74

4.3K 322 2
                                    

74

           Dogon d'akine, saidai anyi kananun d'akuna aciki tamkar na prison, yawancin d'akunnan dukda mutane aciki, matane kuma zallah awajen.
    d'akin dake can k'arshe suka k'arasa, kubrah Na zaune tacusa kanta tsakanin cinyoyinta, sai kuka takeyi, bata ta6a tunanin shiga wanga haliba, musamman yanda ta'iya takunta.
   K'arar bud'e k'ofarce tasanyata d'agowa da sauri dukta fita hayyacinta, kamar wata sabuwar kamu a hauka.
    Ganin khaleel yasakata mik'ewa zumbur zata nufosa, wata uwar tsawa Taheer yadaka mata, babu shiri tayi baya ta zauna da6ar.
        Lumshe ido khaleel yayi yana girgiza kansa, Samuel dake binsu abaya ya ajiyema ya khaleel kujera, zama yayi idonsa akan kubrah data koma jikin bango ta raku6e.
     Saida yamata kallon minti 2 sannan yajuyo yakalli Sam... Da Taheer batareda yayi maganaba.
      Ficewa sukayi, Dan sungane miyake nufi.
    Suna fita yadawo da kallonsa kanta, itama dataga daga ita saishi saita fashe da kuka, tana fad'in "Dan ALLAH khaleel kafitar dani, wlhy bammusu komaiba, zalincine yasakasu kamani".
       K'asaitaccen murmushi ya khaleel yayi, Wanda yadad'e baiyi irinsaba saboda damuwa, cikin turo iska daga hancinsa yace, " nima abinda yakawoni kenan kubrah, nasan ked'in mutuniyar kirkice, banta6a ganinki kina aikata Abu mara k'yauba, zan ku6tar dake ammafa saikin bani had'inkai".
      Har taune harshe takeyi wajen fad'in "wane irin had'inkai?".
      Nanma murmushin yasaki, muryarsa can k'asa yace, "kwantar min da hankalinki mana my Sweet".
    Wani dad'i yaratsa kubrah, khaleel yacemata Sweet.
     Shima murmushin yayi danya hango matakan nasara.
      " kubrah wanne kasuwanci kikeyi ak'asashe daban-daban Na duniya?, dannaga bak'ya kulla watanni biyu a Nigeria ".
     Tashin hankali, jikin kubrah ne yafara 6ari. Khaleel yace, " yahaka kuma da rawar jiki? Tambayacefa bawani abuba, saikace wata mara gaskiya?".
      "A...a'a wlhy, inada gaskiya khaleel, dama dai tambayarce tazomin a bazata, shi....shin...shinefa kawai".
       "Uhyimm, Sorry fa kinji".🤨
   Khaleel yay maganar yana d'age gira d'aya sama.
      " ina jiran amsarki".
     "To khaleel mizance maka, kasan ina business ne aii".
        " Nasan business kikeyi, amma wane iri nufina?".
      Gumin da keta tsatstsafo mata ajiki tashare da hannun doguwar rigar atanfarta, amma takasa furta komai.
    Shikam khaleel yayi masifar tsura mata idanu, zuwacan yace "shikenan, shikenan, barma waccan tambayar Nagano amsarta, miye alak'arki da hajia khaltum?".
     "Kamar Yaya take a wajena".
      "OK".
" akwai wadda kuka ta6a zuwa gidanmu da ita, lokacin bikina, itakuma wacece? A INA kuma take?".
         "Kamar zata fasa kuka tace k'awatace".
    "Tana ina yanzun?".
       " kwanaki tayi had'arin mota tama rasu".
         "Ayya, lalai ta iya mutuwa, amma nikuma naganta kwanakin baya a Lagos, zataje America".
      Afirgice kubrah tace, "glory d'in?, itafa a Islands UK takema".
        K'aramar dariya ya khaleel yasaki, danya samo amsar tambayarsa, yace, "kwarai kuwa, saidai inaga bayan dawowarta tamutu ko?, waccan dai kamar sunanta glory Zamani, koba ita baceba?".
       Kubrah tasaki ajiyar zuciya, "A'a ba ita baceba, k'awata sunanta glory maba".
          " dak'yau 'Yar gari, kin gamamin komai, tabbas ba ita baceba, amma ina jajanta miki mutuwar k'awarki, zanje muyi magana da habeeb dan yazo ya kar6eki, idan ni nanemi haka baza'a baniba, za'aga kamar munhad'a bakine".
      Godiya kubrah tamasa, dad'i yakamata baigano komaiba, gashima har yana shirin k'ubtar da ita.
   Harya mik'e Yakoma ya zauna, af kinga kuma Na manta, a INA zan samu habeeb?, Dan inaso yazo gobe, jibi inada tafiya zuwa London ".
       "Ito habeeb d'inne sai a slow, amma hanya mafi sauk'i kaje Cinema, yau za'a haska film, Na tabbatar zaije".
      "OK thanks, angama, gobe ki saurari sakamako, bye my Sweet😉".
      Dad'i kamar yakashe kubrah, haka Sam...yashigo ya d'auki kujera yafice, aransa yace banza, bakisan halin boss bane, dagani wayo yamiki.

______________________________

         Tunda ya khaleel yadawo office yaketa tunane-tunane, ta hanyar dazaibi yaje Cinema yau, ga tunanin binciken glory, ta inama zai fara?, kiran wayarsa da'akayi yakatse masa tunani.
       Wayar ya d'auka yaga Aysha Ce.
     Guntun murmushin yayi, danya kula kwana biyunnan tashiga damuwa da sharetan dayakeyi, saida takatse yakirata, bugu biyu kuwa ta d'aga.
     Muryarta can k'asa akuma galabaice tayi sallama, komawa yayi yajingina da kujera, shima murya can k'asa ya amsa mata, yace, " gimbiya yajikinne?".
        "Ga shinandai, ya aikin?". 'Duk a shagwa6e take maganar'.
         Saida ya furzar da huci sannan ya amsa mata da Alhmdllh, yaudai babu zazza6in ko?".
        " akwai mana, yanzuma nagama amai".
         "Wannan amai bazai tausayaminba, yabarki kid'anyi k'ibama, mikikaci to?".
      "Kunun gyad'ane".
     " sannu kinji sholyna, babies suna wahalarmin dake, dolene idan sunzo duniya namusu bulala, Saboda wahalarmin dake dasukayi, kona dawo gidane?".
     'Yar dariya tayi, wadda tadad'e batayiba, tace, _''A'a Sadauki, gara kazauna a office, kullum burina bai wuce kakawo k'arshen azalumaiba, idan kayi hak'an 'ya'yankama zasuyi alfahari dakai, hakan zaikuma tabbatar musu mahaifinsu jarumin jarumaine, 100% nimai k'arfafakace, bamai raunanakaba, koda yaushe addu'ata nanan biye dakai, nidai Burina kada kabar Azzalumai suyi barci mai dad'i, kahanasu dariya da farinciki, ALLAH ya dafa maka mijina abin alfaharina nida al'umma💋💋._
    d'ifff takashe wayar.
    Zabura ya khaleel yayi daga kwancen dayake yana saurarenta, "please karki kash......"
     Ina harta kashe, cikin hanzari yake dialing d'in number, amma ance switch up, yagwada yakai sau hud'u amma maganar d'ayace akashe take. Maida akalar Kiran yayi kan Ammah, cikin kwakwazonta ta amsa, dama Amman bata iya waya ahankaliba🤣.
      Kowacce Lamba da alamar datama mutum yanda zata gane, Dan haka khaleel Na kira taganeshi, iro!! Kaine da rana tsakarnan? toya ofishin nakune?".
        Dafe Kansa yayi, afili yace, ''wayyo nafa kira uwar kwarmato, yanzun saita had'amin mutanene gidan duka".
      "Wai iro Baka jinane?! Allo iro!, nifa banajinka, inaga natuwok ne, kasake kirana kawai ta ajiye batareada ta Yanke wayarba.
    tsaki yaja ya Yanke wayar, afili yace, " kai tsohuwarnan akwai kwakwazo, zubaina kenan, tuni Ammah zata saka kwalwar mutum harmutsewa, shi kawai inda yake sonta akwai tsage gaskiya".
     Komawa yayi Yakuma lafewa jikin kujerar, kalaman Aysha sai kai kawo suke a zuciyarsa, yarasa mitake nufi? Yakuma kasa fassarasu? Amma tabbas kalaman NATA sunfi kama dana mai gugar zana.
      "O my god, waimike faruwane?".🤦🏻‍♂

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now