35

3.5K 296 0
                                    

3⃣5⃣

       Kano tadabo tunbin giwa, kofa dami kazo dagaske munfika😜, amma banda tsiya🤕.
       Tunda akace sunshigo Kano farincikin Aysha ya bayyana, babu abinda kake gani tareda ita sai farin ciki tsantsa, itakam tsaf tagane gidansu, dukda canje-canje da'aka samu kuwa, gidanma gaba d'aya ya canja mata, danyasha sabon fenti sai d'aukar ido yakeyi, 'yan anguwa kam sai kalon zuk'a-zuk'an motocin sukeyi, hardasu Kansu masu motocin, ko kad'an babu wanda yagane Aysha, to yama za'ayi kad'auka Aysha bahaushiyace, balle tak'ara girma da k'yau, kaikace irin bak'ak'en Amurakawan nanne,   itakam dayawansu ta shaidasu, saidai dukta mance sunansu, murmushi taketa zubawa abinta, dakanta tamusu jagora zuwa cikin gidan, tunda sukayi sallama tafara kwala kiran mama da Ummah.
    Fadeela daketa faman jijjigar Ummu-hanee tana kuka talek'o Dan mamakin kiran da ake kwalama iyayen nata.
    Tsam tatsaya tana tantama akan shin Aysha ce? Kokuma watace mai kama da  Aysha?, gadai kamannina na Aysha ajikin matashiyar budurwar, amma ko dawasa ba'a fara kiranta Aysha ba.
    Da gudu Aysha tak'arasa wajen Anty fadeelah, ta mamuk'eta tana ihun murnar ganinta, ihunne yatada Ummah dake barci saboda kanta dakeyin ciwo.
    Ai Aysha naganin Umma tasaki Fadeelah taje ta d'are Ummah, wayyo ummanah nayi kewarki wlhy.
      Ummah tarungume Aysha, hawaye nazuba a kumatunta tace Aysha dagaske kece? Dama zaki dawo garemu? Shikenan babuke babu bintu?.
     Meerah mom ifteehal natsaye suna kallonsu cikin burgewa.
   Dad da Naufal maheer suna k'ofar gida suna jiran amusu iso.
      Fadeelah Ce taimasu mom marhabun, aka shiga dasu falon Ummah, haryanzu Aysha na nane da Ummah, sai tanbayar mama takeyi, babudai Wanda yabata amsa.
       Bayan zamansu ne fadeelah takawo musu ruwa, Ummah kuma takira number mijinta da kawu bilyamin, hardasu Qasim yayunta wad'anda aketa shirin bikinsu.
      Aysha tak'ara fad'in Umma wai ina mama?.
        'Yar dariya Ummah tayi. Tace Aysha mama na Abuja abinta.
     Abuja kuma Ummah? to wajen wa?.
      Aure takeyi, Ummah tafad'a tak'aice.
Nan take fuskar Aysha ta canja, idonta tab da kwallah tace  aurefa Ummah?. Kishin sosai a idanun Aysha tana taya mahaifinsu kishi.
     Babu Wanda hace komai saboda shigowar Mijin mama da kawu bilyamin, saisu dad dake binsu abaya.

Gaishe gaishe aka fara, kowa sai d'okin ganin Aysha yakeyi, ita kuma tana jikin Ummah rik'eda Ummu-hanee.
         Su dad sunyima su kawu bilya bayani akan Aysha, amma sun 6oye komai kamar yanda Aysha tabuk'ata, Dan so take da kanta tad'au mataki akan su gwaggo bintu.
       Sunce Aysha karatu taje, kuma tun farko a hannunsu take, kowa yaji dad'i kuwa, sunsha godiya sosai.
     Kafin kacemi anhad'a musu cima mai k'yau da gamsarwa.
     Dukda bawani sabawa da cimar sukayiba sunci babu laifi, ita kanta Aysha ta fara manta cimar k'asarta, (kowa yabar gida, aii dolene gida yabarsa)..
         Aranar aka kira mama aka sanar da'ita dawowar  Aysha, tayi farinciki, jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano, lokacin suna shirin zuwa asibiti duba gwaggo bintu.
     Tace zata taho Kano gobe idan ALLAH ya kaimu.
     Kawu bilyamin yace a'a tayi hak'uri, insha ALLAH nanda kwana uku za'a kawo mata Aysha har gida.
    Wannanne yasakata hak'ura da zuwan.
      Aranar su dad suka baro Kano, Aysha harda kuka dazasu taho, sunyi sallama akan saita zo Abuja, suma daga nan Kaduna zasu tsaya, sai zuwa jibi zasu shiga Abuja, daga nan zasuje sokoto ma.

       Zuwa yamma saiga Hafsat, su Rufaida  da sadiya ma saigasu, gida yagama had'uwa, Aysha tana tsakkiyar danginta, jitake kamar ta shekara dubu basa tare, sukam sai sha'awarta sukeyi, danta canja musu gaba d'aya, saikace wata baturiya, anyi-anyi takira mama tak'i, dukda d'okin ganinta datakeyi wai fushi takeyi da ita akan tayi aure, hakama Ummah duk haushi suke bata ita adole kishin babansu takeyi.
     Makwafta sai shugowa akeyi ganin Aysha 'Yar turai, kai kace wani abin kallo aka kawo gidan.
    Koda yake Aysharfa ta cancanci azo kallonta, Dan komai nata ya canja, dolene kaganta ta burgeka harka lalace wajen kallonta.
    Har washe gari bata canja zaniba, 'yan uwa sai tururuwar zuwa ganin Aysha akeyi, itakam kowa yazo kar6ar mutumci take masa, dama can ba halin Aysha bane wulak'anta jama'a.

CIKI DA GASKIYA......!!Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora