13

4.1K 316 0
                                    

1⃣3⃣

   Ransa duk a6ace yake, yarasa miyasa momynsa ke irin wannan halin? gashinan tazama malamar yaranta, sukad'aine baud'ad'd'u agidan, tsomwwww yakuma jan tsaki yana cije le6ensa nak'asa.
    Wlhy dayasan abinda zai tarar kenan, dabazai shigo gidannanba, dama aikine Nanne yatsayar dashi a k'asar, ganin yanada d'an time shine yazauna agidan, Dan rabonsa da gidan tun rasuwar k'aninsa Rufa'ee, yadafe kansa danjin yana sara masa, shi mutumne mai matuk'ar zuciya, Abu kad'an yake hassalashi yayi sama.
    Kwanciyarsa yayi bisa doguwar kujerar falon nasu, sudai k'annen nasa duksuna zaune suna kallonsa cikeda tausayi, babu Wanda yace masa k'ala.
    Saida yakwantane cikin k'arfin hali Mujahedeen yace, "ya khaleel daka koma d'aki aii.
    d'ago manyan idanunsa dasukai jajur yayi yana kallon mujahedeen d'in, yasakar masa guntun murmushin 6acinrai kawai, saikuma yalumshe idanunsa yagyara kwanciya.
       Zunnurain yace ya khaleel please mana.
     Mik'ewa yayi dak'yar, yace, " is OK, kowa yaje yayi kwanciyarsa, nima bara nawatsa ruwa.
    Kawuna suka d'aga MASA kamar k'adan garu.
    Saida yaga kowa yashige d'akinsa sannan shima yashiga.

        Arud'e aunty tak'araso falon 'yan samarin, babu kowa aciki, saidai ko'ina yayi need, dukdama ba akai gayin sharar safeba, k'ofar d'akin ya khaleel tak'arasa tayi Knocking.
    Fitowarsa kenan daga wanka, wajen k'ofar ya matso yana tsane ruwan jikinsa da k'aramin tawul, yace, ''wanene?".
       Aunty Mamie taisaurin cewa nice babana bud'e.
    Cikin hanzari yaja jallabiya blue mai gajeren hannu yasaka, aladabce yabud'e k'ofar yafito, a falo ya hangota, k'arasowa falon yayi har k'asa yadurk'usa ya gaisheta (harga ALLAH yana matuk'ar ganin kimarta, idan yana tareda ita yakanji wani iri saboda kwarjinin datake masa, shima baisan miyasa hakanba, kodan tana nuna kulawarta agareshi? oho. gashi ance nononta yasha yana k'arami).
    Aunty ta amsa kamar yanda tasaba, cikin kulawa tace babana miya sameka? Tasleem tacemin kaji ciwo ahannu, ina wankane lokacin.
    Murmuahi ya khaleel yayi danganin yanda aunty Mamie tarud'e, ko Momy batayi irin rikicewar nanba, ya yarda da aunty Mamie, danhaka yakan iya fad'a mata sirrin aikinsa kai tsaye ya 6oyema Momy, haka kawai yakejinta daban da kowa agidan, (dukda Momy tana cusa musu k'iyayyar aunty fiye data kowa agidan kuwa)....
      Aunty ta katse masa tunani dafad'in yadai babana?.
    Ajiyar zuciya yasauke, aladabce yace karki damu aunty, dama bawani Abu baneba yankane kuma nasamu dukkan kulawa.
      Arazane aunty tace babana yankafa? garin Yaya haka tafaru dakai? Kai nidai wannan aiki naku nabani tsoro wlhy, haka kawai naji gabana nata fad'uwa tun jiya Ashe Kaine......
     Shine me uwar tsurku, wlhy Bilkeesu kifita sabgata banason shishshigin dakikemin akan Ibraheem!, tundani banta6a damuwa dashiga sabgar 'ya'yankiba.
   Kaikuma sakarai kazauna kana kwance mata yanda akayine? Wlhy Ibraheem kazama sallamammedai, kaico da wannan zuciyar taka, gakadai kamar jarumi awaje, amma shiryayyen sakarai akayi, koda yake ba laifinka baneba, anrigaya an rubuce sunanka a allon bak'in k'arfene, kai nidai ALLAH ya tsinema malamin dayaymiki wannan aikin Bilkeesu akan Ibraheem.
      Khaleel yakatse Momy cikin 6acin rai, haba Momy Dan ALLAH, wai wane maganganu kikeyi hakane?, haba Momy, nibansan mi aunty Mamie takemiki acikin gidannanba kike k'inta haka, tanada kirki wlhy m.......
    Dakk'uwa Momy tamasa, cikin masifa tace, "kaida kirkin nata kunci uwarku, wlhy idan Baka rufemin bakiba anan sainaci Ubanka sallamamme kawai.
     Shiru khaleel yayi, amma ransa yakai k'ololuwar 6aci, shiyyasa kokad'an bayason zaman gidannan, idan yabar k'asar ko kewar gidan bayayi.
     Can ya tsinkayo muryar Momy tana cigaba dacima aunty mutunci, wadda tuni tabata hak'uri tafice daga 6angaren, idan dasabo tasaba aii, tun suna zamanin k'uruciya ake Abu d'aya, tarasa wane irin kishi mai zafi hajia babba keyi da'ita? Amma bata nuna kishinnan mai zafi akan hajia saudah, (amma itada hajia Fad'ima sunsha wahalarta tun abaya, saida tayi k'ula-k'ullar datayi Alhaji Abdallah yasaki hajia Fad'ima, mace mai kirki dasanin yakamata).

Tofa masu karatu, wacce hajia Fad'ima??, itama matar Alhaji Abdallah ce kenan? Kamar yanda aunty Mamie tafad'a.
   Toko tana ina yanzun🤔🤕 ?.
    Bara mucigaba dabin labari dai😢.

Ganin Ammah afalon yasa aunty k'ara gyara nutsuwarta, Dan kokad'an batason surukar tasu tasan abinda yafaru, barema har zancen yakai kunnen mijinsu.
    Rissinawa tayi tagaida Ammah, cikin fara'a Ammah ta amsa mata, tana k'aunar Bilkeesu saboda k'yawawan halayenta.
    Aunty tace masu Amal kutashi muje kichin kuhad'a abincin yayyenku, yau har 11 ba'a karyaba. To suka fad'a suna mik'ewa.
       Suna shiga kichin d'in saiga Momy tafito daga 6angarensu khaleel tana hura hanci, saud'aya ta kalli Ammah tace barka da gida Ammah, tayi shigewarta 6angarenta.
     Kwafa Ammah tayi tana fad'in lalatacciya kawai, saiyanzu kika ganni? d'azun bakina ganinaba amma kika wuce mai bak'in halin tsiya, ai wannan yaron bai dace damacen farkoba alkur'an, ALLAH dai wadaran zuri'ar jummai, ya halinki ya halin uwarki dukda tana k'anwata kuwa.
    Haka taita mita da zagin Momy, hardasu gori kuwa, dama anfad'ama ammah masifane.

Duk abinda yafaru tsakanin momy da aunty Mamie da ya khaleel su musleem najin komai, suna zaune jigum-jugum, abin nadamunsu, suna d'agama Momy k'afane kawai saboda tana matar mahaifinsu, kuma tanacin darajar ya khaleel, akullum kuma aunty Na nuna musu kadasu sake Susaka Baki akan abinda ke faruwa tsakaninta da Momy, babu ruwansu, mahaifiya Momy take agurinsu, inhar suna d'aga mata murya, to itama data haifesu zasu iya yimata fiye dahaka, wad'annan abubuwan ke taka rawar gani wajen sakasu kauda kai akan lamarin gidan gaba d'aya, amma abubuwan naci musu zuciya ainun.
     Musanman ma ya mujahedeen da aunty Amatullah dasuka kasance masu zuciyar tsiya kamar ya khaleel.

Shikam khaleel yanacan cikin 6acin ran da Momy tabarsa, sai tsaki yakeyi yana shafa mai, ALLAH da Momy ba mahaifiyarsa baceba datuni yagyarata agidannan, kwata-kwata bayason halayenta, duk gidan tafi kowa fitina, wani lokacin jiyake inama ba'itace ta haifeshiba (idan yay irin tunanin yakanyi saurin yin istigifari, daneman tsari daga sharrin shaid'an maisaka waswasi a zukatan bayin ALLAH).
   Amma gaskiya halayen Momy basa birgesa itada 'yan uwansa, ahaka yagama shirinsa yahaye gado danyad'an huta, babu dad'ewa barci yay awon gaba dashi, dama yagaji over.

    

Yau har 11 babu Wanda yafito breakfast, su Aysha sun kammala komai tuni, sungyara ko ina yad'auki k'amshi.
      Suna d'aki itada Bishirah, Aysha nagyara kayanta, itakuma Bishirah Na tsifar kanta. cikin sauke ajiyar zuciya Aysha tace kai bishirah wlhy nikam  d'azun ya khaleel yabani tsoro, saidai kuma abinda yabani mamaki dukda dukan Hasnah dayayi babu Wanda yace masa baiyi dai-daiba, garama hajia babba naga kamar taji haushinsa. Komiyasa?.
         Saboda batason gaskiyane kawai Aysha.
   Haka yake jibgarsu idan suna kai hak'urinsa mak'ura, shiyyasa idan yana gidan duk wani iskancinsu basayinsa, itama natabbata batayi tunanin zaidawo gidanba yanzun. dabazama tafara aikata abinda tayiba.
      Bak'aramar firgita Aysha tayiba, har taune le6enta takeyi wajen fad'in kina nufin zai iya hukunta kowa akan lamarin cikin  gidannan?.
      Bishirah tagyad'a kai alamar tabbatarwa.
       Shiru Aysha tayi, jikinta duk yayi sanyi, harga ALLAH tana tsoron masifaffen mutum, ballatana wannan murd'ed'en k'aton mutumin, gashi dogo masha ALLAH......
     Bishirah tace, "yadai Aysha?".
      K'utt Aysha tahad'iye yawu sannan tace babu komai, amma wlhy har gidan yama fita raina nikam.
    Maganar Aysha taba bishirah dariya, kinga karki damu kanki, indai ya Khaleel nema zai iya barin k'asar gobe idan ALLAH yakaimu, tunda kika gansa yanzuma wani aikinne yazaunardashi. Itama Hasnahr ita tajama kanta dukan, dukda nasan batayi zaton ganinsa yanzuba...........
        Shiru kawai Aysha tayi, amma harga ALLAH atsorace take, jitayima gara tabar k'asar kamar yandasu hajia babba sukace, amma tana fargaba wlhy, gashi ance k'asashen waje turanci akeyi, itakuma bata iyaba sosai, anya karatun nata zaiyi tasiri? dukda kwad'ayinsa datakeyi, gashima har yanzu zuciyarta bata amince dawai karatun za'a turataba, dukda basu 6oye mataba sunce harda hidimar wasu zataje a can.
    Bakomai tadogara ga ALLAH, shizai tsareta akowanne yanayi.
        Damuwarta d'ayace su mamanta, tanason ganinsu kafin tawuce, shiyyasa tadage da sallar dare akan ALLAH yad'orata akansu hajia babba subarta taje tama iyayenta bankwana, kodan tasamo albarkacinsu........🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now