15

4K 294 1
                                    

1⃣5⃣

       Ubangiji ya kar6a addu'ar Aysha hajia babba ta amince suje Kano suwuni Dan da driver ma aka had'asu yakaisu, bak'aramin gargad'i Aysha tasha barazana.
    Haka sukatafi itada gwaggo bintu da yakubu direba. Kasancewar tafiyar asuba sukayi k'arfe 11:24am acikin birnin Kano tamusu, amotama gwaggo bintu nata kwakwkwafar Aysha.
     Ita Aysha ma dariya suke bata wlhy, kokad'anma batadamu da fargabarsuba, damuwarta tafi karkatane da d'okin san ganin mamanta da ummah, saikuma yayunta tunda tasan k'annenta duk basa cikin Kano yanzun.
    Motar natsayawa kojiran yakubu yagama parking batayiba tafice da gudunta tana kwala kiran sunan ummah da mama.
        Ummah Ce kawai a tsakar gida tana tace kullun awara dasuke sonci yau, mama kuma tana bayi, Aysha tadaka tsale tad'ane ummah tana fad'in wayyo ummanah nayi kewarku wllhy.
      Tuni Ummah tasaki abin Tatar tarungume Aysha itama, suduka kukan farinciki sukeyi, mama jin karad'in Aysha yasata fitowa da hanzari.
        Aysha tasaki ummah taje tamak'alk'ale mama, adaidai nan gwaggo bintu tashigo, ganin yanda Aysha tad'ane mama yasaka gwaggo bintu ta6e baki.
        Da k'yar Aysha ta iya sakin mama, su saima yanzu suka lura da gwaggo bintu daketa wani 'yan yatsine-yatsine, sunsaba da halinta shiyyasa suka watsar da lamarinta suka mata tarbar mutunci su.

    Dukda Aysha tana fuskantar wahalhalu agidan Alhaji Abdallah, hakan baihana jikinta murjewaba, tak'ara girma da k'iba, ga hasken fatarta yak'uru sosai Dan Aysha farace tas dama,  yanayin canjin abinci darashin yawo arana saiya k'ara hasken NATA, Aysha doguwace gaskiya dukda dai ba irin shantaleliyarnanba, idan zata tsaya kusadasu ya khaleel dogaye sosaima baza'aga tsawontaba, farace tas kuma k'yak'yk'yawa, tana masifar kama da mama, Aysha batada k'iba, amma k'ila zuwa nangaba idan hankalinta yakwanta tak'ara girma zatad'an k'ara k'iba fiye da yanzun, a6angaren k'yawun fuska kam ba'a magana komai yaji masha ALLAH, tanada manyan idanu da dogon hanci, ga zara-zaran gashin ido masu d'aukar hankali, idan Baka saniba saika rantse tak'arane, kuma natane, idan Aysha tak'ara girma zuwa nangaba dolene akirata sarauniyar mata gaskiya.
     Mama taji dad'in ganin yanda Aysha tayi k'yau, wannan yasaka hankalinta k'ara kwanciya dazaman Aysha gidan Alhaji Abdallah, tasan yanzu hankalin d'iyar tata akwance yake tunda gashi har za'akaita makaranta k'asar waje itada yarangidan. (Nace hummmm kedai mama abar kaza cikin gashinta kawai, su gwaggo bintu sundai tsarakune).

Sai wani dama-dama gwaggo bintu takeyi da Aysha saboda gudun karta fad'i wani Abu, su mama basu kawo komai aransuba, gwarama Fadeela da Hafsat sukam saisukaga kamar Aysha nacikin damuwa, amma gaba d'aya gwaggo bintu tahana Aysha sakewa barema tafad'a, dak'yar gwaggo bintu tayarda Aysha tashiga makwafta ta gaidasu, Duk ida taje sai sha'awar kyawun data k'ara akeyi, itadai batacewa komai saidai dariya, damacan asali Aysha bamai yawan surutu baceba, idan kaga tafiya magana akan Abu tofa takai makurar cutuwa dashi, bayan sallar azuhur suka ajiye uwar tsaraba da hajia babba tayimusu sukai sallama Aysha nakuka suka taho, jitayi kamar kada tadawo Abuja ma, amma tanason tacigaba da ganin ya khaleel koda daga nesane, tunda tafara ganinsa yake bala'in birgeta. (Hummm Aysha miye sirrin🤔?.)
          Sunbiya tagidan kawu bilyamin, suntarar yaran gidan duksun tafi islamiya tahfiz, suma su Aysha sunayi sanda mahaifinsu Nada rai, amma yanzu rashin gata dukya ruguzawa rayuwarta wannan tanajin.
    Aysha bataji dad'in rashin ganin su sadiyaba, tayi kewarsu sosai, amma yazatayi.
    Tunda suka kamo hanyar Abuja takifa kanta da guywa, ahankali taketa rera kuma maiban tausayi da tsuma zuciya.
    5:pm suka iso abuja.

Hummm abinda yabama Aysha mamaki bai wuce  ganin sunnufi wata anguwar dabanba sa6anin maitama.
      Abinda Aysha bata saniba shine bayan tafiyarsu Kano hajia babba tasanar da 'yan gidan cewar Aysha bazata dawoba, wai k'anin mahaifinta yace makaranta zai sakata.
    Lamarin ya Sosa zuciyar aunty Mamie, takumaji haushin gwaggo bintu sosai tunda bata sanar da itama Aysha zataje gidaba, dama tanada k'udirin saka Aysha amakaranta, jiratake hankalin ya khaleel yakwanta tasakashi yasamoma Aysha school mai k'yau, to gakuma abinda yafaru.
    Tunda Aysha tagansu a gidan hajia kaltum jikinta yayi sanyi, lallai tasan yau tafaru ta k'are kam, kukadai tashashi awannan daran, tayi mai isarta tahak'urema ranta.

CIKI DA GASKIYA......!!Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora