69

4.6K 334 0
                                    

69

             Akwana atashi babu wahala awajen ALLAH, kwanaki  nata gudu lamarin tamkar k'yaftawar idanu, kamar wasa saikaga seconds sunkoma minutes, minutes sunkoma hours, hours sunkoma day's, days sunkoma weeks, weeks sunkoma months, months sunkoma years, baka fargaba saikaga kanka amatsayin gawa😭. Da d'an  Adam yana tunawa akwai k'alubalen mutuwa agabansa dabai aikata wata 6arnarba, hummm kunsan wani abu kuwa?, (wlhy dayawanmu gani muke bazamu mut yanzuba, dukda munsan tabbas mutuwa gaskiyace, Dan inba'a d'auki mamankaba, and'auki babanka, ko yayanka, ko k'anwarka, ko mijinki, ko mataraka, ko k'awarki, ko makwafciyarki, amma lokacin da'akayi mutuwarne kawai zakiga hankalinmu yatashi, kwanaki k'alilan zamu koma dukkan ayyukanmu, wani gani yakeyi shifa k'aramine mutuwa bazata d'aukeshiba yanzu),  kai👉🏻🧕🏻👳🏻‍♀d'an adamu wanene kai?, mikake tak'ama dashi?, karinga tunawa mutuwa tana d'aukar d'a acikin uwarsa👉🏻🤰🏻, tana d'aukar jariri a hannun uwarsa👉🏻🤱🏻, tana d'aukar yaro d'an shekara 1👉🏻🙇‍♀tana d'aukar masu shekaru biyu👉🏻👫, tana d'aukar budurwa ko saurayi masuji da tashen lokacin k'uruciya👉🏻🙎🏻‍♂🙍🏻‍♀, tana d'aukar magidanci. Mai fafutukar Kare martabar iyalinsa wajen cigar dasu da tufatar dasu👉🏻👨🏻, tad'auki miji gaban matarsa, 'Yaya gaban iyayensu, uba gaban 'ya'yansa, bazatabar tsohoba komin tsufarsa👉🏻🧔🏼, Duk k'arfin mulkin mai sarauta saita d'auka👉🏻🤴🏻, duk yawan dukiyar attajiri da alfarmarsa saiya tafi, Duk iskancin d'an iska koyakai shaid'an 👹tantiranci wajen bijirema ALLAH sai anshafe tarihinsa watarana.
         Shin miyakaika shagala yakai bawa?, miyasaka mantawa da k'alubalen mutuwa?, miyasa? duniya da kayan cikinta sukafi tasirantuwa azuciyarka fiyeda tunawa kwanciyar kabari daranar hisabi, ranarda kowa aikinsane makaminsa, wane rud'in shaid'anne ke d'awainiya dakai har kakasa jin kunyar ubangijinka daya halicceka danka bauta masa kake aikata zina agabansa, kake shaye-shaye agabansa, kake luwad'i agabansa, kake mad'igo agabansa, kake sata agabansa, kake bin bokaye agabansa, kake cutar da d'an uwanka saboda ALLAH yabaka wata dama ta mulki ko k'arfin iko, miyasa yakai bawa?, shin baka tsoron randa za'a shiryo rundunar mala'iku domin kar6ar ranka?, aranarfa aikinkane kawai guzurinka?, anya kuwa bawa  yana k'iyasta kansa amatsayin gawa idan yanutsu, kokayi wannan tunanin, kobakayiba wlhy billahi saika mutu👉🏻😭.

    

________________________________

         Bikinsu Amal nata matsowa, gaba d'aya yau saura kwanaki 6 kacal d'aurin aure, kusan zan iya cewa duk masu aikin gidan da 'yammata harda matansu sultan dasu mama duk suna kichin, chin-chin d'in gara dakuma rabo akeyi.
     Aysha ce kawai babu awajen, tana d'akin Anty Mamie kwance, yau kusan satinta d'aya kenan, Dan ya khaleel yayi tafiya zuwa France tun last week, shine yace tadawo d'akin Anty Mamie harsai yadawo.
     Kusan kwanakinta uku kenan batajin dad'i, k'irjinta namata ciwo, dauriya kawai takeyi bataso kowa yagane.
     Wajen aikin chin-chin d'inma hartaje takasa zama saboda jiri datake gani kad'an-kad'an.
        Batacewa kowa komaiba tazaro jiki tadawo d'aki, kwance take shiru tana tunanin ya khaleel, tunda yatafi sau hud'u kacal sukayi waya, ko kiransa tayi saiyace aiki yakeyi, lamarin ya khaleel Na damunta wlhy, ita yanda take karanta novels taga mazan ciki Na tattalin matansu, harma sukan manta da ayyukansu, duk motsinsu yana gidansu, soyayya kaga harta fitar hankali, catake haka zata dinga gani ga ya khaleel, amma yayinda ta auresa saitaga sa6anin hakan, dai-dai gwargwado yana nuna mata kulawa da soyayya, saidai batakai ko rabin wadda ake nunama matan novels ba, shin ko ita bata iya tattalin miji baneba kamarsu? To amma ai matan novels ma girki, iya kwalliya, tsafta, kusan shine sukema mazajen, itama duk tanama mijintashi, hardama biyayya, wadda take ganin mafi yawan matan novels basuda ita, (hummm indai hasashenta gaskiya ne to tabbas zata iya cewa irin wannan mahaukaciyar soyayyar da miji kan nuna ga matarsa, harkiga yana mata kuka to sai'a novels, saboda k'arancin samun irin wannan soyayyar a gidajenmu yasaka mata raja'a wajen karanta hikayoyin marubuta, musamman ma buk  na batsa, Dan suna kallon hakan amatsayin soyayya, mukuma yawanci bama samun irin wannan soyayya agidajenmu) "ya ALLAH ka gyara gidajen auranmu", Aysha tafad'a tana share hawaye.
      Wayarta tajawo ta dialing d'in number ya khaleel ta France, harta tsinke bai d'agaba, saida takira sau biyu. Ana uku harta kusa katsewa sannan yad'auka.
         Cikin dauriya tace, "Assalamu alaika".
       Ya amsa yana fad'in "o, nayi laifi fa, jiya nace zan kiraki ban kiraba, amin afuwa aikine wlhy A'eesha".
     Danne zuciyarta tayi tace, " babu komai sadauki, Na fahimceka, ya aikin?".
      Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yakuma jingina sosai da kujerar motar tareda lumshe ido, yace, "Alhmdllh, ngd sosai dakike fahimtata akowane lokaci, haka akeson mace tazama maima mijinta uzuri, Dan itadama rayuwar aure tagaji hak'urine kawai, bakomai ake nema asamu 100% ba".
         Aysha tace, " hakane".
     "Yauwa ya shirin biki?".
    ''Gashinan anatayi, duk sunacanma suna chin-chin".
       "Tofa, kekuma kina ina".
     " ina d'aki kwance, wlhy haka kawai naji inajin d'an jiri, bansan daliliba, amma yanzu yadaina".
         "Sholyna kodai asibiti zakije?".
     " lah karfa ka damu, wlhy da sauk'i, yanzuma zan koma wajen aiki, yaushe zaka dawo".
        "Tom ALLAH yak'ara afuwa, Indai kinji bai tafiba karkiyi shiru, kifad'ama Anty Mamie kuje asibiti, Nima insha ALLAH zuwa nanda 4days zandawo k'asar".
        "anafa jibi d'aurin aure kenan?".
      "Eh, insha ALLAH, ko kina kewatane?".
      Cikin shagwa6a tace, " wlhy sosaima kuwa".
         "Humyim, karfa nadawo kice kuma Na gundureki".
         "ni wlhy babu waninan, kadawo please ".
       Guntun murmushi yasaki, yayinda shagwa6arta ke rura masa wata kasala mai kashe jiki da sanya jini gudu da sauri, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, " my sholy karki kasheni da salonkifa, kinga bana kusadake, please karki saka sadaukinki cikin wani hali kinji".
     Dad'ine Yakama Aysha, tasaki siririyar dariyar data kuma narkar dashi, aii babu shiri ya Yanke wayar gaba d'aya, yay saurin kifa kansa jikin sitiyari yana sauke numfashi a hankali, tabbas Aysha dabance wlhy, yafad'a cikin furzar da iska daga bakinsa, kashe AC d'in mortar yayi, danshima k'ara sakashi kasala yakeyi, dajin buk'atuwar kasancewa da matarsa.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now