57

5.2K 365 0
                                    

    57

       Ammah Na kacire saman kujera doguwa ta kurama TV data kunna idanu, kaikace tanajin yaren da'akeyi, tanason canzawa amma tarasa yanda zatayi, kunnan tvn dai ta iya.
       Daga momy har Anty zuwairah babu Wanda yalura da Ammah, itakam tun shigowarsu idanunta Na Kansu, k'iyarsata yanda zataci mutuncin momy azuciyarta kawai takeyi.
      Momy daketa harare-harare da hura hanci tafara kwalama ya khaleel kira. "Ibrahim! Ibrahim!! Kobaka jinane?".
        "yaza'ayi yajiki? Bayan yanacikin halin ciwo Laure!".
        Afirgice suka juyo suduka suna kallon Ammah, Anty shukurah dake k'ofar d'aki tsaye tayi murmushin jin dad'in ganin Ammah, shiru momy tayi takauda kanta daga kallon Ammah, zuciyarta sai suya da zugi takeyi.
     Anty zuwaitah ce tasamu k'arfin halin Jan k'aramin tsaki, tana ta6e fuska.
    Ammah tace, "kinyiwa Abdillahi da Laure, mara mutunci fitsararriya, mai girman kwabo kawai, 'Yar banza magajiyar uwarta".
         "nidai badai uwataba ehe".
       Tassssss!! Kakeji afuskar Anty zuwairah, gaba d'ayansu suka waigo dansan ganin Wanda yay marin, bakowa baneba face baffah da Anty shukurah takira awaya tasanar masa gasu momy can suntafi 6angaren khaleel. 
      Dafe kunci Anty zuwairah tayi, tunda ta girma tayi hankali baffah baita6a ko dungurintaba, amma yau harda mari? Da girmanta, ga zagada-zagadan 'ya'ya.
     Momy kam baki bud'e take kallon baffah, tama rasa abin fad'a.
     Ammah tataso tana tafa hannaye, ''kayimin dai-dai, kuma tabbas nahaifi d'an halak, kekuma kince badai uwarkiba?, to saitawa kenan?".
      Cikin zubda hawaye Anty zuwairah tace, "nidai aii ban fad'aba ko".
         Ammah zata sake magana baffah yace, ''kiyi hak'uri Ammah Dan girman ALLAH, basai kincigaba da 6ata rankiba akan rashin tarbiyya irin ta wannan mara mutuncin da uwarta ba, namuku biyayya Na auri Laure badan inason halayentaba, ayanzukam ina rok'on alfarma agareki, abisa madadin baba zan saki Laure yanzunnan, saboda halayenta sun isheni, banajin dad'inta, banajin dad'in 'ya'yanta sai shukurah da mu'azzam kawai, dan ALLAH Ammah kibari nasaketa kawai".
         " humm bazaka saketaba Abdullahi, saboda wasu dalilaina, munhad'a aurenka da ita saboda darajar zumincin dake tsakanina da jummai mahaifiyarta, sannan kuma akwai 'ya'ya tsakaninku yanzu, to taci darajar y'ay'an dakuka haifa, d'ayan sirrin kuma nabarma zuciyata, dan haka kabarta duniyace zata koyar da ita hankali kwanannan".
          Wani irin kallon momy take bin Ammah dashi, maid'aukeda abubuwa da dama, tsoro, tsana, k'iyayya, k'yama, hasala, bak'inciki, wai agaban 'ya'yanta wannan tsohuwar take cin zarafinta itada d'anta, lokaci yayi dazata d'auki mataki akan baffah da uwarsa, batareda tace komaiba tajuya afusace tabar falon.
       Anty zuwairah ma baya ta take mata.
    Baffah ya dakatar da ita, "kije yanzun ki tattara kayan 'ya'yanki da naki kibarmin gida Dan ubanki, kuma wlhy karna sake ganin k'afarki agidannan Harnan da shekaru biyu, inkuwa bahakaba saina sa6a miki kamanni Mara mutunci kawai, karna fito Na iskeki cikin gidana wlhy kinji Na fad'a miki shashasha".
      Wannan hukuncin yamin dai-dai, Dan in ba hakaba wannan makirar saita kashema iro aurensa, Dan itace ke zuga uwarsu, Na tabbata ko wannan ciwon k'aryar da Laure taitayi harda bakin 'yar banzar can".
         Anty shukurah tamatso jiki a sanyaye tana Bama baffah da Ammah hak'uri.
         Albarka sukaita saka mata, sannan Ammah Tamusu bayanin ya khaleel d'inma bashida lfy.
     Har d'akin ya khaleel baffah yashiga, khaleel Na kwance idonsa biyu, tun fara maganar Ammah dasu Anty zuwairah ya farka, komai akan kunnensa yafaru, bak'inciki da k'yamar halin mahaifiyarsa da 'Yar uwarsa yahanashi fitowa, dukda abin yahad'ama darashin jin k'arfin jikinsa.
     Su Ammah na shigowa ya lumshe idanunsa, baya buk'atar Susan idonsa biyune, Anty shukurah tajawo stool d'in madubi ta ajiyema baffah gaban gadon, kusada ya khaleel, zama yayi yanamai tausayin d'an nasa, saboda halin mahaifiyarsa, yasan kokad'an khaleel bayajin dad'in mahaifiyarsa, hak'uri kawai yakeyi kasancewarsa mutum mai kawaici da had'iye damuwa, kokai waye Baka isa tantance damuwar khaleel ba, mutumneshi mai taka tsantsan da iya zaman duniya, komansa namasu nazari da dattakone, gashidai yaro amma akwai halayen manyan mutane tattare dashi, wannan baiwace da ALLAH yamasa tun yana k'araminsa.
    Ahankali baffah yakai hannu yana shafa kan ya khaleel d'in, cikin taushin murya yace, "ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, ALLAH yabaka lfy".
    Ammah da Anty shukurah sukace ameen.
      Ammah tace, " aii zazza6in ya sauka ko? Dan sanda yakirani yanajin jiki sosai, amma dayake iro jarumine baka gane hakan".
    Murmushi baffah yayi, "Ammah da d'an sauran zafi kam ajikinsa, amma ba sosaiba".
     "To Alhmdllh, aidayake likita ya dubasu".
     Baffah ya jinjina kansa yana kuma fad'in " ALLAH dai yak'ara sauk'i, ina ita matar tasa?".
     "Itama tana d'akinta babu lafiyar, Shukurah duba ita kiga tashi".
     " to Ammah".
Addu'a ya khaleel yakeyi azuciyarsa ALLAH yasa kar Ammah tamasa 6arin makauniya a gaban baffah, kaidata gama kasheshi wlhy.......
    Tunaninsa yakatse lokacin da Anty shukurah tadawo tana fad'a musu haryanzu Aysha barci takeyi.
        d'akin Ayshama saida baffah yashiga, sun isketa tanata barcinta itakam hankalli kwance, itama baffah yamata addu'a sannan suka fito.
          Suna fita Aysha tabud'e idonta, Ashe itama idonta biyu, duk badak'alar da akeyi acikin kunnenta, jin motsin tahowarsu yasakata rufe ido harda d'an munsharin k'arya.
    Jitai wata k'aunar surikin nata kuma mijin mahaifiyarta na ratsata, tareda kakar mijinta, surukar mamarta, dakuma d'iyar mijin mamarta kuma yayar mijinta, ta share hawayen dasuke kwarara bisa kumatunta, zuciyarta Na mamakin hajia babba wace irin mutumce?, akoda yaushe tana mamakin taurin zuciya irinta hajia babba, ga maigadonta nan kuma sak tasamu Anty zuwairah.
    Ta sauke ajiyar zuciya, yayinda tunaninta ya iso kan mijinta, shikuma halayensa sunyi mugun samun tazarar nisa tsakaninsa dana mahaifiyarsa, kokad'an ko alama babu kamanceceniya yanayin halitta ta halaye da jini da yakamanta hajia babba da ya khaleel, tomiyasa haka?, wannan ikone kuma Na ALLAH mad'aukakin Sarki, mai fidda rayayye daga jikin matacce, zuciyar Aysha tafad'a yayinda tunaninta ke k'ok'arin tasirantuwa da shakku, "hakane kuma" tafad'a tana gyara kwanciyar, tareda dawo da tunaninta akan mutanene jiya dasuka shigo musu gida.
    Tabbas yakamata tayi tunani akan waya turosu? Shin ta 6angarenta sukazo? Kokuwa ta 6angaren mijinta?, tasan zuciyar su hajia babba a bushe take, bushewa kuma irinta kututturen marke daya mutu a shekarun tashen k'uruciyarsa, tacije le6enta Na k'asa da k'arfin masifa, kaikace zata hudashine da hakwaranta, lokacifa yayi dazatayi aiki ba saka lokaciba, inkuwa bahakaba lokaci zaita gudun zomo da tunaninta, zata kira Anty meerah dansu mik'e tsaye, wannan lokacin bana tsare-tsare baneba na gudanarwa ne da zartar da hukunci ga masu laifi irinsu hajia babba, zasu farane da k'ananun kwari irinsu glory domin dakushe kaifin su hajia babba, tasaki murmushin gamsuwa akan tunaninta.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now