37

3.5K 307 1
                                    

3⃣7⃣

     Tunda sukayi sallama su Amal dake falon suka taso da gudu suka rungume fadeela, kowa Na k'ok'arin d'aukar ummuhanee dake hannunta.
     Aysha gefe takoma tana kallonsu cikeda birgewa, saida suka gama murnarsu sannan suka lura da Aysha, itama sunmata tarar mutunci, amma abinda talura dashi shine babu Wanda yaganeta, hakan yamata dad'i kuwa.
        Haka sukaita kaya-kaya agidan har yamma, amma Aysha bataga koda gilmin ya khaleel ba.
       Duk suna zaune afalo, amma banda samarin, Dan duk basu dawoba, hajia babba tadawo daga aiki, sannu da zuwa suka hau yimata, ciki-ciki ta amsa tayi shigewarta 6angarenta.
    Idan da sabo sun saba da hakan, harma yazame musu jiki, Aysha kam afakaice tarakata da harara, sannan batayi gaisuwarba koda yaran sukayi.
       Kwala kiran sallar magriba yasakasu mik'ewa suduka, su Shahuda sukaja Amal d'akinsu, Su Tasleem kuma Aysha, ita bama sallar takeba tana fashin sallah.
      Su Tasleem duk sukayi alwala, Aysha Na kwance a gadonsu tana latse-latse a awayarta, kukan Adeel tajiyo a falo, har Maleeka zata fita Aysha tace zokiyi sallarki, bara Na dubasu.
         Maleeka tace to, Aysha kuma tafita.
       
Miya faru kake kuka Adeel?.
        Cikin kukan ya nuna Haleefa, ta maida kallonta kan Haleefa dayay kwal-kwal shima yana niyyar kukan.
     Mekamasa?.
  Cikin tsamin bakinsa Na yara yace Anty bacineba icimin biscuit d'ina.
      Shine kadakeshi? Haleefa kaji tsoron ALLAH, yayan kanefashi?.
      Affan yarik'e hannun Aysha yana fad'in Anty nimafa sai ya dukeni a school tazun, kuma cena fad'ama ya khaleel.
     O kai haleefa ALLAH ya shiryeka dubeka.......
     Bata k'arasaba taji affan ya fusge hannunsa anata yakwasa aguje.
       Juyowa tayi da sauri Dan ganin shima Adeel yagudu sai Haleefa dayaja baya zai 6uya abayanta.
        Kasa ya duk'e suka shige jikinsa, bataga fuskarsaba saboda yaran sun kare, amma jin yanda kirjinta keta harbawa taji ajikinta shine, dak'yar tacira k'afa danufin barin falon ta tsinkayi Golden voice d'in nan nasa na kiran ke maleeka zonan.
     Bak'aramar fad'uwa gabanta yayiba, dan bataso had'uwarsu yau ba, ganin tamak'i juyowa ransa yafara 6aci, k! Banason iskancifa, bakiji minacebane?.
            Jiki a sanyaye Aysha tajuyo gareshi, wata 'Yar zabura ta mamaki yayi, yanunata da d'anyatsa zaiyi magana kenan saigasu Maleeka sun fito, 6oyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya wayance dafad'in k! Kikawomin tea.
     Yana gama fad'a yakama hannun Adeel da Affan zuwa 6angarensu, Haleefa nabinsu abaya a6oye.
     Itama Aysha ajiyar zuciyar ta sauke ahankali, su maleeka kam sai dariya suke saukewa, Tasleem tace kije kicika aikin oga, Dan wlhy ya khaleel babu ruwansa da bakuwa, kuma tunda ke yace babu Wanda zaikai shayin baikusa cinyeshi da jarabar masifarsaba, kema daga nan kun k'ullah kenan.
    Miya farune? Mama dake fitowa ta tambaya.
   Tasleem tafad'a mata ya khaleel ne yace Aysha takai masa tea.
      Mama tace to shine take tsaye kuma? Kiwuce yana nan nama dafa masa tun d'azun, dan naga zaije masallacine shiyyasa ba'a kaiba.
     Kamar Aysha zata fasa kuka haka takeji, kicin d'in taje ta d'akko k'aramin tire mai d'aukeda falas d'in tea, sai mug da cokali k'arami.
    Falon tadawo tana tura baki gaba, tace, maleeka rakani, nibansan d'akinsaba.
      Hararta mama tayi, tace kishiga nan aibazaki rasa d'akinba, anty Mamie data fito tace a'a Yaya fad'ema, kibari ta nuna mata, in bandama abin babana yazakasaka bak'uwa aiki, ai saiya bari tad'an k'ara kwana biyu ko.
     Mama tace ko zuwanta kenan gidan yasakata aiki badole ta ajiye jakka tayiba, tayi shigewarta kichin.
    Maleeka taraka Aysha 6angarensu samarin gidan, bin komai Aysha takeyi da kallo, komai Na falon bawanda tasani baneba, ancanja komai, saidai fes yake tamkar yamda tasani abaya, ak'ofar d'akin ya khaleel maleeka tatsaya, tace gashinan.
      Aysha ta langa6e kanta tamkar zatayi kuka, kai maleeka please kirakani mana.
     Idanu maleeka tazaro, kai Aysha rufamin asiri, tunda ke yasaka aikin walhy naje yanzu saiyaci k'aniyata, kedai jeki zan jiraki afalo, aii babu abinda zai miki, shifa sai an ta6ashi yake fad'a, kuma ma su Adeel suna wajensa aii.
      Babu Wanda Aysha zatayi haka taja k'afa tamkar wadda kwai yafashema aciki, ciki-ciki tayi sallamar, yana zaune akan sofa, dagashi sai wando 3quarter da vest fara k'al, duk su Adeel suna jikinsa, ya ajiye musu lap-top d'insa suna kallon cartoon, shikuma idonsa a wayarsa yana danne-danne.
     Rumtse ido Aysha tayi gabanta Na fad'uwa, bak'aramar firgita tayiba daganinsa haka, Dan damtsen hannunsa yamugun tsoratata, tai saurin kauda kanta daga kallonsa.
       Har yanzu idonsa nakan waya, su Affan ko bama susan tashigoba, kallon cartoon yad'auke hankalinsu.
       K! Idan bazaki ajiyeba ki koma dashi.
       Haushi yaso kama Aysha, amma saita dake, tajawo k'aramin glass table dake gefensa tad'ora, saida tafara tafiya takusa k'ofar fita yace dawo.  murgud'a bakinta tayi sannan tajuyo, alokacin kuma yad'ago suka had'a ido, Aysha tayi saurin janye nata, tunba yanzuba wlhy tsoron mayun idanun nan nasa takeyi, gashi yanzu sund'an shanye alamar haryanzu akwai sauran gajiya taredashi.
     Kafeta tayayi da idon nasa, wannan yasakata gaza koda satar kallonsa, tambayar daya jeho matace tasakata d'agowar dole.
   K wacece!?
    Batasan sanda bakinta yasu6ce tace kamarya? Ni wacece?, ni mutumce mana, tak'arashe maganar da murgud'a baki.
      Aransa yace akwaifa rashin kunya buhu-buhu awajen yarinyarnan..
     Afili kuma saiya gallah mata harara, k banason tsiwa, mikikazo yi gidanmu?.
     Baki Aysha taturo gaba, cikin shagwa6a tace nima kuma gidanmune, ahankali tace bare amin gori.
        Su Halefa dake jikinsane yahanasa tashi, dasai ya saita bakin yarinyarnan wlhy, amma cikin tsawa yace anturokine lek'en asirina ko? Shiyyasa kike bibiyata?.
     Aysha batasan sanda tasaki wani mugun murmushiba, harta samu kwarin guywar kallon cikin idonsa, amma kwarjinin dake taredashi yasakata saurin janye idon nata, da gudu tabar d'akin batareda ta bashi amsaba.
      Kuttt! Yafad'a yana binta da kallo, yana rasa mizaice, saikawai yaja ajiyar zuciya, dolenema yayi bincike akan yarinyarnan, danyasan wacece ita?, shifa mamaki take basa, saikace aljana, tunda yake babu macen data ta6a kallon tsakkiyar idonsa sai yarinyarnan, duk girman mace kwarjini yake mata takasa masa kallon minti2 ma, bare cikin idonsa, duk jidakan yarinya da isarta, inhar zatazo wajensa tace tana sonsa, kotazo suyi wata magana, wlhy inhar yadasa mata idonsannan na 1minute kawai saikaga jikinta narawa, tashiga hankalinta daganin bakin Rijiya bawajen wasan makaho baneba.
     Amma yau ga yarinya k'arama, wadda k'annensa nawajen 15 sun girmeta, ta kalli tsakkiyar idonsa.
    Ya furzar da huci daga bakinsa, Wanda yasaka su Affan kallonsa.
         Aysha kam koda suka koma babban falon wajen sauran yaran, batawani dad'e Na firaba tatashi takoma d'akin mama, firarce ta'isheta, dama can Aysha bamai son hayaniya baceba, Anty meerah takira sukasha hirarsu, wai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu dawo daga Kd, harda mama Dan dad yabiya za'a kaita india asaka mata k'afar roba.
     Aysha tayi farinciki sosai, Dan mama tabata tausayi, rashin k'afa bala'ine.
        Fadeela zuwa tayi tad'auki kayan barcinta Dana Ummuhanee,  d'akinsu Amal zata kwana, Aysha tace aii ina gadon uwata, saida safenki.
   Bayan tafiyar fadeela mama tashigo ta kimtsa, baffah yadawo yanzu babu dad'ewa, kuma girkin mamane.
     Ganin haka Aysha tace aikam bara Na shirya Nima d'akinsu Tasleem zanje Na kwana, bazan kwana nikad'aiba.
      Mama tace a'a kiyi kwanciyarki, inasu Affan? Basai Ku kwana tareba.
    Mama suna d'akin wannanfa mutumin, kuma k'ila a can zasu kwana.
    Waye mutumi? Mama ta tambaya tana fesa turare.
      Wanda yace nakai masa tea d'azun.
        Zai dawo dasu indai babana ne, idan yana gida dama canne wajen hirarsu tunma basukai hakaba, dayaga sunyi barci zakiga ya kawosu. Mama bata jira amsar aysharba tafice abinta zuwa 6angaren baffa.
            Mama nafita Aysha tamik'e tashiga wanka, bayan tafito tashirya cikin wando dogo da Riga Na cartoon kalar popul, sunmata kyau, tana gaban mudubi tana tufk'e gashinta Dan bataso tayi barci dashi ahaka, yaturo k'ofar yashigo, da sauri Aysha tajuya tana kallonsa.
     'Dauke yake da haleefa da Adeel a kafad'a, sa6anin d'azun yanzu yasaka doguwar jallabiya, Affan nabiye dashi abaya, da'ala shi baiyi barcinba.
     Ko kallonta baiyiba yad'orasu a gadon mama, saida yagyara musu kwanciya sannan yanufi Waldrop d'insu ya d'akkomusu kayan barci.
  Mamaki dukya cika Aysha, aranta tace irin wannan samun waje haka.
     Tana jingine da madubi tana satar kallonsu ya canjama yaran kayan barci su duka, sannan yamusu addu'ar barci ya shafa musu, Affan yace Yaya ni awajenka Jan kana.
      Murmushi yayi tareda jawo yaron jikinsa, yace haba my lil bro d'ina, kaga zomu kwanta, nima yau a gadon mama zan kwana, amamakin Aysha saitaga ya kwantar da yaron a jikinsa shima yaja filo ya kwanta, ahankali yake bubbuga bayan yaron idonsa a lumshe
    Aysha samun kanta tayi da sak'a wani Abu a zuciyarta, tasaki sassanyan murmushi, jitake inama tunanin nata yazama gaskiya.
      Duk abinda takeyi ya khaleel Na kallonta ta k'asan idonsa, bakinsa yata6e ya kauda kansa daga kallon nata.
     Saida ya tabbatar barcin Affan yayi nisa sannan ya kwantar dashi kusadasu Adeel yakuma yimusu addu'a yarufesu da bargo yafice abinsa, batareda ya nuna yamasan dawata hallita a d'akinba.
    Da uwar harara Aysha taraka bayansa harya fita.
    Yana fita tafad'a gadon tareda jawo filon daya d'ora kansa ta rungume tareda lumshe manyan idanunta, jitake kamar ya khaleel ta rungume, ga sassanyan k'amshin turarensa natashi ahankali, shidai baka ta6a cewa wannan shine turarensa Na dindin din.
    
Shima yana fita 6angaren mom yanufa.
    Babu kowa afalon sai Mufeeda dake barci, itama nakula bawai barcin takeyiba, takune kawai naneman hanyar dazata fita anjima wajen saurayinta atafi shek'e ayar da'aka saba, Dan batama San ya khaleel yadawoba.
       Ganinsa yasaka gabanta fad'uwa, amma saitayi lamo kamar tana barci.
    Tashinta yayi yace tashiga d'aki, tatashi tana wani Mirza ido, kaikace gaske barcin takeyi, lah ya khaleel yaushe kadawo?.
    d'azun. Yafad'a a tak'aice.
   Yace Momy fa?.
Takwanta tun d'azun saboda tagaji tace, su Hasnama sun kwanta.
     Yace kema shige ki kwanta.
      Ranta A6ace tashige d'akinta, amma tana addu'ar ALLAH yasa fita zaiyi.
        Samun kansa yayi dason zama afalon, saboda American film d'in dasuke nunawa a Fation yamasa k'yau, yad'auki remote d'in yakoma saman 3seter ya kwanta.
       Kamar mufeeda zata fasa ihu haka taji, gabanta yaywata muguwar fad'uwa lokacim datajiyo wringing d'in wayarta dake gefen ya khaleel..................✍🏿

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now