27

3.5K 313 1
                                    

2⃣7⃣

        Cikin rawar baki data jiki meerah tace, umm...um Anty kubra ina kichin ne, sanyi nakeji shine nadafa shayi nad'ansha a can.
    Bata jira cewar Anty kubra ba tafad'a d'aki wuff.
    Haka kawai kubra taji bata yarda da meerah ba, dasauri tamik'e tanufi d'akin nasu.
     Saidai tana shiga ta iske meerah kwance agado tana hawaye.
    Kuka kuma? Waike mike damunkine? Naga wannan karon tunda Nazo duk kinwani canja? Kodai wani yafara tsara miki wani abune?.
     Zaune meerah tatashi, a'a Anty zauna kiji abinda yasakani kuka, wlhy Naufal ne ko! Wai mukai fad'a jiya, shinefa yace wai murabu kawai, nikuma wasu kud'i nakeson tatsa ajikinsa, idanma zamu rabunne saimu rabu, tunda dama kinsan mu rayuwarmu babu doguwar soyayya.
     Dariya Anty kubra tayi, tace, akan wannan kike 6ata ranki, kwantar min da hankalinki, bayau saura kwana 6 birthday d'in John ba? Kuma yace anan k'asar zaiyi celebration?.
    Eh Anty.
To aranar zan koya miki wani salon dazakiyi maganin iskancinsa, ki gayyatoshi kedai.
     Cikin murna meerah ta rungume kubra, kekyace murnar gaskiya takeyi, amma a can cikin ranta fad'i takeyi nima aranar zanbaku mamaki aii. Dan nasan dukkan shirin dakukeyi akan Aysha ranar.
              Bayan fitar kubra ad'akin meerah tad'aga filo tazaro box d'innan, dama tanajin tafiyar Anty kubra tacusashi awajen.
    K'ark'ashin gadomsu tasakashi itama tafad'a wanka cikin farincikin tasamu nasara.
         Bayan tafito tad'auki wayarta tayima ya Naufal text message, tana turawa tatshi tahau d'aukar abubuwansu masu muhimmanci tana shiryawa a k'aramar bag.
    Saida tagama tsince komai tas sanan tad'aukar musu kayan dabasufi seat 5-5 ba suma tasaka awata bag d'in.
    Kafin Aysha tashigo tagama komai tasaka bag d'in cikin wardrobe nasu.
    Koda Aysha tashigo bata Sanar mata komaiba, fira sukad'an ta6a Aysha tayi barci, itakuma tatashi tafita fallo kar a d'auka wani abun suke kullawa.

        Da daddare meerah tashirya tafita club kamar yanda suka saba, Aysha kam barcima tayi kwanciyarta.
        Bayan kowa yagama kwalliyarsa tarashin mutunci yafita, meerah tadawo gidan, dama tunkan tafita saida tad'auki mataki akan CCTV d'in dake falonsu data k'ofar dazaka fita zuwa titi.
     Bag's d'inan tad'auka tafita dasu, ya Naufal dake mota takaimawa, yauwa ya Naufal kaje dasu, sauran bayani kuma saimun zauna, insha ALLAH zakaji komai daya angancemu a wannan karon.
      ALLAH Sarki Naufal sarkin sauk'in kai, murmushi yamata tareda fad'in karki damu, bara nawuce kada wani yadawo cikin 'yanmatan gidan naku.
     OK.
Bayan tafiyar ya Naufal meerah tadawo tad'auki box d'in data d'akko ad'akin Anty glory tamaidashi, danta d'auki abinda takeso aciki.
         Kuma ficewa tayi bayan tamaida CCTV cemara d'in gidan yanda suke cikin dabara batareda samun wani kuskureba.
         Fitarta babu jimawa Anty glory da anty kubra suka dawo sukam, Dan meerah ma taga sanda aka ajiyesu amma tad'an 6uya dankarsu ganta.
    Dukda haka saida Anty glory tace nikam sainaga kamar meerah ta gitta yanzunnan.
    Kai a'a gaskiya glory, kodai kinsha abinda yafi k'arfin kankine? Cewar kubra.
      ALLAH sainaga tamkar itane.
    To ba itabace kuwa, idonkine kemiki gizo kawai.
    Shiru Anty glory tayi tunda batada hujja.
   Duk firar dasukeyi meerah namak'ale tana jinsu, saida taga sunshiga gidan sanan tafita daga Inda take 6oye.
       Kusan atare suka dawo dasauran 'yan gidan, daganan suka Shiga ramuwar barci kuma.

_____________________________
            Tafiya yakeyi cikin Nutsuwa da k'asaitarsa, kaida kagansa kasan kaga jarumin ma'aikaci, su Samuel na take masa baya.
        Inda Oga David yake rufe suka nufa, yaud'inma d'akin dund'um yake da duhu, saida aka kunna fitulu masu hasken tsiya.
    Bak'aramin girgiza nayiba daganin yanda aka maida Oga David, gaba d'aya yafita hayyacinsa, Wanda yasansa ada bazai ta6a shaidashiba ayanzun kam.
        Khaleel ya zauna idonsa akan Oga David d'in, fuskarnan d'am-d'am babu alamar sauk'i, iska ya furzar daga bakinsa, yad'age gira sama, tareda crossing kafafunsa, cikin muryarsa mairazana marajin magana yace, "David Obiner! haryanzu kana kan bakanka ne?".
      Dak'yar David ya iya d'ago kansa, idanunsa suna lumshewa da bud'ewa cikin matuk'ar nuna wahaltuwa, maganarma bafita takeyi dak'yauba, yace young man kona fad'a maka babu abinda zaka iya musu, munada d'aurin gidin manya-manyan jami'an tsaro takowanne fanni, harma acikinku, karkaga kasamu nasara akaina kacigaba da walar da kanka dason kama sauran friend's nawa, nima kuskure aka samu, kuma zanfita, kasaka aranka nakusa fita anan gurin, daga wannan lokacin kuma zan nuna maka k'arfin ikona.
             Murmushi ya khaleel yayi, haryanzu kuma idonsa nakan David, yasauke k'afarsa k'asa yanacigaba da kallonsa, kaikace television yasamu,  bindigarsa yaciro a k'ugunsa yana gogata a gemunsa, haryanzu baice komaiba, kallon dai David d'in yakeyi.
     Su Samuel da youseef ma suna tsaye suna kallon ikon ALLAH, sunsan shirunnan Na J bakomai bane face hasala da zuciyarsa keyi, kuma tabbas yau sai David ya d'an d'anama aya zak'inta..........
    Basuko kai k'arshen tunaninsuba sukaji k'arar bindiga da ihun Oga David alokaci d'aya.
         Babu Wanda hantar cikinsa bata motsaba, amma gogan naku tamkaa bashine yayi harbinba, yawani d'age gira sama yanacigaba da wasa da bindigarsa hankali kwance.
     Saida David yagama ihunsa da murgina-mirginar azabar shigar bullet ajikinsa yakoma fidda numfashi dak'yar ga uwar zufa daketa kwarara tako ina ajikinsa, kaikace wanka yayo, ga k'afarsa da ya khaleel yaharba sai zubda jini takeyi.
          My Sweet Friend! Kashirya fad'ane?.
    Ya khaleel yay maganar yana latsa wayarsa.
     David da azaba ta Isa yace, "bazan fad'aba, amma tunda kace kai jarumin ma'aikacine mai kwazo akan binciken mai laifi mizai hana naga kwazon naka, kana kiran kanka young tiger amma kakoma kare mai dogara ga uban gidansa, mizaisa ka la6e a bayana wajen nuna jarumtarka, inhar kacika tiger kaje daji domin farauto abincinka, hakan shine zai tabbatarmin kaid'in jarumine, amma cigaba daneman bayanai awajena yanasani kallonka amatsayin kare Wanda kullum sai uban gidansa yanemomasa abincin dazaici".
                Saida yama David kallon mintuna 4 sannan yamik'e yana wurwura bindigarsa, baicema kowa k'alaba yabar d'akin.
    David kuma yakece da dariyar mugunta, dukda muryar tasa agalabaice take.
        Bai waigoba, kuma baice kalaba harya fice, cikin hanzari su youseef suka take masa baya.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now