23

3.4K 289 0
                                    

2⃣3⃣

     yaukam tafiyar tawa akawai 'Yar rakiya, Dan miss xoxo tahad'o kaya itafa sai UK👜.
     Tagaji so take tagano muku Aysharku🤣
       Idan munrasa kud'in jirgin dawowa saimu mak'ale a can kawai, dama kullum da ji6in goshi nake had'a na tafiyar😂.

       Islands (UK)

Da acefa zan aureka, zan biyayya abayanka.
     
ina sonka, nayaba da halinka, k'yan jiki da surarka, sahibi da hannunka kaban ruwa.

ni nai sa'a kan masoyi mai fara'a, kai ka fara sa shadda duk garinmu an shaida d'an uwa.

K! Wai lafiyarki kuwa?. Meerah tafad'a tana zungurin Aysha dake kwance akan gado idonta arufe tanata rero wak'ok'i, tayi wannan tasaki takama waccan.
     Firgigit Aysha tatshi zaune, ganin Anty meerah sai kunya takamata tayi k'asa dakai tana murmushi da fad'in Anty meerah yaushe kikazo?.
         Ya za'ayi kisan nashigo sholy? Kinfad'a soyayya, dama nadad'e ina zargin hakan wlhy, meerah tayi maganar cikin damuwa da fargabar kodai Aysha tafad'a tarkon wani cikin yaran turawannan?, karfa ayi gudun gara, afad'a gidan zago kuma.
        Meerah tace, "sholy please kifad'amin gaskiya waye zai wargazamin tanadina danakeyi akanki?".
     Yanda meerah tayi maganar cikin damuwa yasaka Aysha d'ago manyan idanunta dake cike da gashi ta saukesu kan Anty meerah, kaitashiga girgiza mata cikin sanyinta tace, " wlhy Anty meerah babu kowa".
     To amma Aysha wannan wak'ok'in hausar dakikeyi koda yaushe suna nunamin akwai soyayyar wani aranki, kada ki 6oyemin, bazan hanaki sonshiba, zanduba cancantarsane kawai. Dan ALLAH kada ki 6oyemin, inhar kind'aukeni yanda na d'aukeki.
        Ajiyar zuciya Aysha tasauke tareda had'iye yawu, muryarta Na rawa alamar shirin yin kuka tace wlhy Anty ba anan yakebafa, tun a gida Nijeria ne, kumafa nima banyarda sonshi nakeyiba, Arena ce tacemin sonshi nakeyi.
      Meerah ta girgiza kai tana kallon ainahin k'uruciyar ayshar, matsowa tayi kusada ita takama hannunta, to nayarda ba sonshi kikeyiba, amma fad'amin wanene?.
      Aysha tad'ago ido tad'an kalli meerah saikuma tayi murmushi, ALLAH Anty ba sonshi nakeyiba, haka kawaidai nakejin nadamu dashi, kofa nature tunaninsa saiya dawo, ninamasan yafi k'arfina.
     Hhh aini sunansa nace fad'amin my lil.
      Kai Anty ya khaleel nefa.
        Bak'aramar dariya meerah tayiba, wai Aysha tasan soyayya, takatse dariyar tana kallon aysha, karki damu, Indai ya khaleel ne baifi k'arfinkiba, kedai kitsaya kiyi karatu, duk sanda yaganki dakansa zai soki, kuma zakice ninafad'a miki.
     Aidama tuni nafahimci wani Abu, tunda kika bani labarin gidansu, yanda kike Shiga shauk'i inkinzo Kansa da kurantashi dakikeyi nagane yayi kamun zuciyar sholyna😂.
          6oye fuskarta Aysha tayi tana dariya.
    Meerah kuma taita tsokanarta.

            A6angaren karatun Aysha kam saidai muce Alhamdullahi, komai yana tafiya yanda yakamata kam, tana k'ok'ari dak'ara fahimtar abubuwa yanda yakamata, Arena kuma nak'ara bata taimako wajen zaburar da ita abinda bata saniba.
     Wad'annan abubuwan suka had'u wajan bunk'asa ilimin Aysha da k'arin kwazonta, ayanzu haka suna shirin yin exams, wannan yasaka ayshar sake maida hankali sosai, meerah ma Na taimakonta wajen k'yautata mata da d'auke hankalinta ga damuwa ko tunanin gida da ayshar kanyi akoda yaushe, inhar ta tuno gida takan zauna tasha kuka harsai taji tagaji, meerah bata hanata, Dan aganinta kukan zai rage mata nauyin zuciya da damuwarta.
      Alhmdllh itama meerah a 6angarenta komai natafiya yanda yakamata, tayi tuba Na gaskiya, duk abinda tasan zai ta6a imaninta tana guje masa, kullum da k'aryar dazata sambad'a saboda kartaje club, bata shaye-shaye yanzun, Anty glory tatsareta ranar da tambaya akan canjawa datayi.
     Sai kawai meerah tafashe mata da kuka.
   Hankalin Anty glo yatashi sosai, tashiga tambayarta miya farune?.
     Meerah kan ta karkace ta sambad'o k'arya wai sunyi fad'a da saurayinta, Dan takamashi yana muna furtarta da wata budurwa.
     Anty glo....tayi tsaki, yo saime? Shine zakiyi kuka akansa? Kema kiwatsar dashi, gari dayawa wai mutuwa tashiga birni.
     Karin maganar Anty glo.... Tasaka Aysha dake gefe tana duba books d'in school NATA gumtse dariya.
      Anty glo....tacigaba dafad'in kibarsa nasan wani zaizo aii, kinada k'yanki da k'uruciya, shine banza Dan dama nagaji da ganinku tare.
     Dama madam Joy ta turomin kaya daga Nijeria suna zuwa Zamfara had'aku keda Aysha da besi, yanzu kihuta kawai abinki harsai kinsha gyaran kece raini.
                Gaban Aysha yafad'i, itakam haryanzu fargabar kaidinsu Anty glo.... Nabata tsoro, kuzo Ku ajiye yara kawai Dan biyan buk'atarku, aranta tace, "ALLAH yamana tsari daga sharrinku".
     A can kuwa meerah cewa tayi inayinki Anty glo..... d'inmu, aikinki Na kyau tayi maganar tana rungumeta, aranta kuwa fad'i take tsinanniya aniyarki tabiki, awanan karon tuba nayi Na gaskiya, insha ALLAH kun kusa nemanmu kurasama, baradai Aysha takammala karatunta.
     Anty glo....taji dad'in furucin meerah kam, sai washe hakwara takeyi.
     Ahaka happy tashigo ta samesu, daga ita sai bes iyakar cinya, ko bra babu ajikinta, 🎁abinda ke hannunta tamik'ama Anty glo....., waigashi wani yakawo abaiwa sholy.
       Ido Aysha tazaro waje, Anty happy nifa?.
   Eh ked'in, cewar happy.
    Kar6a Anty glo.... Tayi tabud'e, 💐filawa ce mai k'amshin tsiya aciki, saikuma d'an kwalba mai kyau anzuba k'ananun kifin roba aciki da ruwa, sunata yawo acikin ruwan, wata 'Yar takarda Anty glo.... ta zaro anrubuta.
*_for you! my Hayatee._*
          Cikin mamaki duk suke kallon Aysha, Anty glo.... tamik'ama Aysha kayan.
      Itamadai juyasu take tayi, amma tagaza gane wanene zai iya tura mata wannan sak'on?, tad'an shinshina fulawar, kamshi mai dad'i yadaki hancinta, harsaida ta shak'a ta lumshe idanunta, kamar tata6a jin k'amshinan, to amma a ina?, wannan itace tambayar.
        Sholy waye ya aiko miki?.
   Wlhy Anty glo....ban saniba nima?.
    Anty glo.... Tamaida kallonta ga happy, happy waye yakawo?.
     Wata 'Yar budurwace Anty glo....
       Aysha tayi saurin fad'in ALLAH Arena cemato.
  Kai amma ta rud'ar dani.
      Suma su Anty glo.... Duksun amince hakad'inne.

(Nikamdai nace ALLAH yasa to)🤭

Washe gari koda suka had'u a makaranta Aysha batayima Arena maganarba, tace, "inhar batayi mataba, itama bazata yimataba ko".
    Har suka kammala exams d'in kuwa arena batayi maganarba, itama Aysha ta share batayimataba.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, su Aysha sunkammala exam d'imsu, Alhmdllh tayi kwazo kam, dantasamu nasarar shiga grade 2, (kunsan sufa ba jss ko ss suke cewaba) kuma kwakwalwarka ke kwatarka sukam.
     Sosai Aysha tak'ara maida hankali akaratunta, Dan Arena Na taimakonta sosai, turancikam anwuce wajen tuni, idan tana zuba yaren turanci saika d'auka haihuwa da girman cance, abincinsuma tafara kwarewa daci😂.

Yau takama weekend basuda school, Dan haka meerah tace, ''tashirya suzaga gari".
   Dama haka take mata, inhar batada school ko wani uzuri sai Anty meerah tad'auketa takaita wajaje daban-daban, dukdan ta d'ebe mata kewar gida dana 'yan uwa.

Baramu lek'a Nijeria kuma.
    Amma zanbar xoxo a UK kawai😜

*_Nigeria_*

                Baffah ya sanarma Ammah zancen fad'ima, bak'armin farinciki Ammah tayiba kam, Dan shikansa baffan yayi mamakin yanda Ammah ta nuna murnarta sosai.
       Takumace karyaji komai ita zata sanarma matansa.
    Bikinsu fadeelah ma da ita za'ayishi.
    Yaji dad'in kalamanta kam, dan haka yafara shirye-shirye abinsa.

Baffah shiri babu amincewar amarya😂.

*_Kano_*

      Tunda mama suka dawo daga Jigawa abubuwa dayawa suke caccakar mata rai, amma saita d'ebesu tawatsar baya saboda shirin bikinsu Fadeelah dayaketa kawo jiki.
    Shiri akeyi sosai, Dan kawu bilyamin da kawu Ahmad suna k'ok'ari, tamkar Malam Abubakar mahaifin su Aysha nadarai.
    Amare Hafsat & fadeela kam aii ba'a magana.
   Sunata shan gyara wajen gwaggo Asma'u, Dan kusan sati biyu kenan tad'aukesu suna wajenta a katsina.

_____________________________
Zaune suke awajen shak'atawar, wajene had'ad'd'e Wanda akayishi Dan hutawa kawai, yaran turawa da iyayensu kowa nata uzurinsa awajen, bak'ak'en fata d'ai-d'ai sukan gitta.
     Meerah sanye take da wandon jins bak'i tad'ora wata farar Riga mai santsi, sai jibgegiyar rigar sanyi ja data saka a sama, takawo siririn gyale tarufe kanta dashi, tayi k'yau sosai masha ALLAH.
       Aysha kam Na sanye da wando da Riga itama, Jan wando da yellow d'in Riga, tasaka pink d'in rigar sanyi Asama, bata saka d'ankwaliba, saidai taja hular rigar sanyin har saman kanta, takalminta mai igiya yellow yayima k'afarta k'yau ainun, zagaye wajen sukeyi anutse suna 'Yar hirarsu cikin harshen Hausa.
        Aysha tsaya tareda rik'e k'ugunta tana dad'in wash Anty meerah, ALLAH nagaji over.
    Matashin saurayi bak'in fata dake zaune bisa kujera yana karatun wani story book yad'ago da sauri danjin yarensa a inda baiyi zatoba.
      Kallon Aysha da meerah yakeyi cikeda mamaki.
   Meerah tayi dariya, to raguwa zomu k'arasa can muzauna kihuta.
      Binsu yayi da kallo harsuka zauna, yasauke ajiyar zuciya yana maida kansa ga karatunsa, amma saidai yakasa hakan.
   Tsam yamik'e yanufi indasu Aysha kezaune sunacin popcorn🍿...........🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now