18

3.8K 310 1
                                    

1⃣8⃣

            Ido kawai baffa yatsare ya khaleel dashi, yayinda shikuma yayi k'asa dakai k'irjimsa na dukan 100-100 saboda k'aryar daya sambad'ama baffan.
    Shimutumne kaifi d'aya, Wanda baisan 6oye-6oyeba amagana, kaitsaye yakeyinta kuma cikin tsantsar gaskiya. Amma yarasa miya shiga kansa awannan lokacin daya za6i yin k'aryar dankawai yasamu ku6ta da zancen auren da iyayen sanasa sukeson tasashi gaba akansa?, shifa harga ALLAH har yanzu baiga matar dazai kira kalarsabama, ballantana tadace da ra'ayinsa, shikuma bayason auren dabana soyayyaba, gudun sa6awa ubangijinsa wajen k'untata rayuwar yarinyar data Shiga tarkon aurensa........
      Ta6ashin da baffah yayi yasakashi sauke ajiyar zuciya, amma har yanzu yakasa d'ago kai yadubi baffan saboda nauyin maganar data shiga a tsakaninsu, dukda bada fatar Baki yafad'aba arubuce yabama baffan.
     Canai katashi kaje mu'azzam.
    Jinjina kai yayi tareda mik'ewa, har yanzu kansa sinne, gudun karsu had'a ido da baffah.
    Harya fice daga falon baffah nabinsa dakallo, saida ya6acema ganinsa sannan yamaida Kansa ga takardar hannunsa da ya khaleel yabashi, shiru yay yana sake nazarin rubutun.
     Akuma lokacin aunty Mamie tashigo falon da sallama, kasancewar yau aikintane. Kuma tahad'u da ya khaleel d'in ahanyarta tashigowa 6angaren baffah.
      Baffansu miya farune wai?.
    Kansa yad'ago yana kallonta, yad'an muskuta domin bata gurin zama akusadashi kasancewar asaman 2setae yake zaune.
     Kofin dake hannunta tafara ajiyewa akan table d'in dake tsakkiyar falon, sannan tazauna kusada mijin nata.
      Ina saurarenka, abinda tafad'a kenan tana dubansa.
     d'anyatsansa d'aya yasa yana Sosa gefen bakinsa, ya ce, "humm wai maganar aure nasake yima mu'azzam, kasancewar naga Sultan & Mujahedeen sun tsaida Matan aure, to amma shine yabani wannan takardar. "Yay maganar yana bata takardar hannunsa".
        A'a baffansu fad'amin kawai abinda takardar tak'unsa, Dan mawuyacine nafahimci abinda aka rubuta, kasancewar ilimin nawa bamai zurfi baneba.
     Baice komaiba yafara mata bayani.
     _takardar tana k'unshene da bayanan likita akan wai mu'azzam d'in bashi da lafiyar dazai ajiye mata yanzu, Yakuma kai tsawon shekaru biyu da Sanin matsalar, kuma sun d'orashi akan magani dazaisha natsawon shekara biyar._
           Kasa magana aunty tayi, shiru yaratsa falon, kowanne da irin tunanin dayakeyi tsakanin baffah da aunty Mamie.
    Zuwa can aunty Mamie tanisa, muryarta a sanyaye tace, "ALLAH to yabashi lafiya. Amma azumin mi yake yawanyi? Kuma basai alhamis da litininba?.
        Kallonta baffah yakeyi cike da nazarin maganarta, yace, " Bilkeesu Kodai Mu'azzam hanyar gujema aure yakeyi? Saboda wani Abu dayake aikatawa bamu saniba?.
   Lamarinsa yafara damuna, anya kuwa yaronnan baya Neman mata?, tsawonfa shekara 2 kenan INA fama dashi akan aure amma yana kawomin k'auli da ba'adi, ada tunani nake saboda aikinsane, amma yanzu nafara zarginsa da aikata wani Abu, shekarunsa sunkai yaso ajiye iyali dakansa, amma yaronnan sai yawo da hankali yakemin. Kullum Ammah nad'oramin laifin saka MASA idanu.
   Nayima mahaifiyarsa magana tanuna halin ko inkula dabatun.
    Kayi hak'uri baffansu, badamuwa yakamata kayiba ko fushi, mucigaba damasa addu'a koma wane hali yake Ciki, kuma Dan ALLAH kadaina zarginsa da aikata Neman mata, kawai nidai abinda nafahimta ga babana yakasa tsaida hankalinsa waje d'ayane yasamu matar aure.
    Kasandai miskilancinsa aii.
         Shiru baffah yayi yana nazarin maganar ta aunty Mamie da gaskatata. Yasauke ajiyar zuciya dafad'in to ALLAH ya k'yauta.
    Yacemin gobe idan ALLAH yakaimu zaije Indonesia.
 
Eh Nima yafad'amin jiya, ALLAH yatsare dai yakaremanashi da sauran 'yan uwansa daga Sharrin rud'in zamani aduk Inda suka tsinci Kansu.
                 To amin baffansu, zo6on tazuba MASA tabashi.
   Yakar6a yana murmushi da kashe mata idanu.
   Murmushinsu Na manya tayi tace, "kai baffansu kafa girma".
    Siririyar dariya yasaki yana rungumota dafad'in aini bana tsufa wajen my bilyna, kokin manta sunan namune? *(Bilyn Abdull)*🤣
    Dariya tayi tana sinne kanta ajikinshi, hakane kuma mijina uban 'ya'yana, saidaifa naga wata harta kwaykwayemu🤕.
     Kai haba da gaske?.
   ALLAH kuwa, writer ce wai ita Bilyn Abdull.
     Barta dear na, aidai tasamu gwanjon mune ko?😉.
    Hakane kuma tafad'a tana k'ank'ame dattijon mijinta, Wanda har yanzu kwarjini da kamalarsa natare dashi, uwa uba k'yawu d'an asali, da dukkan yaransa suka gado agareshi.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now