79

4.4K 314 4
                                    

79

"Mama da saninki kenan aka kaini karuwanci?".

      Gaba d'aya falon kowa juyowa yayi yana kallonta, Aysha ce tsaye abakin k'ofa, sai Khausar dake rik'e da ita, doctor Abraham kuma yana bayansu, kallo d'aya zaka mata tabaka tausayi, saboda rama datayi, sai uban haske da tsayi, idanu jajur saboda wahala.

       Aleeya Ce tak'arasa garesu da sauri takama hannun Aysha, saman kujera takawota ta zaunar.
    Doctor Abraham kuma yak'araso inda Ammah take, domin bata taimakon gaggawa.
     Da k'yar tayarda aka mata allurar rage rad'ad'i, dantace babu mai mata allurar barci yahanata jin *Sabon al'amaree*, saida baffa dasu taheer sukaita lalla6ata sannan.
    Ya khaleel kam nazaune tamkar wani hoto, shidai binsu kawai yakeyi da rinannun idanunsa, amma ko motsin kirki bayayi.
      Dukda Aysha taji tundaga farkon labarin hakan baihanata tsare mama da kallon tuhumaba, tarasa yadda zata fassara abubuwan.

       Ummi amarya tad'ora dafad'in........
       ............Hakane Aysha, dasaninmu kikaje islands UK, ammafa bada nufin turaki karuwanciba.
      Bayan shigowata gidannan nacigaba dabin diddik'in hajia laura batareda sanintaba, saidai bangane komaiba saboda k'arfin rik'e sirrin k'ungiyarsu dasukeyi, babu wata kafa dasuka bari dawani zai samu shiga al'amuransu.
     Nayi iyayina nagaji.
       Saida Na zauna nayi dogon nazari sannan nagane yakamata ace munsami yarinyar dazataje anufin hajarsu, tawannan hanyarne kawai zamu ringa samun bayanan sirri.
     Nasamu Yaya fad'ima da bintu dawannan batun.
     Tashin farko bintu tace musamo yarinya daga k'auye.
     Yaya fad'ima tace a'a, bazai yuwu mu tsare 'ya'yanmuba mu tozarta nawasu, inhar bazamu iya saka 'ya'yanmu awannan had'arinba, to babu d'an dazamu saka aciki, mudaije musake nazari.
      Mun amince da maganarta kam.
       Kafin muyi zama Na biyu Alhaji yasakani binsa Saudia yin Umrah, Dan lokacin inacikin hutun aiki Na k'arshen shrkarah.
         A Wannan tafiyace ALLAH yahad'ani dawata matashiyar budurwa, masaukinta Na kusada namu, saiyazam kullum tare muke zuwa massalaci. Abinda nalura dashi ga wanan budurwa shine yawan kuka datakeyi dafad'in ALLAH ya canja mata rayuwarta, Dan ba'a son ranta takeyiba.
    Banta6a tambayartaba, sai ana jibi zamukomo gida, nadai kasa hak'uri Na tambayeta, dafarko tayi kamar bazata fad'aminba, saida naita lallashinta sannan takwashe labarinta kaf tasanarmin.
    Na tausayama yarinyar sosai, har hawaye nazubar mata, sannan kuma nayi farincikin jin tanada alak'a da k'ungiya mai tambarin🦂.
      Bayan dawowarmu saudiya muka iske tashin hankalin rasuwar Rufa'i, lokacin kwana d'aya tak, rasuwarnan ta girgiza Yaya Bilkisu da khaleel ainun, hakama dukkan jama'ar gidanan.
        Babu dad'ewa kuma sai mijin Yaya fad'ima ma yarasu.
    Bayan lafawar wad'annan rasuwa mai ta6a zukata nasake dawoma Yaya fad'ima da zancen baya, harma da labarin matashiyar budurwa nan damuka had'u a saudia.
   Lokacin kwanakin mijinta 5 kacal da rasuwa, gaisuwama naje mata.
    Atake anan Yaya fad'ima tacemin muyi amfani da Aysha d'iyarta kawai.
    Wannan magana bak'aramin razanani tayiba, nacema Yaya fad'ima hakan bazai yuwuba, yaza'ayi musaka rayuwar Aysha ahad'ari, tunda bamuda tabbas akan zata iya baro wajennan ba'a 6ata rayuwartaba.
    Bud'ar bakin Yaya fad'ima saitace hakane, kuma tayarda da zancena, amma ita bazata saka rayuwar d'an kowa ahad'ariba, itakuma nata 'ya'yan a killace, ta sadaukar da Aysha danta ceto rayuwar yara masu d'unbin yawa daga gararin rayuwa, inhar rayuwar Aysha ta lalace awajennan tad'auki hakan amatsayin k'addara, amma tana rok'on ALLAH yama tsare mata ita, kodan darajar maraicinta dakuma sadaukarwa datayi amatsayinta Na uwa agareta.
      Hummm Na jinjinama k'ok'rin Yaya fad'ima awannan lokacin, Dan masu irin zuciyarta k'alilanne aduniya, bakowane keda irin wannan k'yak'yk'yawar zuciyarba, kuma duk akan kishiya, wadda mutane dayawa suke d'auka amatsayin abin k'yama, (wlhy hakan datayi yakuma sakama zuciyata salama akan wani Abu waishi kishin banza, tabbas kishin taimakon juna shine kishi, ba kishin hauka Na wannan zamaninba), awannan lokacin naji araina ina addu'ar son dawowar Yaya fad'ima d'akinta Na asali.
      Haka nadawo Abuja cikeda al'ajabin jarumtar mace irin Yaya fad'ima.
       
    Kwanakina biyu da dawowa kacal saiga bintu d'ukeda Aysha kuwa.
    Aysha bata sanniba, saboda duk sanda zanje gidansu saida nik'af nake zuwa, ko Ummah abokiyar zaman Yaya fad'ima bazata ta6a shaida fuskataba bare yaran gidan, bama koyaushe nake zuwa gidanba, saidai Yaya fad'ima tafito muhad'u awani waje.
          Hummm wani al'amarin ubangiji hajia laurah naganin Aysha kuwa saita tanka, dama nasan dawuya hakan bata faruba, saboda Aysha tanada k'yau da tsarin halitta irinta mata, dukda alokacin yarinyace ita k'arama.
        Wannan tankawa datayi kuwa bintu ta sallama mata bisa yanda muka tsara.
     Hajia laurah suka d'auki mak'udan kud'i suka bama bintu, duk Na kar6ar Aysha.
     Dukda yarinyar tana bani tausayi, amma haka muka kauda kai nida bintu aka tafi da ita, da taimakon wata mai dillacin yara muka samu akabama kubrah Aysha kamar yanda muka tsara, ita kuma waccan mai dillacin ba 'Yar k'ungiyar baceba, suna amfani da itane batareda tasaniba, saisu sakata samo yara daga k'auye amatsayin za'a sakasu aikatau, data basu shikenan sai'a rarrabasu k'asashen duniya batareda sanin iyayenauba da ita kanta wannan mata.
             Alhmdllh Aysha taje islands UK, inda matashiyar budurwar nan take, kuma ana kaita ta ganeta, Dan nasanar mata komai akanta ta waya.
      Hummm kuyi hak'uri, bakowa baceba budurwa nan face meerah!!...
   
   Arazane Aysha tamik'e cikin dafe k'irji, tace, "Ummu amarya kina nufin Anty meerah ta?."
   
"Yes lil sholyna haka zancen yake".
          Meerah tafad'a daga k'ofar part d'in Ummu amarya.
     Kowa saida yajuya ya kalli meerah dake takowa cikin falon inda kowa yake.
         " lil sholyna kiyi hak'uri, kuma kimin afuwa, banida za6in d'aya wuce hakan, saboda ceton d'inbin yara mata dake fuskantar mulkin mallaka irinnan k'ungiyar su hajia laurah, wadda akema lak'abi da saunan *('ya'yan kunama)*, tabbas sud'in 'ya'yan kunamane masu amsa sunan 'ya'yan sharri, Dan adalilinsu ALLAH kad'ai yasan yara nawa suka salwanta da matasanmu. Nadad'e ina neman hanyar ku6tar da 'yan uwana, amma babu mai taimakona, sai had'uwata da wanan baiwar ALLAH hajia saudah, itace ta k'arfafamin guywa da yak'inin zamu iya tarwatsa wanan k'ungiya da ire-irenta, amma saida k'arfin addu'a da taimakon juna.
       Aysha shugowarki rayuwata itace mataki nabiyu danagane ubangijina ya amshi addu'ata danakeyi adare darana, akan ALLAH ya canjamin rayuwa, dukda sanadin kwad'ayin mahaufiyata Na tsinci kaina, tabbas kece kika canjani, dukda kasancewarki k'aramar yarinyar akaina.
     Aysha nina shiga nafita nasamu aka sakaki makaranta, saboda ALLAH ya taimakeni john yanuna yana sonki, nasan kuma hakan daga ALLAH ne kawai, (maybi ALLAH yadubi sadaukarwar mahaifiyarkine, kokuma maraicinki, dakuma yawan ibadarki) yacusa soyayyarki a zuciyar john, harya kasa keta miki mutunci aranar daya fara ganinki, bayan kuma hakan baita6a faruwaba, Dan tunda nake banta6a ganin john yad'agama wata yarinyar da'aka kawo k'afaba komin k'ank'antarta kuwa, amma ke sai ubangiji yahanashi cutar dake.
    Nasarar dana samu tasilar abokinsa kika shiga makaranta shine yazama matakin nasararmu tafarko akan k'ok'arin mahaifiyarki da kuma hajia saudah.
     Alhmdllh saikema kika maida hankalinki, gakuma kwazo da ALLAH yabaki.
       Ya Naufal shine mutum na biyu damuka k'ara samun ha6akar nasarori ta silarshi.
    Dukda naso fahimtar kamar akan aiki yake bibiyarmu, amma yata 6oyemin hakan, nima saina tattara Na hak'ura saboda nakasa gano komai.
       ALLAH sarki Aysha aranar da kad'an yarage john ya keta miki mutunci bakiyi mamakin zuwan period d'inkiba?.
      Bata jira amsar ayshaba tacigaba dafad'in, nina baki magani dasafe saboda jininki yazo, nayi hakanne dalilin jin firar glory da kubrah awannan daren, suna labarin washe gari kema john zai d'and'anaki, hankalina yatashi ainun Aysha, adaren ranar saida Na nemo maganinan da k'yar, saboda komai Na turai akwai tsari da k'a'idoji.
       Hankalina yatashi sosai ganin har John yazo gidan banga alamar jininki yazoba, alokacin haka naita kuka, danna sadak'ar john zaici galaba akanmu, amma alhmdllh Shi ubangiji baya barci, kuma yanjin kukan bayinsa da taimakonsu, saiga jininki yazo, Wanda hakanne matakin nasara Na uku, john bai keta haddin mutuncin marainiyar ALLAH ba, wadda tafito daga tsatson uwa mai tsarkakakkiyar zuciya.
      ALLAH gafurun rahimun yabama ya Naufal damar ku6tar damu, bayan Na tattaro mafi yawa daga cikin sirrin k'ungiyar su hajia laurah, batareda yayi la'akari damu suwayeba.
    Mijina ngd sosai akan rawar daka taka arayuwarmu.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now