90

4K 235 14
                                    

90

Kwana biyu kenan da dawowar khaleel Nigeria, har yanzu kuma fushi yakeyi da Aysha, zaidai shigo yad'auki junior yafita, Ammah ma baya kulata, yana dai gaisheta amma babu hira.

      Yau takasance monday, dawuri khaleel yay shirin office, ko cikin gida bai shigaba yafice da hanzari.
   Adams yabud'e masa mota yashiga, bayan sunyi salute nashi.
    Tafiyar mintuna k'alilance takaisu.
 
      Zamansa babu dad'ewa a office saiga kira yashigo wayarsa, dubawa yayi kasancewar wayar office ce, ganin ogansa yasakashi d'agawa da hanzari.
   Cikin girmamawa ya gaidashi.
    Saikuma naji yana fad'in "OK sir, ganinan zuwa to".
    Yana Yanke wayar yamik'e yad'auki wasu takardu yafice.
     Saida yayi knocking aka bashi izinin shiga sannan yatura k'ofar yashiga, ya k'ame tareda salute na ogansa.
    Fuskar Oga d'aukeda murmushi yanuna masa wajen zama bayan yamaida masa murtanin salute d'in.
 
     " J! Ya iyali?, da abokina Abdallah?".
    Murmushi ya khaleel yayi, yace, "yana nan lfy sir".
        " to ALLAH ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa yafika jarumta da kwazo".
         Murmushi sosai khaleel yakumayi, Wanda har hakwaransa suka bayyana, yanason ayaba masa d'an Abdallansa😃👍🏻.
      Yace, "to ALLAH ya amince sir".
    Oga yay 'Yar dariya, tareda mik'ama khaleel wata Leda mai azabar k'yau.
    "Ga wannan j!, gobe idan ALLAH ya kaimu su zaka saka, kuma kaida madam zakazo".
      Cikeda mamaki khaleel yakar6i ledan, yad'an lek'a cikinta sannan yakalli ogan nasa.
    " sir! wani abune za'ayi?".
        "A'a, kaidai kasaka kawai, kuma sai around 11 za'azo a d'aukeku insha ALLAH".
      
kasa cewa komai khaleel yayi, sai jinjina kai yake tamkar k'adan gare.
       Oga yayi murmushi, tareda basar da zancen yace, " so ina takardun danace kazo dasu?".
     Mik'a masa khaleel yayi.
    Oga yakar6a yad'an dudduba, sannan yad'ago yakalli khaleel d'in, " ehm j akwai wani aiki daya taso mana again, so zamuyi meeting akan batun next week insha ALLAH, kuma aikin gaskiya dolene kaine keda zarrar yinsa, Dan wad'anda za'a kamad'in saida irinku awajen, amma gawad'annan kaduba wani 6angarene nabayanan, zan turo maka sauran ta network".
     "OK sir!".
" zaka iya tafiya abinka".
     Mik'ewa yayi tareda k'amewa dayin salute na ogan, sannan yafice.

     **********

Tunda yadawo office yaketa juya maganar ogan nasu, baidai bud'e kayanba, yamaida hankalinsa akan binciken bayanan da oga yabashi akan aikin kuma dayake tunkarosu.
     Yaja tsawon lokaci a binciken yaji alamar shigiwar massage a wayarsa.
   Kamar bazai dubaba dai yad'auka.
     Number Aysha yagani, yasaki guntun murmushi sannan yabud'e sak'on.

_"Amincin ALLAH ya tabbata agareka yakai sanadin farincikina, inafatan kana cikin kwanciyar hankali da walwala ahalin yanzu?, Alkairin ALLAH yacigaba da yalwatuwa aduniyarka, ALLAH yatsareminkai daga idon mata🤕, masu k'arema mazan mutane kallo😏."_
      _"junior yace dadynsa yakasance cikin kwazon aiki da farinciki, gefe kuma yaringa tuna mamansa, yamata uzuri, adaina fushi da ita, ba laifinta bane, itama tana kewar bakandamiyar rayuwarta Abban junior💋."_

Baisan sanda wani murmushi ya su6uce masaba, yakuma maimaita sak'on sannan ya tuntsure da dariya, kai yarinyarnan sai'a barta, 'yar k'arama da ita ta'iya kishi.
   Cikin lumshe idanu ya sumbaci massage d'in, shikansa fushin dayakeyi dauriya kawai yakeyi, amma yana kewarta, yanaso kod'an kissing d'inta yayai, amma  Ammah takafa tatsare.
      Bud'e idanunsa yayi, sannan yay dealing d'in number d'inta, harta katse bata d'agaba, kasa hak'uri yayi yakuma kira, bugu biyu kuwa tad'aga.

    Murya can k'asan mak'oshi tace,
      "Hii my lollipop".
Lumshe idanun yakumayi, da k'yar ya iya furta " A'eesha kin rainani ko? kimin laifi amma kimaidashi wasa?".
         _"Ooo! my god, ni na'isa wasa da jarumi mai zarrah irin j!, karfa ka manta j! Ne, kuma j!! Bayason raini, amin afuwa, komai akaga nayi, akan kuskurene, amma bazan sakeba, junior nataya Amminsa bada hak'uri, kagama kuka yake shirinyi, harya fara ta6e baki"._
     "Kai haba dai?".
  " ALLAH kuwa". "tayi maganar tana kara wayar kusada Junior".
    Aikam tamkar jira yake yafashe da kuka😂

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now