22

3.5K 311 3
                                    

2⃣2⃣

            Nikam momy miyasa zaki turomin matarnan?, nifa bancemiki ina buk'atar 'yan aikiba, nawa sun isheni.
           to naji, amma kimin alfarmar barinta tazauna anan zuwa wani d'an lokaci, nima bacanayi tazauna ananba aii.
    Shikenan momy, ammafa wlhy aikin zanke sata, danbazata zauna min saidai taci ta kwantaba.
    Bakida matsalar wanan, kisakata komiyema, itama aii 'Yar aikince, shikuma d'an aiki babu wani banbanci tsakanin babba da k'arami, duk'a mizani d'aya suke.
       To waini momy miyasama kikace tabar nan Abuja?.
    Wannan sirrinane kam zuwairah.
     Hummm momy kenan, kekomai da anta6aki saikice sirrinkine, ninarasa wanne sirrine haka?. Ina khaleel? Koyabar k'asar?.
      Yana nan, bakwa wayane?.
   Gaskiya kwana biyu bamu gaisaba, kinsandai halinsa da shegen shariyar tsiya, saidai kai kagaji kakirashi, amma hakanan dai bazaka ta6a ganin kiransaba.
          Saikuta hak'uri dashi, idan yay aure k'ila matar ta canjashi, sai anjima, agaida yaran. Yauwa kayan dakika turo hajia maryama tad'auki Na 2million's, sai hajia Fanta ma tad'auki Na 1.5million.
     OK momy, Dan ALLAH kimatsa musu wannan karon suhad'amin kud'ina dawuri, Dan dadyn Najwa yace, "nanda sati biyu zaije Germany, inaso nabashi yamin Oder d'in wasu kaya.
    To babu damuwa, kikira Khursum kuyi maganafa.
    Zankirata momy, agaidamin 2wins da mufeeda, shima khaleel ace ina fushi wlhy.
     Dariya momy tayi ta yanke wayar tana fad'in dukzan fad'a to.

Ajiye wayar babu dad'ewa ya khaleel yashigo falon da sallama, sanye yake da wando ja iya guywa, sai bak'ar riga mai gajeren hannu, hannunsa d'aukeda system da wayoyinsa.
      Harya zauna momy nabinsa da kallo, yace, " wash ALLAH nagaji momy".
       Baki momy tata6e, Ibraheem ainazata kamanta danima agidan?.
    😳ido yazaro waje, momy mantawafa?, ni khaleelu jikan Rufa'ee da Mujeetafa, na Isa manta uwata duniyata.
      Yay maganar yana tasowa daga inda yake, yadawo kusada momy yazauna.
     A shagwa6e yakamo hannunta tareda kwantar da Kansa saman kafad'arta, haba momy dabakinki kike fad'ar Na manta dake?, to ashema Ibraheem zai manta da kansa kawai sanyin idaniyata?.
     Da irin wad'annan kalaman yakan tausasa zafin momy aduk lokacin datau hayak'i akansa, tuni kuwa yayi tasirin sanyaya zucyarta, cikin mirmushi takai hannu tashafa fuskarsa.
    To yarona kaid'inne wani lokacin saina rasa kanka, dama nasan wasu abubuwan bayinkanka baneba, anjuyarmin dakaine kawai.
      Murmushi ya khaleel yayi kawai, yasan momy bazata ta6a canjawaba kam, yad'ago hannunta nadama dake rik'e a hannunsa Wanda yasha Jan lalle da manyan zobuna Na zeenari har uku ya sumbata, cikin shagwa6a yace, "karki damu my first love d'ina, bazasu ta6a rabani dakeba, Dan kekad'aice mai Ibraheem khaleel duk duniya, ko baffah saidai yabiyo sahu.😅
      Bak'aramin farinciki kalam d'an NATA suka sakataba, Dan haka tace, " ALLAH yamaka albarka Ibraheem, kai d'ane ain alfaharin kowacce uwa, ALLAH yacigaba da tsareminkai kaji.
     Amin mamyna.
Yanzudai yunwa nakeji, mizaki bani naci?.
            Mikakeson ci to?.
       Komike akwai zanci momy, sonake nad'anyi wani aiki.
        OK tom bara Nagano mike a kichin d'in?.
   To momyna, amma naji shiru, inasu Mufeeda?.
        Mufeeda taje Raka k'awarta biki tunda yamma, basu dawoba.
     'Yan biyu kuma sunje wajen baffanku kar6o kud'i, sunason zuwa shopping gobe.
               Kai momy! Kai momy! ALLAH yarannan basajin magana, yanzu bana hanasu fitar dareba kota yamma gefin magriba?, amma harkika bar mufeedah zuwa biki?.
      To kayi hak'uri, wlhy magiya taita yimin harda kukanta, wai k'awarsuce, bara nazo nakirata tadawo gida.
    Baice komaiba yajingina da kujerar yana k'aramin tsaki.
    Su hasnah suka shigo da murnar samo abinda sukaje nema, amma ganin ya khaleel sai kowacce ta kama kanta, suka aro nitsuwa suka yafama kansu. Ya khaleel barka da dare.
    Idonsa yabud'e akansu, ya amsa  babu yabo babu fallasa. Ganin fuskarsa da d'an sauk'in d'aurewa suka zauna a falon, amma kowacce a d'arare. Yana kula dasu amma yashare.
   Saima yad'auki wayarsa yahau kiran mufeeda.
      Harta tsinke bata d'aukaba, saida yay kira Na uku sannan ta d'auka gabda zata tsinke.
        Wlhy nabaki nanda 15minutes, inhar baki bayyana agidaba sainaci ubanki adarenan, danhar wajen iskancin naku zanzo Na 6a66allaki 'Yar iska kawai.
      Abinda yafad'a kenan ya yanke wayar.
     
gaba d'aya Mufeeda takid'ime, fad'itake nashiga uku ya khaleel yana gida, cikin hanzari take had'a inata-inata.
   K'awayenta suka shiga tambayar lfy kuwa mufeey?..
     Kai kubarni tafiya zanyi wlhy, ya khaleel yana gida shine yakirani yanzu, dayawansu sunsan khaleel d'in, harma damasu dakon soyayyarsa acikinsu.
   Harbakin mota sukamata rakiya, dama birthday d'in wani boyfriend nata sukazo, babu wani biki...........
 

Anty Mamie zaune gefen baffah tana had'a masa dinner cikin nutsuwarta.
   Tagama tahad'a komai agabansa tareda fad'in bismillah.
     Murmushi yamata, cikin tsokana yace, "saidai kibani abaki".
       'Yar dariya tayi, lallai baffansu, yakamatafa kasan ka girma, ga 'ya'ya ga jikoki, ko Najwa d'in Zuwairah aka aurar yanzu zama zatayifa.
    girarsa yad'age yana fad'in ummyim shikenan kuma Dan inada jika data kusa isa aure bazanyi soyayyaba?.
     Kanta ta girgiza masa tana murmushi, tace, " wane mutum, ai soyayya bata cancanci kasuwa daga gwarzo irin Abdallah naba.
       Wata dariyar jin dad'i yayi, yagyara zama yafara cin abincinsa, sunayi suna hira har ya gangaro inda yakeson zuwa.
    Yauwa nikam Bilkeesu su maleeka sun fad'a miki munhad'u da fad'ima a Jigawa?.
    Kanta ta girgiza alamar a'a, tad'ora dafad'in kasan basusan wacece itaba shiyyasa bazasu kawo komai.
      ALLAH Sarki Yaya fad'ima baiwar ALLAH, yanzu kotana inane da aure? Wlhy ina k'aunar baiwar ALLAHrnan baffansu.
    Murmushi yayi, yad'auki ruwa yasha sannan yagoge bakinsa da tissue, idonsa akan aunty Mamie yace, "ai yanzu batada aure, mijinta yarasu wata biyar kenan, harma tagama iddah.
           Wani zumud'in farinciki Anty Mamie tayi, cikin matuk'ar murnarta tace, " wayyo baffansu dama kadawo da ita d'akinta, wlhy danayi farinciki.
     Shiru yayi yatsuramata idanu, yarasa Bilkeesu wace irin macece mai dattako da hangen nesa, (baya raba d'ayan biyu tasan sirrinsa) shine tabiyo masa ta wannan hanyar danta k'arfafashi, ( haka take, inhar talura da yadamu da Abu tokobai fad'a mataba zataita karantarshi harta fahimta, koda abinnan baimata dad'iba to insha ALLAH zatayishi danta faranta masa rai.
   Rungumota yayi jikinsa yana fad'in Bilkeesu ALLAH yayi miki albarka, ketadabance acikin mata, amma kina ganin dawo da fad'ima gidanan bazai zama matsalaba?, kuma itama sainaga kamar bazata amincebafa? Dan wlhy ajigawa yitai tamkar bata sanniba.
            Karka damu muyita addu'a insha ALLAH babu abinda zai faru sai alkairi, batun Yaya fad'ima kuma kabari zanje gareta dakaina, tunda kace zata aurar da yariya ko?.
   Kansa ya d'aga mata.
    Tace, "amma kasanarma Ammah?.
     A'a dama kunakeji, amma nasan Ammah zatayi farinciki, dan tanason fad'ima.
    Hakane, ALLAH yashige mana gaba.
   Daga nan suka cigaba da tattaunawa, ak'asan ran baffah kam yana tunanin yanda zai tunkari sauran matan nasa, dukda yana ganin Na Umme Amarya mai sauk'ine, hajia babba Ce matsalar, tunda dama bason Fad'ima takeba, harta bar gidan basu ta6a zama lfy ba, kasancewar fad'ima Nada zafi, bata d'aukar raini gakowa.

Yanacin abinci tashigo, sai la6e-la6e takeyi, momy ce tace, " waike Mufeeda la6e-la6en mikikema mutanene?.
    Da baki tama momy nuni da ya khaleel.
   Momy tamaida kallonta ga ya khaleel daketa cin abincinsa hankali kwance, duk kuma abinda ke faruwa yana kallonsu ta gefen ido, amma yayi kamar baisan abinda akeyiba.
      Ibraheem!.
Momy tafad'a tana ta6ashi a kafad'a.
    d'agowa yayi yace, ''na'am momy".
       Kayi hak'uri.
Momy hak'urinmi? Mikikamin?.
      Baniba mufeedah.
       Maida kansa yayi yacigaba dacin abincinsa, momy bar 'Yar iskarcan, tacemiki biki taje, amma k'arya takeyi.
     Inataje to?.
Tafad'amiki da bakinta.

Momy tamaida kallonta ga mufeeda, inakikaje? bacakikaimin ana kamun seematu ba yau?.
       Shiru mufeedah tayi tana tura baki gaba.
      Ya khaleel yadaka mata tsawa, Dan ubanki badake ake maganaba?.
     Zabura tayi gefe, cikin rawar baki race, momy wlhy fa....um....um.
    Um...um...mi? Mufeeda wai mikikeson maida kankine? Nifa wlhy halayenki sunfara bani tsoro, lfy lau narabu da zuwairah da Shukrah, ammake naga baki biyo hanyar hakanba, to wlhy bazan d'aukaba, babanku zanma magana yahad'a aurenki danasu Sultan wlhy, bazan iyaba, banyi iskanciba, bazan haifi 'Yar iskaba.

(Nace, hummm momy kenan, kin salwantar da 'ya'yan mutane, amma kike tunanin naki zasu sami tsaro, a'a momy, ba'a shuka shinkafa agirbi alkama.🤣🤣).

        Ya khaleel daya gama cin abinci yature gefe, k'afafunsa yakwashe yamaida saman table d'in bayan Hasnah takwashe kwanikan. Yace, ''momy harda laifinki, yarannan babu maifad'a musu basuyi daidaiba agidannan saidai Idan inanan, yanzu ace kamarsu Sultan bazasuga yaranana Na Abu mara k'yauba su tsawata musu? haba momy mana, to wlhy yanzu wani abokinane Hasheem yake sanar dani yaganta a wani Hotel suna rawa suda samari, wai na birthday d'in boyfriend nasu.
     Amma dayake ita batada mutunci saitace dake biki suka tafi, ALLAH yau saina kusa 6allaki agidanan mara hankali kawai, saboda kingama degree kinfara aiki shine kanji ke hayak'in iskanci ko? To zan sauke mikishi yanzunnan yay maganar yana mik'ewa kanta
              Kafin tayi yunk'urin guduwa kam ya cafkota, damaruka yafara mata, tad'an daku kam tasamu tagudu d'aki, momy batace komaiba, Dan itakam gwara yayma mufeedan haka kartaje takwaso mata abin kunya, kishiyoyi susami abin yimata gori agida, wannan yasa ta kauda kanta bata hana ya khaleel dukan mufeedar ba..........🖊

Bara mulek'a mutanen UK su Aysha sholy🤪

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now