31

3.6K 328 0
                                    

3⃣1⃣

         Tab lallai yarinyar nan tantiriyace J, kallafa kaga shigar dake jikinta?.
      In banda abinka youseef ba 'yar gata baceba, kowafa yasamu rana yay shanya, aii duk Wanda yasayi rariya yasan zata zubda ruwa.
     Mafi yawancin yaranmu idan anturosu karatu k'asashen k'etare abinda sukeyi kenan, kadubafa ko agida Nigeria yanda jami'oin mu suke, saikayi babbar sa'a zakasamu Na kirki acikinsu, haka zakaga weekend anata kwasar 'yan matan jami'a zuwa d'akunan maza, kaikace gidan karuwaine, iyaye kuma sunacan sun saki baki 'ya'yansu Na karatu a jami'a, wani har k'afafa zakaga yanayi.
    Inhar ak'asarka ana irin wannan 6arnar kuwa, yakake gani lokacin da 'ya'yanmu suka gama samun damar zuwa karatu k'asashen k'etare?.
     Shiyyasa Baffah baita6a yarda yakai d'ansa karatu wata k'asaba, kaf d'inmu agida Nigeria mukayi karatu, saidai wani coast yafiddaka amma bashi yakaikaba.
        Ai wlhy haka yanada k'yau, nifa tsoronma aure nakeyi, aje a haifamaka d'anda zai kaika lahira baka shiryaba.
        Youseef kenan, zakaima ALLAH wayone?, aii ka tabbata yanda kata6a 'ya'yan wasu sai anta6a naka, dama masu iya magana nacewa (wanzami baya son jarfa).
           Youseef zaiyi magana saikuma yayi shiru. Saboda isowar Taheer wajen.
       Ya zauna yana sauke numfashi. Suduka idanunsu akansa, wai miya farune kaketa wani hura hanci kamar kayi noma?.
      Mtsoww kabari kawai j, ALLAH yarinyar can bala'ice, inaga kawai muyi amfani da hanya tabiyu, ita ayanda nalurama bata harka saida turawa.
     Murmushin k'asaita ya khaleel yayi, yagyara tsayuwarsa tareda cin serious, ganin haka ya tabbatarma su Taheer amatsayin ogansu zaiyi magana ba abokiba.
      Mik'ewa sukayi tsaye suma, suka k'ame dama salutes.
        Cikin sanin darajar kai shima yamayar musu murtani, ya kalli agogon dake manne a tsintsiyar hannunsa, sannan yamaida kallonsa ga Taheer, inason magana da headquarter d'inmu nan America.
       OK sir.
Taheer yafad'a da girmamawa.
        A cikin mintuna dabaifi 5 ba Taheer yagama komai, daga nan kai tsaye babban Office d'in shugaban Interpol Na America suka nufa.
      Sungama dukkan shigi da ficinsu, tareda samun had'in guywar 'yan uwansu police interpol na k'asar, insha ALLAH a Daren ranar suka had'a tarkon kama Alhaji Alasan Atiku kwangila..

___________________________
        Baffa ya kalli matan nasa, ransa duk a6ace yake, yace ina Laurah?.
        Kowa tayi shiru batareda sun bashi amsaba, Dan basusan mizasuce dashiba.
    Shima baidamu dajin amsar tasuba, yaciro wayarsa daga aljihu yakira hajia babba, harta yanke bata d'agaba, Yakuma kiranta a karo Na biyu, nanma saida takusan tsinkewa tad'aga tana Jan tsaki.
    Kina INA? Baffah yayi maganar cikin serious.
          Nafita, itama tafad'a adake.
     OK, yamiki k'yau sosai, kuma INA mai tabbatar miki inhar Baki dawoba wlhy saikinyi Dana Sanin fitarki, idan kinji wasa kuma kada kidawo d'in, ya yanke wayarsa kawai.
    Ran hajia babba ya6aci, amma tasan sarai wanene Baffah, baya d'aukar raini koda wasa, duk iskancinta tasan kalar datake masa, amma tanajin shakkarsa sosai.
    Tsawa tadakama driver, wadda tasakashi taka birki cikin hanzari, balbaleshi tayi damasifa akan Yakoma gida.
     Su Kansu su hasnah Lamarin yabasu tsoro.

Afusace tashigo 6angaren baffa, babu Wanda yace da ita k'ala acikinsu umme amarya, baffa kam dama tun d'azu yashige bedroom d'insa.
          Sai surutai hajia babba takeyi, wai anyi munafurcinta, babu Wanda yakulata har baffa yadawo falon.
          Cikin tsare gida yafara musu fad'a, yace, ''kukam wai sai ayaushene? zakusan kun girma, gida cikeda 'ya'yanku da surikai amma bakubar raba abin kunyaba, wlhy inamai gargad'inku akan wannan yazama shine first and last dazaku k'aramin haniya agida, nagaji da iskancinnan hakanan, da girmana kuringa zubarmin da mutunci wajen Matan 'ya'yana da 'yan aikin gida, awannan karon gargad'i namuku, next time idan aka sake mataki zan d'auka akai.
    Daga nan kuma saiya kwantar da murya cikin hikima da dattako irin Na dattijan kwarai yafara musu nasiha, duk kuma sai jikinsu yayi sanyi, har ita hajia babba d'in, suduka hak'uri suka bashi da alk'awarin insha ALLAH baza'a sakeba.
       Yayi farinciki, da fahimtarsa dasukayi, sund'an ta6a hira daga nan ya sallamesu.
     Fitarda hajia babba batayiba kenan aranar.
        Suna fitowa daga ang6aren baffa suka Tatar Zunnurain yadawo da Ammah daga asibiti, dama yakaita taga likitane saboda ciwon k'afarta.
    Duk rissinawa sukayi suka gaisheta, tareda mata sannu.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now