56

5.3K 311 0
                                    

56

       Tsorone yafara kamani danjin kamar takun mutane, hhhh yaukam tak'arema bilynku, karfa su kwamishine su zata Ayshan ce😿.
      Addu'a nafara da fatan ALLAH ya fiddo ya khaleel nikam😩.
  

_______________________________

       Su gwaska suka gama zagaye gidan, kowa yatsaya inda yadace, suna hasashen yanda za'ayi sushiga ainahin cikin gidan.

Ya khaleel kam yanacan rungume da Aysha daketa kukan da muryartama bata fita, wani irin tausayinta da k'aunarta Na ratsa dukkan wata ga6a da magudanar jini ta jikinsa, yana godiya ga ALLAH daya masa k'yautar samun mace tagari, wadda tarik'e mutuncinta, takuma kawoshi inda yadace, sosai kukanta ke sukar zuciyarsa, amma yakasa hanata, Dan shima bashida wani k'arfi, ga wani zazza6i dake Neman rufesa.
           Dukda ba lokacin sanyi baneba, amma rawar sanyi yakeyi, yanaso yaja bargo yarufesu amma yakasa hakan, kuma matse Aysha yayi ajikinsa daboda taimako da d'umin jikinta ke bashi.
     Aysha tafara tsagaitawa da kukan datakeyi, saboda jin ya khaleel na rawar sanyi, gawata matsa dayamata ko numfashin kirki batayi, dukda d'akin akwai duhu hakan bai hanata bud'e idanuntaba da k'yar, dansun mata jingim saboda kukan data 6arza, bata ganinsa sosai, d'akin babu fitila dukya kashe, sai hasken fitulun waje dana farin wata dasukad'an hasko glass d'in windows d'in.
       Tana k'ok'arin mik'a hannu ta kunna fitilar gefen gadon kuma aka d'auke wutarma gaba d'aya, yarage asken farin watane kawai.

Hakan yayma su gwaska dad'i sosai, zasu gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali kenan.

      Dukda tayi bala'in wahaltuwa hakan baihanata son tashi danta taimaki ya khaleel d'inba, rawar sanyi yakeyi sosai, har hakwaransa Na had'uwa waje d'aya.
     Kuma matseta yayi, Dan bayason tabar jikinsa.
      Muryarta a dakushe cikin wahaltuwar  tace, "ya khaleel kabari natashi, ko fitila Na kunna".
        " karkibar jikina A'eesha, sanyi nakeji, kedai lullu6emu". 'Yaya maganar cikin dauriya'.
        Bata iya cewa komaiba, Dan itama bawai lafiyar garetaba, da k'yar ta yunk'ura tajawo jargon takuma kullu6esu da k'yau.
         Kamar wasa ya khaleel ya rikice mata sosai, ga jikinsa yayi masifar zafi, sai rawar sanyi kuma yakeyi, ita kanta kamar zazza6in keson kamata, ga azabar zugi da k'asanta keyi, gakuma ya khaleel yahanata koda motsin kirki yamanneta tsam da jikinsa, sai hawayen wahala da tausayin ya khaleel d'in takeyi, tarasa yazatayi.
        Kamar wasa tafara jiyo motsin takun mutum ta bayan windows d'insu, tad'aga ido da k'yar saita hango inuwar mutum.
     Wata irin fad'uwar gaba tasameta, itama sai jikin NATA yafara rawa, ahankali cikin rad'a tace, "ya khaleel kalla mutum jikin window d'inmu".
         Baijitaba saboda muryarta a dasashe take, bata fita da k'yau, takuma matsar da bakinta saitin kunnesa tafad'a masa.
      Dukda halin dayake ciki bai hanashi d'ago kai cikin hanzariba ya kalli window d'in shima, shiru yayi yana nazarin inuwar mutum d'in.
      Aysha zata k'ara magana yay saurin rufe bakinta alamar tayi shiru.
     Shirin kuwa tayi, saidai Duk tsoro ya dabaibayeta.

            Dak'yar ya iya mik'a hannu yad'auki wayarsa dake gefen gadon, komai yanayinsane cikin dabara da taka tsantsan, Yakuma Jan bargon ya lullu6esu sosai sannan yakira number Adams.
      Atak'aice yamasa bayani yakashe wayar.
      Itadai Aysha dukta Shiga damuwa, gani takeyi kafin su Adams d'in suzoma mutanene sunyi yanda zasuyi dasu.
   
Su gwaska kam nacan suna nazarin yanda zasu Shiga gidan, d'aya daga cikinsu yana gwada wani d'an k'arfe a k'ofar falonsu kozai bud'e, cikin ikon ALLAH kuwa k'arfen yabud'e k'ofar falon su Aysha.
     Dad'ine yacikashi, ya dunk'ule hannu yana fad'in yeees!.
      Jin haka Wanda ke a kusadashi yamatso yana tambayarsa tabud'e?, yace Masa eh tabud'e.
    Zagayawa yayi domin sanar dasu gwaska, shikuma d'ayan yashiga cikin falon.
    
               Hankalin Aysha yayi masifar tashi, Dan batasan  dami mutanene sukazoba, amma amamakinta saitaga ya khaleel ta Kansa kawai yakeyi bawai damuwa da mutanenba, Dan haryanzu yana manne da jikinta, data yunk'ura danta tashi zaice please karki barni, sanyi nakeji, Abu goma da ashirin inji Aysha.
        Motsi sukafaraji alamun ana ta6a k'ofar d'akin, amma anjita GAM a kulle, sunata k'ok'arin sakab. k'arfennan dansu bud'e amma sun kasa, saboda key d'in yana ajiki ya khaleel bai zareba.
    A tsorace Aysha tace, "ya khaleel zasu shigofa, Dan ALLAH katashi, wlhy k'ila kashemu zasuyi".
             Tabashi tausayi, amma bashida k'arfin tunkarar kowa awannan yanayin dayake ciki, shikad'ai yasan halin dayake ciki, baita6a tsintar kansa acikin wannan halin ciwonba tunda yay wayo, yasandai yana ciwo, tunda yasha kwanciyama a asibiti, amma baita6a jin mai azaba irin wannanba, gabad'aya ga6o6in jikinsa kwankwatsa sukeyi, ga bala'in sanyin dayakeji.
        Ahankali yace, "ki kwantar da hankalinki gasu Adams nan zuwa, bazasu iya bud'e k'ofarnanba saboda akwai key aciki, kibar kuka".
    ''Ya khaleel idan suka 6allafa?".
         Shiru yayi yakasa bata amsa, ana cikin haka sukajiyo alamar ana dukan Abu, ya khaleel ya sauke ajiyar zuciya, Dan yasan su Adams sun iso, magana suke jiyowa sama-sama.
    Su Adams ne  suke dakama su gwaska tsawa, bayan sun tattaresu waje d'aya,  katafila ne zaimusu gaddama Samuel ya dakesa, shine su Aysha sukajiyo.
        Su Samuel suka tasa k'eyar su gwaska zuwa waje, mamaki yakama Adams ina ogan nasu yashiga haka? Har wawayennan suka shigarmasa gida?, gashi yaji maganarsa kamar a mawuyacin hali d'azun daya kirasa, tomeke faruwane?. wayarsa yad'auka yakirashi.
      Ya khaleel yad'auka murya a dakushe yace, " Adams kunzone?".
     "Ye sir, harma mun kamasu, amma kana inane?".
       Da k'yar yace, " inan ad'aki kwance banida lfy, kuje dasu kawai, saida safe idan naga yanda natashi zan shigo".
     "Oga kodai akira doctor k muje asibiti?, nake ganin baikamata kazauna cikin ciwoba".
    " karka damu kuje, da safe zan kira Dr Abraham".
    Badan Adams yasoba yace, "to shikenan Oga, ALLAH yak'ara afuwa".
     "Ameen". ya khaleel ya amsa yana yanke wayar.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now