21

4K 335 4
                                    

2⃣1⃣

           

Kano

   Alhmadulillh su mama sun fita takaba tuni, suna zamansu lafiya da k'yautatama juna kamar yanda suka saba.
    Matar uncle Ahmad tahaihu suketa shirin zuwa Jigawa suna.
    Kawu bilyamin dakansa yabada mota akaisu harda iyalansa.
         Sun isa Jigawa lafiya ansha suna kuma lfy, da yamma mama tashirya danufin zuwa wani gida gaida abokan arzik'i data sani.
         Itadasu Rufaida suka tafi da sadiya.
    Tun'a k'ofar gidan sukaci karo da zuk'ek'iyar mota bak'a wulik, su Rufaida sunata santin motar, mamadai batace dasu komaiba, sai murmushi datakeyi.
    Gidane madaidaici mai d'akuna uku, babu kowa a tsakar gidan, amma a share yake tas, saida sukayi sallama sau kusan uku sannan aka amsa, wata dattijuwar tsohuwa tafito tana kuyi hak'uri inata amsawa, karar TV tahana kuji......
    Maganarta takatse saboda ganin su mama, kai wanake gani kamar  fad'ima haka?.
     'Yar dariya mama tayi, tace, "wlhy kuwa inna mune mukazo garin, shine nace bara Nazo Na gaidaku andad'e ba'a had'uba.
    Aikuwadai wlhy, 'yanmata kushigo kunji.
     Rufaida da Safiya suka shiga gaba, mama nabinsu abaya.
      Falone irinna tsoffi, amma komai atsare, sai 'yanmata biyu dake zaune, kowa da 'abinda takeyi.
    Bayan sun gaisa inna tace haba fad'ima shikenan kuma anyanke zuminci shekara kusan ashirin?.
    Kuyi hak'uri inna, nayi laifikam amma amin afuwa, insha ALLAHU za'a canja.
    To ALLAH yayi albarka, wad'annan jikokinane ko?.
     Dariya mama tad'anyi, kanta ak'asa tace eh inna amma nawajen abokiyar zamatane.
    ALLAH sarki, masha ALLAH, amma fad'ima kardai had yanzu Baki haihuba?.
      A'a inna akwai uku.
    ALLAH Sarki, ALLAH ya albarkacesu.
    Ta kalli 'yanmatan nan biyu datum d'azu suke satar kallon mama Dan tamusu kama dawata dasukanta6a Sani. Tasleem tashi kuhad'o abinci mana ga mamanku wadda Baku saniba.
      To inna, tasleem da maleeka suka fad'a suna mik'ewa.
    Mama tabisu da kallo tana murmushi, inna wad'annanfa nawajen waye?.
         Fad'ima 'ya'yankine aii, 'Yar farar tawajen bilki Ce, d'ayar kuma d'iyar amaryarsuce, tare suke da Ibraheem da babansu.
         Ikon ALLAH, yanzu yaran Bilkeesu nawa?.
    Wai aii bilki anzama kaza uwar 'ya'ya, aibayan bariwarki gidannan haihuwarta 12, saidai d'aya yarasu kusan wattani goma kenan.
      Lallai Bilkeesu ALLAH yaraya manasu to...
    Ameen dai fad'ima, yanzu kuwa kuna inane dazama?.
     Inna INA nan cikin Kano, amma ALLAH yayima maigidanma rasuwa kusan wattani Biyar kenan.
    Sallallami inna tafara dafad'in oh ni Dije ALLAH yajik'an musulmai........
            Shigowar mutanen biyu yasaka su Rufaida gaishesu.
    Muryar Wanda mama taji yasakata kid'ima tad'ago ido da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna, ita tafara janye nata ido tayi k'asa dakai.
    Inna tace Abdillahi kundawo?.
  Jikinsa a sanyaye yace, ''eh inna mundawo.
      Matashin saurayi yace, "lallaima tsohuwarnan, nibazakice nadawoba ko?.
    Dariya inna tamasa yo Ibraheem kakoma mana, aidai bakaine Malam irona Na gaskiyaba ko? Aini tunda k'akiyin aure munraba jaha.
     Aikam saidai muraba harma k'asa kuwa.
   Dariya akad'anyi.
  Mama tagaida dattijon mutumin, ya amsa mata cikin kafeta da idanu, itakuma tak'i kallonsa.
    Shi ya khaleel ma sai yanzu yalura dasu mama, gaisheda mama yayi yanason tuno ina yasan wannan fuskar?.
   Su maleeka suka shigo da kulolin abinci.
     Mama tayi k'arfin halin fad'in wai Babane yagirma haka?.
    Kwarai kuwa fad'ima shine, Ashe zaki ganeshi?, gashinan d'an kwal uban yak'i aure.
      Kai Dan gidanku mamarkace wannan.
    Ya khaleel yashafa kansa, cikin murmushi yace, " inna aiban santaba kuma."
    Katanbayi Abdillahi aishi yasan kowacece.
    Juyawa yayi yana kallon Baffah datuni tsohon tsumi yamotsa masa, sai satar kallon mama yakeyi.
   Baffah fad'amin to.
             Dak'k'uwa Baffa yawatsa masa, yana fad'in ungo wannan Dan k'aniyarka.
    Dariya sukad'anyi.
Su Rufaida kam dukda kasancewarsu yara tuni ya khaleel yatafi da imaninsu.
   Yau sanye yake cikin shadda marun, wando dariga d'inkin zamani, rigar iyakarta cinyarsa, ya d'ora hulla zanna Bukar datai mugun fito da ainahin suffarsa ta Hausawa, sai k'amshi yake tashi ajikinsa mai sanyin dad'i.
       And'an ta6a hira wadda mama da baffa suka kasa sakewa, kowa da abinda yake sak'ama ransa.
    Ya khaleel madai baya cikin hirar, Dan tuni Yakoma can gefe saman wata kujera yazauna yanata danne-danne awayarsa, lokaci-lokaci yakan amsa calls da ake masa.
         Su mama sukamik'e domin tafiya.
     Inna tace, 'Dan ALLAH fad'ima kidinga waygowa yanzun, kuma insha ALLAH zamuzo bikin Fadeelah, Agaida yaran Dan da abokiyar zaman, ALLAH yak'ara hak'uri kinji.
    Amin inna mungode, ALLAH yak'ara lafiya.
    Su maleeka suka mik'e danyin rakiyarsu, Dan tuni har sabo yashiga tsakaninsu dasu Sadiya.
    Baffa yakira Tasleem yabata Rafa's d'in kud'i yace tabasu suhau mota, shima ya khaleel yakira yay dad'i akai.
                 Inna dama fad'ima nazuwa gidannan?.
   A'a wlhy, rabona da ita tunda kuka rabu, nima nayi mamakin ganinta, Ashe k'anin mijintane yake anan, matarsa ta haihu shine sukazo suna, 'Yar albarka bata mantamuba tazo gaishemu.
        Jinjina kai kawai baffa yayi, batareda yace komaiba.
   Ya khaleel daya dawo falon yace, "wai Dan ALLAH inna wacece ita?".
    Matar babankuce dasuka rabu bayan haihuwarka da wattani uku, yarinya mai hankali dasanin darajar mutane, kagadai ni amatsayin uwar kishiya nake gunta, amma wlhy tamkar mahaifiyarta tad'aukeni, (inna mahaifiyar aunty Mamie Ce masu karatu).
    Shiru ya khaleel yayi, danshikam k'yaunar matar tashigeshi sosai.
    Inna tace, ''kajima mijin nata yarasu wattanni 5 dasuka wuce.
   Da Sauri baffa ya kalli inna, suna had'a ido yay k'asa da kansa.
   Murmushinsu Na manya inna tayi, danta gano wani Abu ga Baffan.......

To komiye masu karatu?.😂

_____________________________
           Waini meerah kindaina zuwa club ne? naga 2days saikice kinajin barci,  kodai kinyi fad'a da babyn kine?.
     Murmushi meerah dakema Aysha kitson makaranta tayi kawai, amma batace komaiba.
   Lyn ta ta6e baki tana hararar meerar, o miskilancin yamotsane? Kokuma kinsha abinda yafi k'arfin kankine?.
          Eh, meerah tafad'a batareda takalli inda Lyn takeba.
   Itama saitaja bakinta tayi shiru, dantasan sarai meerah tafita buyagin rashin mutunci.
    Aysha najinsu, saidai tanata danne danne awayar meerah abinta.
    
Washe gari akakai Aysha wata had'ad'd'iyar makaranta dake nan bayansu, komai nad'an gata aka matashi, saita saje da 'ya'yan turawan kasancewarta fara tas, kuma k'yak'yk'yawa, kawai dai duk inda bak'i yashiga acikin turawa dolene ka shaidashi saboda yanayin halittarmu datasu akwai banbance-banbance. Amma badan hakaba saika rantse cikin tsatsonsu tafito.
    Taji nasihar meerah sosai, wannan yasakata maida hankali akan abinda yakaita, dukda haka tayi k'awa maisuna *Arena* itama baturiyace 'Yar asalin k'asar, amma tanada yanayin sanyi kamar Na Aysha, tasu tazo d'aya kam da Aysha sosai, kuma itace ke k'ok'arin k'ara fahimtar da Aysha abinda bata saniba, kasancewar har yanzu tanada sauran rashin gane turancin.

____________________________
    Gwaggo bintu tuni tahad'a inata inata tacane Lagos, tatafine akan zata zauna da aunty zuwairah saboda cikin datake dashi, sudai su aunty Mamie sunyi matuk'ar mamaki, danba yau Anty zuwairah tafara cikiba, kuma wani baita6a zuwa ya zauna mataba sai awanan Karon, alhalin wannanma itace haihuwa ta hud'u dazatayi.
         Tunda gwaggo bintu tasauka gidan Anty zuwairah bataga wata fiskar rahamaba agareta, babu wata tarbar mutunci data samu, ballatana kallon arzik'i.
    d'akin masu aikin gidan aka kaita.
   Aikam bak'in ciki tamkar yakarta🤣.

______________________________
    Tunda baffa sukadawo daga Jigawa yakasa sukuni, duk-yar zama wani kala dashi, har yanzu yana k'aunar fad'ima, Dan itace first love nasa, auren had'i akamasa da hajia babba, amma fad'ima za6inshice, akanta yafarason wata 'ya mace aduniya, shiyyasa yakan jita daban acikin mata, tundaga randa yafara ganin Aysha tatuno masa da Fad'imarsa, saboda wata muguwar kama dayaga yarinyar nayi da ita, baikawo komai aransaba alokacin, amma tabbas tundaga lokacin yaji yana begen son ganin fad'ima, saidai basan ina zai dosaba wajen sansanin indama take, gashi iyayenta duksun rasu tuni.
   Yaduk'ufa da addu'a tun'a lokacin, saigashi ALLAH ya kar6a masa, harda albishir mafisaka farinciki, shine fad'ima batada auren kowa akanta yanzu, harma ta kammala ida, Abu mafi damunsa kuma, halin ko'in kula da fad'ima tanuna akanshi dasuka had'u a Jigawa, 'ya'yansa kawai tasakarma fuska, saikuma matarsa bilkisu dataita tanbayar labarinta, amma shi yitayi kamarma bata sanshiba, yacije le6ensa tareda juya kwanciyarsa, gaba d'aya yarasa walwalarsa.
     Umme amarya dake gefensa kwance duktana lura dashi, kasa hak'uri tayi, tace, "waini alhaji lfy kuwa?".
      Murmushin k'arfin hali kawai yasakar mata, muryarsa a sanyaye yace, ''babu komai Saudah, kawai kainane yake ciwo".
    Ayya todakasha magani.
   A'a barshi kawai, kedai yi barcinki, kinga gobe idan ALLAH yakaimu kinada aiki.
     Shiru tamasa, kasancewarta mace mai halin ko inkula akan abinda bai shafetaba, amma amatsayinta Na lauya ta tabbatar yanada damuwa, bayason fad'a matane kawai. To itama batadamu dasonjiba. Kowa yaji da matsalarsa kawai.
       Shikam yak'i sanarmatane saboda gudun rigima, yatabbata kaf matan NASA Bilkeesu Ce kawai zai Tara da zancen azauna lfya, danhaka zaiyi hak'uri har ranar aikinta tazo, Dan gobema hajia babba Ce dashi.

Anty Mamie kam tun randa sukadawo daga Jigawa su Tasleem sukabata labarin komai, kuma mahaifiyartama tasanar da ita komai awaya, tayi farinciki matuk'a, kuma tana addu'ar ALLAH ya tabbatar baffah yace zai dawo da Yaya Fad'ima gidansa, zatafi kowa farinciki, dantana k'aunar matar, bata ta6a mata kallon kishiyaba saidai 'Yar uwarta. Tayi gum dabakintane Dan taga iya gudun ruwan baffan, tafiso yafad'a mata da kansa kamar yanda inna tace taja bakinta ta tsuke............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now