228 1
                                    

89

Azaba ta ishi Aysha, duk addu'ar datazo bakinta yitake, tana kiran mama da khaleel suzo su taimaketa zata mutu.
   "Wayyo Ammah zan mutu, Dan ALLAH ki ciremin jaririnnan, zai kasheni wayyo Anty Mamie."
         "Daure Aysha kiyi nishi da k'arfi kinji, kinga kan yaro gashinan, insha ALLAH kinayin nishi zai fito ki huta, runga addu'a, bazaki mutuba insha ALLAH".
      " to Ammah, inayin addu'ar aii, hazbinallahu wani'imal wakil, ya khaleel kana ina?, shikenan kabarni da wahala? bama zakazo ka taimakenib......? kai ya salam, I love you mamana.....wayyo ALLAH Na.

       Duk surutannan da Aysha keyi dakiran sunansa khaleel najikin k'ofa yanaji, tausayinta yakuma kamashi, jiyake inama zai iya maido ciwon jikinsa, yanzu nan haka Anty Mamie tasha azabarnan, Amma momy bataji tausayintaba ta d'aukeni batareda ko ganina tayiba, momy kin cutar da Anty Mamie gaskiya, wannan alhakin kad'ai ya isa hanaki zaman lf..........
      Tunaninsa yakatse lokacinda yaji kukan babie yacika d'akin, Ammah kuma tana fad'in kai Alhmdllh sannu da k'ok'ari Aysha, masha ALLAH barka dazuwa duniya.......
        Waigawa yayi yaga Anty Mamie bata wajen, tana kichin d'ora ruwan zafi, ai baiyi wata-wataba yatura k'ofar yashige.
    Ganinsa kawai Ammah tayi yafad'o.
      Shikam ko kallo batama isheshiba yanufi inda Aysha take kwance tana maida numfashin wahala da k'yar.
    Kanta yad'auka yad'ora bisa cinyarsa, yasaka gefen rigarsa yana share mata gumin fuskarta, sai jero mata sannu yakeyi .
    Sannu Humairah na, ALLAH yayi miki albarka, yasaka farinciki arayuwarki, kin faranta min, kema ALLAH ya faranta miki fiye da haka, ya ubangijina bazan daina godemakaba da wannan k'yauta dakamin".
        yaduk'o yasumbaci goshin Aysha, datake guntun murmushi idonta arufe.
         Ammah dai batama kulasuba, tana gama yanke cibi tamaida hankalinta wajen gogema jariri jiki saboda d'a na fad'owa uwa tabiyo baya.
           Muryar Aysha can k'asan mak'oshi tace, ''Sadauki zansha ruwa".
       "Ruwa?, tom inazuwa bara Na d'akko miki".
   Da sauri yafita, batareda Ammah ta kallesaba ta tuntsure dadariyar tsokana, baimasan tanayiba, Dan tuni yafice abinsa ma.

            " a'a babana lfy? Mizaka d'auka? Yama naga jini ajikinka?".
      "Anty Mamie ta haihufa, ruwa tace zatasha shine zan d'auka mata."
         "Alhmdllh Anty Mamie tafad'a cikin d'aga hannu sama, amma khaleel yabata dariya yanda yarikice, badai tayiba ta danne".
      " kaga baruwan sanyi zata shaba, kar6i wannan kakai mata".
   Tamik'o masa ruwa maid'an d'umi.

    Yana zuwa ya iske Ammah ta kulle d'akin, bugun duniya amma tak'i bud'e masa, haushi ya isheshi, hardai Anty Mamie tafito daga kichin tana tambayarsa lafiya?".
     Da hannu ya nuna mata d'akin.
   Murmushi tayi, dantasan shida Ammah ne, tunda sunsaba, "kaga kyale Ammah kaji babana, tashima kacire wannan kayan kayi wanka, kaga duk jini ya6ataka ko?".
     Kallon jikinsa yayi, shi saima yanzu yalura jinin ya6atashi. mik'ewa yayi yashiga d'akinsa, sai jero tsakin haushin Ammah yakeyi, batama barsa yaga koda jaririnba mtsoow, ALLAH tsohuwarnan tagama rainashi.😂

********

  Cikin mintunan dabasufi 30 ba Ammah tagyara maijego da jariri tsaf, d'akinma aka gyarashi, kaikace ba'a haihuba.
    6angarenta taje ta d'akko turaren wuta data tanada domin wannan ranar, matan su Sultan ma duk haka tamusu, harda kayan sanyi Na jarirai masu azabar k'yau.
        Tazo ta kunna, Dan danan 6angaren Aysha yad'auki k'amshi, aka sakama jariri fararen kayannan Na sanyi, sunmasa k'yau, sai barcinsa yake zubawa hankali kwance, bashida wata damuwar data wuce hakan to🤷🏽‍♀.

     Sai a lokacin Anty Mamie takai labari cikin gida.
   Aifa kowa yarud'e da murna, Dan danan suka cika d'akin, jariri d'an dangi, harfad'an wazai d'auka akeyi.
   Suna tsaka da murnarsu ya khaleel yashigo, babuma Wanda yalura dashi, sai Aysha dake kwance akan gado tana kallonsu cikeda jin dad'i.
     Yunk'urawa tayi zata tashi zaune Dan ganin ya khaleel, amma saiya dakatar da ita, tareda zama kusada ita abakin gadon ya kamo hannunta yahad'e danasa.
      "Sholyna sannu da k'ok'ari kinji? babudai inda kemiki ciwo ko?".
      Akunyace ta jinjina masa kan, dansu ummi Amarya suna d'akin, ga matansu ya mujahedeen mamadai batazoba, Anty Mamie ma batadawoba duk sunama ummi amarya kara.
      Yasan sarai mitake jima kunya, amma yak'i sakin hannun.
     Ammah data shigo d'aukeda kofin tea ta balla masa harara, shima hararar tata yayi yana kauda kai.
    " yo iro, iyakarkadai hararar tawa, amma babu yanda ka iya dani, ka harareni son ranka, nasan yanda zanyi maganinka agidannan".
       Shiru yamata, yacigaba dama Aysha magana.
         "Yo karka tankamin d'in, dama masana sunce dogo da hankali dacene, mtsoow".
        
    Shi dariyama takoma bashi, amma saiya k'iyi, ya shareta.
   Kowa ad'akinkam fad'an nasu dariya yake bashi, kowa kuwa yana darawa k'asa-k'asa, Anty Mamie da ummi amarya ne kawai tasu tafito fili.
     Ummi amarya tamik'o masa jaririn tana fad'in kaga bar Ammah kaji babana, sotake kawai tabaka haushi. Ga maigida kamasa addu'a.
      Sai yanzune zai d'auki yaron, bakinsa d'aukeda addu'a yad'aukeshi, wani farinciki yaratsashi, wai wannan nasane, kai 'ya'ya k'yautar ALLAH, ya mannashi da k'irjinsa tareda lumshe manyan idanunsa.
    Ummi amarya dukta kad'a Kansu suka koma falo, akabar Ammah dasu ayshan kawai ad'akin.
       Cikin mamaki Ammah da Aysha suke kallon khaleel dake rungume da yaro yana hawaye, bakinsa yana d'an motsawa ahankali, dagani kasan ALLAH yakema kirari da godiya, yakai tsawon lokaci ahaka sannan yabud'e idanunsa akan yaron, yashiga sumbatarsa kuma.
    Ammah dai da Aysha sunzama 'yan kallo, Dan sun sakin baki sukayi suna kallonsa.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now