8

4.3K 324 1
                                    

⃣8⃣

      Tana zaune tana dama fura yay sallama, daga ita sai Tasleem da maleeka, tana ganinsa ta washe hak'ora da fad'in a'a lale da mai gidana.
    Zama yay kujerar gefenta shima yana murmuahi, Ammah tsohuwa mikikema jagwalgwalo haka da hannu?.
    Furace nake damawa, zakawanice jagwalgwalo kajimin d'an kwal uba kai.
      Dariya su Tasleen sukayi sannan suka gaidashi, Ammah datagama kammala dama furarta tace ke maleeka d'akko kofi nasama yayanku fura, kuma kud'iba dannasan wannan hirar badan ALLAH akazominba.
     Kai Ammah hakama zakice?.
   Eh mana ai gsky ce. dan gidanku da hakananne daba yanzu kuntafi gun iyayenkuba kuna k'aryar saboda kada Ku makara makaranta.
         Shikenan Ammah zamu dena zuwa miki hira aii ko.
    Yo kada kuzo mana, aii Bilkeesu tazo itada babanku.
       Ya khaleel dai yana saurarensu amma yay shiru.
   Bayan maleeka takawo kofuna Ammah ta zuba musu suka d'auka suka fita, Dan sunsan halin ya khaleel ba'a had'a inuwa dashi.
     Ammah takalli Khaleel tace kaifa saraki nazuba?.
    no Ammah, ni nasha shayi yanzun, kinsan bancika ammafani da Abu mai sanyiba aii.
   Baki tata6e tana fad'in aikaikam matarka tabani da iyayinka billahillazi, daga kace Baka cin wannan, saikace baka son wannan, mutum saikace goyon junnu.
        Lallaima Ammah, idanma nid'in goyon junnu ne ai hardake ciki, tunda taredake aka raineni.
      A'a A'a saidai iyayenka, badai ka gado Bilkeesu ba itada kasha nononta, Dan ita batada wannan fad'in ran naka, mutum kullum fuska ahad'e, shiyyasama sukayi saurin d'aukarka aikin d'an sanda alokaci, sukazo kuma suka had'aka da wannan aikin namarasa kirki.
     Dariya yayi awannan karon, kai AMMAH aikin nawane namarasa kirki?.
    Eh mana, bagashinan yahanaka aureba, kullum shekaru kesake zuwa maka amma kak'i kagane, ga hallidu nan da aka haifeku lokaci d'aya yanada yara 5, yanzu haka babbar 'yarsa nanda kaka za'a iya mata aure wlhy.
    Bakinsa yad'an ta6e yace Ammah aure lokacine, idan nawa yazo aizanyi, nifa har yanzu banga yarinyar dataminba, kumani nafison auren k'aramar yarinya ma, irin 'yar 17-18-20 d'in nan.
       Ahakan ne zaka auri yarinya, anya kuwa kana kallon kanka amadubi iro?, wane sakaren ubane zai d'auki 'yarsa k'arama ya aurama k'aton gardi kamarka.
    Dariya tabashi sosai datace k'aton gardi, saida yadara son ransa sannan yace kai ammah, ammafa kinmin wulak'anci, yanzunan nine k'aton gardin?, bakomai zan rama aii.
     Yo iro, nifa gasky make fad'a maka, yakamata kanemo matar aure hakanan, idanfa bakayiba su Sultan bazasuyi tunanin yiba, dama marigayine ked'an nuna alamar kamar zaiyi, tokuma sai mutuwa tad'auka manashi.
       Cije le6e Khaleel yayi, muryarsa a sark'e yace ALLAH ya gafarta masa.
   Amma tace amin.
 
Mik'ewa yayi yana fad'in Ammah bara naje mugaisa da momy itama, saida safe.
     To ALLAH ya tashemu lfy maigida, ALLAH ya kawo kishiya tagari.
          Fitayay yana guntun murmushi.
   Ammah tabishi da kallon tausayi, tasan maganar marigayi Rufa'ee datayice ta Sosa MASA zuciya, to amma yazasuyi da hukuncin ALLAH, saidai hak'uri aii.

Da sallama yashiga falon momy.
      Aunty Zuwairah dasu mufeela duk suna falon, momyce kawai babu.
     Fuskarsa ahad'e yace Aunty zuwairah bakiyi barciba?.
   Banyiba khaleel, amma kaikam ina kamak'ale hakane? tundazunfa momy ta aika Mufeeda kiranka.
         Um naje gaida jama'ar gidanne, Dan bamu gaisa dakowaba.
        Aunty Zuwairah ta ta6e bakinta, humm aini babu macen data isa nabita har d'akinta gaisheta wlhy.
   Banza yamata bai tankaba, Hasnah tace, ''yo ALLAH natuba aunty bama keba koni k'arama basu isaba wl.....
       Hararar da ya khaleel ya balla mata tasakata yin shiru, k'ofar d'akinsu yanuna musu da hannu, alamar sutashi subar falon.
    Sanin halinsa yasakasu tashi sunata zum6ura baki.
   Adaidai nankuma momy tafito daga d'akinta itada gwaggo bintu wadda tayo sharkaf da zufa, kaikace k'arya tayi aka turketa acan.
         Wani kallon tuhuma khaleel kebinsu dashi, daga momy har gwaggo bintu.
      Ganin kallon dayake musu yasaka momy had'e fuskarta, tace saiyanzu kagadamar zuwa Ibrahim?.
      Batareda yabata amsaba yazamo daga kujerar yana gaisheta.
    Saida tazauna sannan ta amsa masa, takumacewa ko sak'ona bai iso makabane sai yanzu?.
    Ya iso momy.
Uyum rainine yahanaka zuwa tun d'azun?.
    Nanma shiru yayi.
Tasan halin muskilancinsa, danhaka tad'akko wata maganar.
    Mi yarinyarnan keyi ad'akinka?.
    Ayanzunkam kansa yad'ago yakalli mahaifiyar tasa, momy yarinya kuma? wace kenan?.
      Saida tayi kwafa sannan tace yanzuma rainamin hankalin zakayi kenan? Ko mufeeda bata tadda yarinyar nan Aysha a d'akinkaba? wlhy Ibraheem inad'aga maka k'afa fa akan lamarin gidannan, amma wlhy kakusa kakaini bango, kaiwai bakasan ciwon kanka baneba? baka kishina amatsayina Na mahaifiyarka?.
       Please mom, nikam kidaina sakani awannan aikin naku, shiyyasafa wlhy banason zaman gidannan sai dole, nibanga laifin matan gidannanba, iya gwargwadon iko suna gimamaki amatsayin matar Baffa babba, why not kema kikwantar da hankalinki azauna lfy, yanzu kodansu Mujahedeen ba'a ragama Aunty Mamie ba? hakama umme, itabama sabgar gidannan take shigabafa, wlhy ko kad'an banason k'ananun magana arayuwana, Dan ALLAH Momy kiyi hak'uri adaina sakani ciki nidai, kuma ku dinga hak'ur.......
     To Ubana cigaba Damin fad'an to.
     No mom niban Isa miki fad'aba, kawai inaso agyarane.
    To bazan gyaraba, nace bazan gyaraba, nitashi kafitamin, wlhy Ibraheem ka kiyayi randa zanmaka bankad'a agidannan, shashashan yaro kawai lusari, ainasan tuni Bilkeesu tagama shanyeminkai tun kana yaro, aini k'addara tajamin wlhy, kuma babu Wanda yajamin masifar nan sai Ammah, Dan dabata k'arrafa Bilkeesu tashayarmin dakaiba da bantsinci kaina awannan jarabarba, inaji INA gani d'ana yafison kishiyata akaina, abin bak'incikinma kai kad'ai tillo gareni namiji, amma ka KASA sharemin hawayena, saisu zuwairah dasuke mata.

   ALLAH ya huci zuciyarki momy, nidai gaskiya nake fad'a miki, masu iya magana  sukance *CIKI DA GASKIYA... WUK'A BATA HUDASHI* Inzaka fad'i fad'i gaskiya, komai taka jamaka kabiy.....

    Kai tashi kafita!!.
 
girgiza kai khaleel yayi kawai sannan yamik'e.
   Aunty Zuwairah tace kai amma kaji haushin kanka Khaleel.
     ta gefenta yara6a yafice abinsa batareda yakalli ko inda takeba.
      Aunty Zuwairah tarik'e ha6a tanabinsa da kallon mamaki, 6acewarsa tasata dawo da kallonta kan momy, anya momy ba aimiki musayar khaleel a asibitiba kuwa? yaronnan yana Abu saikace ba jininkine ke yawo ajikinsaba?.
        Momy tace, "K! Bansan shirme" kada kik'ara 6atan rai kuma, wannan wace iriyar maganace.
     A'a momy yihak'uri...........🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now